Shafi na talatin da biyu
..............Gidansu Amina yana maƙwaftaka da gidanne, dan duk anguwar kusan shine ginin talakawa, Amina ta taɓa sanarmin Babanta ne ya saidama Dad filinsa kafin ya rasu, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH karya bar wani ya amshe gidan dasu Amina suke ciki danya lura masu hannu da shuni duk sun saye gidajen talakawan wajen sunyi gine-gine saboda ƙyawun anguwar, shiko gidansune na gado bayason yaransa su rasa.
Wannan alƙawarine da dad ya riƙe ya saka gidansu Amina zama zakka a anguwar duk da kuwa ansha ƙulla musu dan a mallaki gidan hakan bata faruba.
Da Amina na fara tozali tana kwance a ƙofar ɗakinsu lulluɓe da bargo tana rawar sanyi, na ƙarasa gareta ina ambaton sunanta.
Dai-dai nan mamansu ta fito tana ɗangyasa ƙafarta dake mata ciwo, saurin dakatar dani tai a zafafe.
Na tsaya cak ina kallonta da mamaki, dan nasan matar tana sona sosai, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka koyamin dabarun rayuwa da mutane.
“Mi kikazo yi mana a gidan, ki fita dan ALLAH, bana buƙatar sake ganin fuskar kowa daga ahalinku, dan haka fita kona miki abinda baki taɓa tsammaniba....”
Kaina na duƙar ƙasa gabana na sake tsananta bugu, murya na rawa nace, “Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kimin uziri bansan komaiba dangane da abinda ke faruwa ba, babu kuma a wajen wanda zanji sai ku, nasan tunda naga fushi a fuskarki an miki ba dai-dai bane, dan ALLAH ki lamincemin mu raba wannan damuwar tare ko zanji sassauci a raina, da......”
Saurin dakatar dani tai da fadin, “Damuwarmu ai tafi ƙarfin mu kasaftata wani ya samu wani yanki a ciki, an rigada an cuta mana, saboda bamu da komai kuma an nuna mana fin ƙarfi, Bilkisu jin abinda ya faru bashi da amfani a gareki sam.....”
“Yana da amfani Mama, koba komai ƙila inada gudunmawar da zan iya badawa”.
“Baki da ita Bilkisu, dan haka fitar min daga gida”
Ko motsi kasawa nai, hawayen da nake riƙewa suka gangaro bisa kumatuna, juyawa nai a hankali zan fice muryar yayan Amina malamin islamiyyarmu na tsinkayo yana ma mamansu magana.
“Mama karki haka mu saurareta, dan muma munsan bata san komaiba tunda batanan, kuma koda tana nan bata da wani ƙarfin ikon sawa ko hanawa a gidan muma shaidane”.
Mama ta sauke numfashi da cewa, “Hakane, dawo Bilkisu”.
Da sassarfa na juyo garesu, na tako inda Amina take na durƙusa ina yaye bargon da take lulluɓe, ƙara ta ƙwalla, hakan ya sakani saurin ja baya a firgice.
Mama ta ƙaraso kusa damu tana mata magana, sai da ta sami nutsuwa ne maman ke cewa, “Kiyi haƙuri Bilkisu haka takeyi wanu lokacin, abu kaɗan ke sakata firgita yanzu”.
Sosai mamaki ya kamani, na kalli maman ina tambayar to minene sanadin hakan? Dan ni dai nasan Amina mace ce mai tarin nutsuwa a komanta.
Mama ta miƙomin kujera ƴar tsigunno, amsa nayi na zauna ina mai ƙarajin tausayin Amina.
Itama zama tayi daga ƙofar ɗakin, yayan Amina ma ya zauna daga ƙofar ɗakinsa.
Kallon mama nayi ina ƙara jeho mata tambayar abinda ke faruwa da Aminar.
Mama ta sauke numfashi mai ciwo tana share hawaye, tace, “Bilkisu fyaɗe akai mata a cikin gidanku, sai dai mun gaza tantance wanene yayi?, saboda abu suka bata tasha batare data saniba”.
Bansan sanda na koma ƙasa daɓas ba nai zaman ƴan bori, har taune harshena nake wajen faɗin, “Mama fyaɗe fa?”.
Kasa bani amsa tayi saboda kukan da takeyi, sai yayan Amina ne cikin takaici yace,
“Abinda ya faru kenan Bilkisu, munje mun faɗama Alhaji amma hajiya ta katsatstsare a kan sharri akaima ƴaƴanta, bayan kuma a idon mai gadi suka fiddo Amina cikin wani yanayi ita da Aamilah, munje mun ɗakko ƴan sanda shine suka basu kuɗi mukuma aka ƙaryatamu, wlhy badan mama ta hananiba da saina kaisu kotun musulinci, amma yanzu mubarsu ALLAH ya tsayar damu a kotunsa, dan yafi kowa sanin gaskiyar abinda ya faru”.
Kuka nake sosai, wanda har su mama sai da suka koma lallashina, ganin dare yayi suka lallaɓani na komo gida.
A falo naci karo da Yah Qaseem, da alama dai ɗakinama yaje bai ganniba, na share hawayen dake gudu a fuskata, ba tare dana kallesa ba nace masa “Ina yini”.
Cikin kafeni da idonun da nakeji suna yawo a kaina ya amsa mani, ya ɗora da faɗin, “Ina kikaje haka? Na leƙa ɗakinki nama zata ko kina bathroom ne?”.
Kaina kawai na girgiza masa amma na kasa magana, hakan ya sakashi takowa gabana dab, baya na matsa dan banason sunamin irin wannan abun haka.
Kafin yay magana nai saurin faɗin, “Kaina ke ciwo Yah Qaseem, ina daga baya ina shan iska dan ina tunanin zafine”.
