Shafi na talatin da bakwai............Bayan shigewar Qaseem da Bily babu daɗewa Mummy na zaune tana saƙawa da kwancewa ta yanda zasu ɓulloma zaman Shahudah da Jawaad kira ya shigowa wayarta.
Ɗauka tayi babu ɓata lokaci, dan kuwa kirane mai matuƙar muhimmanci.
Sama-sama sukai gaisuwa mai kiran ta fara zayyane mata abinda ya faru a family house ɗin su Jay a yau, wato dai walimar cin abincin da aka shirya masa mai taken yaɗa manufar tallar matan aure.
Ran Mummy ya ɓaci ƙololuwa, dan a ganinta wannan tsagwaron munafurci ne kawai ƴan uwan nata suka shirya, taya zasu nema aikata haka?, bayan sunsan akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin Shahudah da Jawaad ɗin, saɓanine kawai da sharrin shaiɗan ya gitta har wancan matsalar ta faru, maimakon su nema hanyar da za'a sulhunta shine zasu haɗa wannan annamimancin? To lallai lokaci yayi da za'ai uwar watsi kuwa ashe, yanzu ace har mahaifiyarsu ta gaza kiranta ta sanar mata balle ƴan uwanta su Uncle Uwaisu, dan bata saka Maimuna ƙanwarta a wannan sabgar, tunda tuni ta nuna musu bata tare dasu ita dama.
A wannan dare gaba ɗaya barci gagarar idanun Mummy yayi, gashi Dad baya gari, tayi kiran wayarsa yafi sau goma taƙi shiga, ta kuma kira Mama Atika ba'a ɗaukaba, ta kira Shahudah shima bai shigaba.
Gaba ɗaya sai kanta ya ƙara ɗaukar zafi, sai sauke ajiyar zuciya takeyi a jere a jere.Gari na wayewa duk da uban barcin dake cin idanunta haka tai shiri tunda farar safiya ta fice a gidan, ko jiran driver bata tsaya yiba, dan aganinta kafin yazo an gama ɓata mata lokacinta.
Tun shigowarta falon mama Atika dake zaune tana lazimi ke kallonta, Mummy sai sake cika take tana batsewa, ganinfa mahaifiyartasu ba ida addu'ar nan tata zataiba ya sata faɗin, “Wai nikam mama wannan addu'ar bata ƙarewa ne?, nifa a ƙage nazo”.
Mama Atika batace mata komaiba, hakama bata tsaya da addu'arta ba sai da takai aya, ta shafa tana faɗin, “Ke dai Wlhy Ai'sha sam baki da ɗabi'ar ƙwarai, ba ƙaramin lalacewa rayuwarki taiba a garincan na marasa sallah, mike faruwa na ganki da wannan uwar safiyar?”.
Cikin sake ɓata fuska Mummy tace, “Ba dole ake ganina da farar safiya ba, yanzu mama dan ALLAH munafurcin da ake shirin ƙullawa ya ƙyautu kenan a gidannan?, kowa yasan alaƙar dake tsakanin Shahudah da yaron nan na wajen Abdul-aziz, amma shine za'a shirya wani annamimanci ta bayan fage ba tare da nasaniba ma........”
Saurin katseta mama Atika tai da faɗin, “Ke da ALLAH rufama mutane baki, waye zai sake haɗa sabgarsa da wannan shashashar ƴar taku mai kama da wadda aka yaye jiya, idan barci kike to kidawo hankalinki Ai'sha, badan wawiyar yarinyarnanba da yanzu mun gama mallakar fiyema da abinda muke buƙata, amma tazo ta ɓata mana komai saboda ita shashashar yarinyace taɓararriya, ki duba yanzu wulakancin data jawo mana ne ya saka dukkan manufofin mutan gidannan ya gama bayyana, yanzu kowama yima ƴarsa farautar yaron nan yake, dan dama can shakkatane ya sakasu haɗiye ƙwaɗayinsu a fili, dukda wasunsu na taƙamar komai yana hannunsu ne ai, maimakon kuma a shekaru huɗun nan ku nema hanyar gyara komai tunkan abunma yay nisa ta bashi haƙuri amma sai kuka ɗauketa kuka sake turawa cikin yahudawa, kekuma kika ɗauki fushi damu, yanzu har nai ciwona na gama a gidannan Ai'sha baki leƙoniba, saboda ke mai ƴa ko? To mune muka saketa? Kokuwa mune muka sakashi sakinta? Muda ta ɓatama komai mune ya dace muyi fushi ba keba? ai ko.......”
