Shafi na ashirin da huɗu
..............Tabbas ran Jawaad a ɓace yake, amma baka isa fahimtar hakan a kan fuskarsa ba, kusan mintuna talatin ya ɗauka zaune kafin ya miƙe da shirin tafiya, a cewarsa zaije ya dawo.
Da kallo duk suka bishi, idon Aamila tamkar zai faɗo ƙasa kuwa, gani take tamkar abinda suka aikata zaije ya binciko.
Salman ya sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Wai miya kawo wannan matsalarne?”.
Jack da Aamilah suka kalli juna kawai, kowanne na haɗiyar yawu da sauri, dan basusan amsar da zasu bama Salman ɗinba kuwa.Dad kam sama ya nufa yace Mummy tazo yana son ganinta.
Koda suka ƙarasa ɗakinsa sai ya turke Mummy da tambayoyi.
“Aysha mi kuke ɓoyewane?”.
“Kamarya Dadynsu?”.
“Ya ina tambayarki kina tambayata? Yanayin yaron nan kawai ya tabbatarmin akwai wani abu dani ban sanshiba, sannan namiki tambayar miya kawo sanadin zubar jinin, kincemin kema baki saniba, tana ɗaki tana barci, amma gashi shi kin sanar masa faduwa tai da takalmi, minene gaskiyar zancen?”.
“Wlhy Dadynsu nima sai da na faɗa ne na fahimci nayi kuskure, amma kamar yanda na sanar maka bansan minene sanadinba, dan tana ɗaki kwance ne”.
Kai Dad ya dafe yana bubbugawa, itama Mummy zama tai ta sake zabga tagumi tana zancen zuci, babban fatanta ace kawai cikin nan bai zubeba.
Sai dai ita kanta zuciyarta na rawa akan kar dai Shahudah bataji ƙwaɓar da sukai mataba sai da ta aikata ƙudirinta kamar yanda take buri tun farko akan cikin?.
‘Innalillahi, kai amma da yarinyarnan ta cucesu wlhy kuwa’.Likitocin nan sai da suka samu dai-daituwar komai sannan suka fito, har lokacin Dad da Mummy basu sakkoba.
Aamilah ta matsa kusa da Doctor ɗinsu, catai yazo zasuyi magana dan ALLAH, tashi yay sukai waje, babu wanda yasan mita faɗa masa, kusan dai mintuna goma sai gasu sun dawo falon.
Itace ta haura sama ta kira su Mummy, Doctor yay musu bayani cewar cikin jikin Shahudah da dai ya zube.
Tambayar farko da suka haɗa baki wajen jefo masa shine, “Minene sanadi?”.
Jimm kaɗan yay kafin yaɗan gyara zamansa, ya ce, “Eto Alhaji matsalar dai kamar daga mahaifarta ne, dan bata da ƙwarin riƙe abu mai nauyi, yanzu kuma cikinta ya shiga wata na uku, shiyyasa ya fara nauyi kaga”.
Kai Dad ya jinjina daga shi har Mummy sun gamsu da hakan, sai yanzu yakejin zargin da yake ya bar ransa, ya gamsu da bayanin matar tasa, amma kuma tayi gangancin cema Jawaad ɗin takalmine ya kada Shahudah.
Itako Mummy dai can ƙasan zuciyarta kamar tai hauka takeji, dan gaba ɗaya kalmar zubewar cikin nan ta gama birkita mata lissafi, kallo ɗayama zakai mata ka fahimci bata a cikin nutsuwarta.
Shi dai Doctor yay musu ƙarin bayani akan idan Shahudah ta tashi, tare da cewa zaije asibiti, idan ya taso aiki zai biyo ya kawo mata magunguna.★★★★★★
Koda Jawaad ya koma Office harkokin gabansa ya cigaba dayi tamkar babu abinda ke damunsa, sai ɗan ciwon kai da yake danganta nasabarsa da jininsa da aka ɗiba, maimakon kuma ya samu nutsuwa ya huta sai hakan ta gagara, dan bayan kamar awa biyuma Asibiti sukaje shi da Hafeez duba Alhaji Kokino da jikinsa yay ƙyau Alhmdllh.
Dukkan iyalansa na wajen, Shema'u ganin Jawaad jikinta har ɓari yake, shiko batasan yanada abinda kecin ransaba, koda ta gaishesa hannu kawai ya ɗaga mata ko kallon arziƙima bata samu daga garesa ba.