Kamar bai gamsu ba, sai kuma cayay, “Okey to ALLAH ya ƙara sauƙi, kinsha magani ko?”.
Kaina na ɗaga masa..
Yace, “To kije ki kwanta, dama nazo naji miya dawo dake gida keda ke shirin dawowa gaba ɗaya”.
Sai da na raɓashi zan wuce sannan nace, “Babu komai, da safema idan ALLAH ya kaimu zan koma, dama abu na manta kuma ana buƙatarsa shine nazo ɗauka”.
Banji amsar daya baniba, dan tuni na shige, nakuma dannama ƙofata key dan karma yace zai biyoni.
Jingina nai da ƙofar ina kuma fashewa da sabon kuka saboda tausayin Amina, inhar zasu iya cutar da yarinyar data ɗauki tsahon shekara tara tana musu bauta to ni ta yaya zan tsira a wajensu? Miyasa zasuma Amina haka? Duk taka tsantsan ɗin yarinyarnan da riƙon addininta da martaba, Amina ko zama babu hijjab batayi a gidan, duk zafi ta gwammaci haƙuri ta zauna a hakan duk dan gujema irin wannan ƙaddarar, “Wane tsinannene ya aikata wannan aikin? Sai yaushene ƴan sandar ƙasarmu zasu ajiye kuɗi su ɗauki gaskiya? sai yaushene masu kuɗin ƙasarmu zasu fara yarda da kuskuren ƴaƴansu su ajiye son zuciya!!” na ƙare maganar da zubewa a ƙasa ina mai tauna leɓena alamar jin zafi mai yawa a zuciyata.
Ni kaina bansan tsahon lokacin dana ɗauka ina kukaba, ban taɓajin takaicin sakacin Dad ba irin yau, dan inaji a jikina koni akaima abinda akayiwa Amina bazai ɗauki matakiba, a halin yanzu kuwa ai nice a halin hau, dan kuwa zasu iya min kwatankwacin yanda sukai mata.
Kuka dai na yisa harna rasa hawayen zubarwa, rayuwar gidan haya da talauci, maraicin iyaye, matsalar Jazuga, haɗarin tsintar kai a matsayin mai kisan kai, faɗawa hannun su Uwargida, kuncin zama gidan Inna zainaba, duk sun faru, yau kuma ga jin daɗin da cigaban rayuwa amma cike take da ƙalubale kala-kala tare da firgicin rashin tabbas, shin mutanen duniyane a haka? Kokuwa duniyarce a haka?, wanene zai bani amsar wannan tambayar ko zata zamemin hasken fahimtar cuɗaɗɗun al'amuran cikinta?.Yanda naga rana haka naga dare, sai gabannin asuba barci yaɗan saceni, hakan yasa na tashi a makare, ina yin salla nai shiri a gurguje, banama son ganin kowa a gidan har Dad ɗin kansa, dan haka na rubuta masa text message akan na wuce dan yau ina da jarabawa, naji bazan iya kwana biyun da nai niyyaba sam.
ALLAH ya soni sanda na fito ana wankema Yah Qaseem motane, bai kai ga fitowa ba.Gidansu Amina na shiga, mama na tsakar gida tana damun kunu, na duƙa na gaidata, cikin bina da kallo da takeyi tace, “Bilkisu miya sami fuskarki haka ne?”.
Murmushi nayi ina haɗiye kukan dake shirin zomin, nace, “Babu komai mama, zan koma makarantane, amma insha ALLAHU baifi nanda kwanaki goma zamu dawo gaba ɗaya ba, akwai wani likita zaizo har gida ya sake duba jikin Amina, insha ALLAHU zai bata dukkan taimako, na kuma muku alƙawarin koba yanzuba saina binciko wanda ya aikata wannan ɓarnar kuma an hukuntashi insha ALLAHU”.
“Ah ah Bilkisu, karki saka rayuwarki a haɗari kinji, koma wanene mun barsa da ALLAH, zai saka mana, mun gode da nuna kulawarki a garemu”.
“Mama barin wanda ya aikata yaci bulus shine yake nuna na gama saka kaina a haɗari, dan abinda akaima Amina, nima zasumin kwatankwacinsa ai, ke dai kimin addu'a kawai”.
Addu'oin fatan alkairi mama ta shiga jeramin, kafin tace na zauna na karya, haƙuri na bata akan bazan iya cin komaiba, sannan inason na wucene dan banason wani yace zai kaini a gida.
Haka na wuce bayan na leƙa na duba Amina dake barci, a motarma lokaci-lokaci haka naita share hawaye, har ALLAH yasa na iso lafiya.
★★★★★
Shigowata gidan duk sai suka taho da murnar tarata, sai dai kuma duk sai sukai turus suna kallona.
Zuhrah tace, “Bily lafiya kuwa? Kinga fuskarki a madubi safiyar yau? K..........”
Kafin takai ƙarshe Rebecca ta amshe da cewa, “Ku wannan kuka ne, Bily miya faru?”.
Duk sun rikice, Nazifa da Ummie sukazo suka kama hannuna, ni dai ban iya bama kowannensu amsaba, kallonsu kawai nake tamkar wata gunki, hakan ne ya ƙara tada musu hankali.
Dai-dai Gwaggo hari ta shigo gidan, da gani daga wani waje take, itama da mamaki take kallona, sai dai batace komaiba har muka shige.
Rufeni sukai da tambayoyi har Gwaggo Hari, sai ma na rasa nawa zan amsa.
Ganin sun matsa ne nace musu banajin daɗinefa, subar ɗaga hankalinsu.
Badan sun yardaba suka barni.............✍🏻ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...