“Nidai mama naji, ya isa dan ALLAH, sai faɗa kike ko haɗiyar yawu baƙyayi, naji anyi kuskure, amma kuma ai bai ƙyautu a wancan karon kowa yaƙi fahimtar ƙaddarace sanadin komai ba, ALLAH ya rubuta cikinnan bazaizo duniyaba, daga baya kuma dai ai komai ya dawo ya daidaita, amma sai babu wanda ya kirani a cikinku, ta yaya bazan ɗauki fushiba to?”.
“Kedai kika sani, ai kuma fushin naki bai miki amfaniba, tunda gashi kin dawo da ƙafarki ko?, kuma a lokacin da kuka makara keda ƴar taki, dan kuwa a yanzu filin dagar ya zama na mafarauta da yawa”.
“Mama ki daina faɗin mun makara, babu wata makara tunda kowa yasan Jawaad nason Shahudah, kuna insha ALLAHU a cikin watannan zata dawo ƙasarnan”.
Baki mama Atika ta taɓe da yamusashshiyar fatarta ta tsufa, tace, “Kudai kuka jiyo, danni tawa tai ƙyau, dama kune masu amfana baniba, a shekaruna ni yanzu amfanin mi abinda akemawa ɗin zaimin?, komai da kukaga inayi danku nake yinsa”.
Shiru itadai Mummy tayi bata tankaba, tana nan zaune har su Uncle Uwaisu suka shigo gaishe da mama Atika, annanfa suma Mummy ta balbalesu da masifa, ta inda take shiga ba tanan take fitaba.
Wasa-wasa rigima ta kaure a tsakaninsu, dan kuwa yanzu suma ba ɗaga mata ƙafa zasuyiba duk da tana babbar yarsu a ɗakin, duk yanda mama Atika taso suyi shiru sunƙi, har sai da ta saka musu kuka sannan suka dawo hankalinsu sukai shiru.__________________________________
To nidai sam bansan bikin da akeba a gidan, naji dai Aunty Aamilah na magana akan Aunty Shahudah zata dawo, banji an faɗi rana ba, bakuma a faɗaminba, nima sai banbi takaiba, dan bakowace sabgar gidan nake shigaba musamman ma yanzu danasan ciwon kaina.
Tsawon kwanakin da suka biyo baya a satin ban sake jin komai na faɗuwar gaba ba, hakama wanda muka taro a ranar nan ban sake ganin koda ɗaya a cikinsuba.
Duk da abubuwa masu yawa game dashi sunƙi barin raina, duk kuma ƙoƙarin turesun da nakeyi hakan baisa na damu kaina da rashin ganin nasa ba, na cigaba da harkokin gabana har a yau da mukai safiyar fita aiki kasancewarta Monday tushen aiki.
Kamar kullum nayi tsaf dani, tamkar ka saceni ka gudu, musamman ma data kasance a yau sanye nake da baƙaƙen suit na mata wando da riga, na kawo farin baby hijjab na saka tamkar yanda na saba a kowace rana, kayan sun zaunamin sosai a jiki tamkar dan jikin aka haliccesu, na saka siririn farin eyeglasess ɗina sannan na fito ɗauke da takalmana a hannu.
Babu kowa a falon, na ajiye takalman na nufi kicin, kuku harya kammala haɗa mana breakfast ni da Yah Qaseem, tea na shiga haɗawa muna gaisawa dashi, ban fitaba na zauna a ɗaya daga kujerun huɗun dake a kicin din, tebir a tsakkiyarsu, ina fara shan shayin Yah Qaseem na shigowa shi da Salman.
Nayi mamakin ganin Yah Salman da wannan farar safiyar, shi da kullum sai anyi fama dashi ma yake tashi da safen yay shirin zuwa aiki, da yake a kamfanin Dad yake aikin sai yakai goma bai fitaba ma.