Basu wani jimaba suka baro asibitin, kasancewarsu ƴan sandan farin kaya, ba kaki suke sakawa ba sai babu ruwan kowa dasu, babuma wanda ya kawoma ransa ƴan sandane su, sai dai iyalan Alhaji Kokinon da suka sani.Bai sake waiwayar gidansu Shahudah ba sai da ya tashi aiki, daga nan ma ɗin gida ya wuce, yay wanka ya kimtsa bayan yasha tea daya zame masa amini yanzu, ya fito cikin kayansa masu taushi farare masu tambarin Adidas, ƙamshinsa yake fitarwa a hankali.
Yauma da kansa ya tuƙa motar zai fice, a gate sukai karo da yaron Kawu Saminu Mas'ood, sauke gilas ɗinsa yayi kamar yanda Mas'ood ɗin yay shima, cikin mutuntawa suka bama juna hannu kowanne yana daga mota bai fitoba sukai musabaha, kowa na tambayar iyalan ɗan uwansa.
Daga haka Jawaad ya fice Mas'ood kuma yay ciki.
Redio ya saka yana saurare harya isa anguwar su Shahudah dake shiru babu hayaniya, duk da babu wutar lantarki ko wanne gida zaka samesa da hasken janareto tunda anguwar duk irinsune masu hannu da shuni.
Yanayin Horn mai gadi ya buɗe da hanzari, dan cayake burkutaccen nanne Qaseem.
Salman da jack na zaune a harabar gidan can gefe, Dukansu kowa da sigari a hannunsa yana zuƙa suna fira.
Salman yay saurin jefar da tasa ya take da ƙafa saboda ganin motar Jawaad.
Nesa dasu kaɗan yay fakin, dukda ya gansu ko kallo basu ishesaba ya rufe motar yay ciki abinsa.
Babu kowa a falon gidan, amma tv nata ɓaɓatu, tsaye yay yana bin falon da kallo kamar wani baƙonsa, hannayensa dukansu na cikin aljihun wandonsa.
Aamila ta fito daga kicin hannunta ɗauke da kofin tea da kuku ya haɗama Shahudah ta amso mata.
Sosai ta firgita da ganin Jawaad, yanda tai bayama kaɗan ya rage ta zubda shayin.
Ɗauke idonsa yay daga kanta tamkar baiga halin data shigaba.
Sannu tai masa, bai amsaba sai kansa kawai ya gyaɗa mata, cikin in ina tace ya hawo sama Shahudah nacan.
Duk da yayi ɗan mamakin miya maidata sama bayan yasan ɗakinta a ƙasa yake, amma sai bai ce uffanba yabi bayan Aamilah.
Aamilah ce ta sanarma Mummy da zuwansa, Mummy taɗan ɗaga murya tana faɗin ya shigo mana.
Jawaad dake ƙofar ɗakin tsaye duk yana saurarensu tura ƙofar yay ya shiga da sallama.
Kallo ɗaya yayma Shahudah dake kwance a gadon dan bata daɗe da farkawa ba, ta daiyi wanka dan ɗaure take da tawul fari, daka ganta kasan batada lafiya dan tayi zuru-zuru, ta ƙara haske sosai ga idanuwa sun kuma yo waje.
Gaisar da Mummy data miƙe yayi, ta amsa suna ficewa ita da Aamilah daga ɗakin.
Tunda suka fita saiya shiga bin ɗakin da kallo tamkar ya ajiye wani abu a ciki, hakan ya saka itama Shahudah ta bisa da kallo ƙirjinta na wani bugawa kamar zai fito.
Kusan minti ɗaya yana kalle-kalle kafin ya koma baya. jingina yay da bango hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa, ƙafarsa ɗaya ajiye a ƙasa ya tokara ɗayar jikin bango, ya tsurama jojo karen Shahudah dake kwance kusa da ita ido ko ƙyaftawa bayayi, sai faman cizon leɓensa na ƙasa yakeyi.
Shahudah da duk jikinta babu ƙwari ta miƙe zaune da ƙyar ta jingina da filo, kofin gefenta ta ɗauka tana juya cokali cikin shayin da Aamilah ta kawo mata, ta ɗago idanu ta sake kallonsa, “Bb ka zauna mana” tai maganar a matuƙar sanyaye.
Ƙala baice mataba, sai ƙafarsa daya sauke yana cigaba da kallon jojo.
Ya tako a hankali zuwa gaban gadon ya tsaya a kanta, sai kuma ya ɗora tsaftatacciyar ƙafarsa saman gadon yana zuba mata idanunsa da suka canja launi baki ɗaya.
A bazata tajiyo muryarsa kausashe yana faɗin,
“Wane likitane yay wannan aiki?”.
Dakewa tai cikin nuna halin ko in kula tace “Wane ai kuma Bb? Kainefa ka bani jini, kuma doctor ɗinmu ne ya ɗiba, wane kuma aiki kake buƙatar sanin wanda yay bayan wannan?”
Ƙafarsa ya sauke ƙasa yana sakin wani murmushin daya saka zuciyar Shahudah harbawa da ƙarfi.
Kujera ya jawo ya zauna, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, ya kuma tsuke fuskarsa yana kafa mata rikitattun idanunsa, “Hudah kinsan sunan aikin ɗan sanda kuwa?”.
Kanta ta girgiza masa a hankali, yanayin da fuskarsa take ya sake ruɗata.
Sauke ƙafarsa yay ya ɗan ranƙwafo yanda zasu ƙara samun kusanci, cikin magana ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ya kaɗa mata yatsun hannunsa biyu yana kuma fiddo idanu waje sosai yace, “Wasa ƙwaƙwalwa. Dan haka ki faɗa min minene gaskiyar zance akan cikina?”.
Babu shiri Shahudah ta saki kofin shayinta a ƙasa, ya zube kofin ya tarwatse, jikinta sai ɓari yake, murya na rawa tace, “Bb wace irin magana ce wannan? Kana zargina nina zubar kenan?”.
Wani murmushi ya sakar mata yana bin kofin dake tarwatse a ƙasa ga shayin ya jiƙe musu ƙafafu da kallo, ya wani wulƙita idanu luuu yana maido dubansa gareta har lokacin fuskarsa da murmushi wanda ita tasan ma'anarsa sam bana farin ciki bane, ya janye ƙafarsa daga laimar ruwan yana miƙewa tsaye.
Key ɗin hannunsa ya shiga kaɗawa yay taku ɗaya biyu kamar zai nufi hanyar fita sai kuma ya juyo gareta yana nunata da key ɗin.
“Hudah nai miki farin sanin da inaga ko iyayenki basu gama nutsuwa sun mikiba, tun muna mu biyu a ɗakin nan ki faɗamin da haɗin kan wa kika aikata?”.
Cikin son kare kanta ta aro jarumtar dole ta fara masa bayanin abinda likitansu ya faɗa.
Uffan baice da itaba ya zaro handkherchief a aljihunsa yana rissinawa ya ɗauki wani abu a ƙasa, takowa yay ya dawo gabanta, ƙafarsa ya maida a saman gadon ya nuna mata syringe ɗin daya ɗaukko.
“Ki bani amsa da gaggawa kafin nakai maƙura, Wane likitane ya bada?”.
Karon farko a rayuwar Shahudah da taso karanto wata addu'a a harshenta saboda tsagwaron tashin hankali da ruɗani, sai dai batama san miya kamata ta karantan ba tunda ba addu'oin ta saniba.
Kanta ta shiga girgiza masa tana hawaye da matsawa baya, “Bb ni bansan komaiba wlhy, wannan abun bansan wanene ya kawosaba, sai dai idan likitocin nan suka yardashi by mistake, ka yarda dani dan ALLAH”.
Cikin halin ko in kula yace, “Ba dolema na yarda dakeba ƴammata” yay maganar yana ɗaukar leda a saman mirror ɗinta ya saka sirinjin, ko kallonta bai sake yiba ya juya ya fice daga ɗakin cike da izzar da ɓacin rai ya haddasa masa.
Da ƙarfi Shahudah tai yunƙurin miƙewa tsaye danta bisa, sai dai rashin ƙwarin jiki yasa jiri ya kwasheta ta koma saman gadon yaraf ta kwanta hawaye na gudu saman fuskarta, ita kanta a yanzu jitai tana buƙatar cikinma, kodan tashin hankali da tsagwaron bala'in data hango cikin idanun Jawaad.
Mummy da Aamilah na falon, sai dai Aamilah ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kaikawo take tsakanin kujeru, gaba ɗaya yanayin Jawaad ya kuma tsoratata.
Duk da ac dake aiki a falon ita zuface ke tsatstsafoma goshinta.
Sarai Mummy ta lura da halin da Aamilah ke a ciki, amma ta kasa tambayarta mike damunta, dan tunda aka shaida musu cikin nan ya faɗi komai ya sukukuce mata, ko mama Atika ta kasa kira ta sanarmawa balle sauran ƴan uwanta......
Sakkowar Jawaad a fusace daga sama ya katse mata tunani, daga ita har Aamilah suka zuba masa idanu kamar yau suka fara ganinsa.
Baiko kallesu ba yay ficewarsa saboda shiyasan shika-shikan rashin mutuncin daya shiryama kowa a gidan akan cikinsa.
Sosai abinda Jawaad yayi ya kuma birkita zuciyar Mummy, hakama Aamilah da tasan dokar.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...