Hannu Yah Qaseem ya miƙomin alamar mu gaisa, amma sai na girgiza masa kai ina murmushi da faɗin, “Yaya ina kwana”.
Hararata yayi sannan ya zauna, Yah Salman da shima ke zama ya taɓe baki.
Shima gaishesa nayi ya amsa a ɗage kamar yanda ya saba.
Ban sake bi takansuba naci gaba da shan tea ɗina nidai, suma kowanne ƙoƙarin karyawan yakeyi.
Ban wani ci abincin kirkiba na tashi na koma falo na barsu a kicin ɗin, ina ɗaura takalmina sai ga Yah Qaseem ɗin ya fito yana faɗin, “Tashi muwuce mun makara”.
Miƙewa nayi muka fice.★★★★★
Yayin da muka isa office ina fitowa daga mota da shi na fara tozali.
Hakanne ya saka gabana faɗuwa, ganin bamu yake kalloba na ɗauke kaina daga garesa, sai ta gefen ido nake satar kallonsa, sanye yake da jeans ruwan toka da farar shirt mai gajeren hannu, idanunsa sakaye cikin glasess da yay masa matuƙar ƙyawu.
Dole inda suke tsaye shi da wani a jikin wata mota itace hanyar da zanbi ta kaini inda zanje, sai kawai na canja hanya saboda yanda nakejin gabana na cigaba da tsananta faɗuwa.
Nidai nasan ba tsoro bane ba, sai dai yanamin kwarjini da zan iya rantsewa wani ɗa namiji bai taɓamin irinsa ba, bansan miyasa hakanba? Bankuma san minene dalilin hakanba?.
Hanya na canja, sai dai inajin tamkar ana bina da kallo, juyowa nayi kaɗan dan inga ko zanga mai kallon nawa, sai dai banga kowaba.
Na cigaba da tafiya ina karanto addu'ar duk da tazomin kan harshe.
Ikon ALLAH tunda nayi nesa da wajen dana gansa sai na koma normal, harna ƙarasa wajen da nake ƙyautata zaton ganin Ummie.Ɓangaren Jawaad kam da a yau suka dawo aiki shi da tawagarsa, ya iske ayyuka da dama, musamman waɗanda suke da matuƙar haɗarin da ake buƙatar mutum mai ƙwazo da jajircewa irinsu, wasu ayyukan kuma an badasu ga wasu jami'an ne amma sunata musu tafiyar hawainiya basu ƙarasaba babuma wani bayani mai gamsarwa, hakan yasa yau aka miƙasu gaban su Jawaad ɗin.
Kansa yaɗauki zafi da ganin ayyukan dake jibge a gabansu, duk da kuwa a yanzu sun sake samo dabaru na musamman shida abokan aikinsa da suka samu zuwa wannan horo na musamman a ƙasar amuruka, ya kuma dawo ne da karsashin aikin canja wani abu a ƙasarsa dan bai isa canja komaiba shi yasan wannan, irinsu masu son jajircewa ƙalilanne, tayaya kuwa suka isa canja komai? Sai dai suyi nasu ƙoƙari su koma gefe, UBANGIJI shike da sauran hanyoyin maganin sauran tunkafin nasu, rahamarsace ta saka zukatansu suma jin son gyaran.
Baƙon da yayi wani abokinsa da sukai secondary tare lauya, yazone bincike akan wani case shine ya rakoshi suka tsaya a jikin motarsa suna magana.
Sarai Jawaad yaga lokacin da Qaseem da Bily suka fito a motar Qaseem ɗin, amma sai ya ɗauke kansa cikin basarwa, duk da a ƙasan zuciyarsa yana tunanin minene alaƙar Qaseem da wannan yarinyar? Saboda a koda yaushe yake ganinsu tare da juna.
Sai kuma akai rashin Sa'a shima abokin nasa idonsa suka hango su Bilkisun.
Yace, “Woow, Jay kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta mai tsada da daraja kuwa?”.
Jawaad da ras ya fahimci inda abokinsa ya dosa tsabar rainin wayo sai yay tamkar bai fahimtaba............✍🏻ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...