46

15.1K 1.2K 212
                                        

Page 46

..................Tsaf muka kammala komai tare da shi, kiran sallar zuhur da akayine ya sakashi fita ya barni ina ƙarasa sauran abubuwan. Nima a gurguje na ƙarasa komai na fito yin sallar. Na idar kenan ina addu'a naji ana sallama, kafin na miƙe na fita ganin wanene Nabeelah ta shigo ɗakin.
Murmushi mukaima juna, ta ƙaraso ta rungumeni tana faɗin "Amarsu ta ango mai daɗin suna, bara na faɗa a hankali kar yauma nai suɓutar baki ya jini ya markaɗa". Dariya ta bani sosai, dan haka na shiga yi. "Hum ke dariyama abin ya baki, wlhy kaɗan daga aikinsa yamin casar gyaɗa indai yayanmu ne. Ina fata baya nan?". Toilet na nuna mata da ahannu ina faɗin, "Yana ciki kuwa". Sosai ta waro idanu waje da faɗin, "Na shiga Uku dan ALLAH da gaske kikeyi?". Yanda ta rikice ɗinne ya sakani sakeyin murmushi, na ajiye abin sallar dana linke, "Wai ke kaɗai kikazo ne?". "A'a ni da su Ummah ne fa, suna falo". Ban bata amsaba na fito batare dana cire hijjabin ba.
Tunda na fito suka zubamin idanu har abin ya bani kunya, na ƙarasa inda suke kaina a ƙasa, har ƙasa na durƙusa inai musu sannu da zuwa. Cikin fara'a suka amsamin har suna haɗa baki wajan faɗin nazo garesu. A kunyace na kuma tashi naje gabansu dab zan sake tsugunnawa Ummah babba ta riƙoni, tsakkiyarsu ta zaunar dani tare da rungumeni jikinta tana sauke wani nannauyan numfashi daya bani mamaki matuƙar gaya, itama Ummah ƙarama saita riƙo hannuna da faɗin, "ALLAH yaymiki albarka kinji, lallai ƙaunar da muke miki da gaske ta wuce ta surukuta kawai". Ban fahimci zancen nataba nidai, na ɗago daɗan satar kallon Ummah babba da naga kamar tana hawaye. Kaina na maida a ƙasa nace, "Bara na kawo muku ruwa".
Ummah ƙarama da itama na ga tana share hawayen tace, "Bara mu fara yin salla ɗiyata, dan ta riskemu a hanya saboda go-slow ɗin garin nan da baya ƙarewa". Kaina na jinjina musu tare da miƙewa nai musu jagora har cikin ɗakina. Sai da na saka musu abin salla sannan na fito dan na basu waje suyi.
Kwance na iske Nabeelah na danna waya, na zauna kujerar dake kallonta, "K bazakiyi sallarba madam?". Wayar ta janye daga fuskarta tana tashi zaune, "Aini shehi yamin". Nace, "Okay to acigaba da gashi". Dariya ta sanya tana ƙoƙarin komawa ta kwanta, ni kuma na miƙe dan naje na shirya abincin a dining, harna miƙe na dawo na sake zama. "Nabeelah niko kinga abinda na gani kuwa? Saifa naga kamar su Ummah kuka sukai?". Kallona tai tana murmushi, "Nima dai ba komai na saniba akai, amma tabbas akwai wani abu da suka sani game dake wanda na lura shine dalilin kukan nasu". Babu shiri na koma na zauna a kujerar sosai ina faɗin, "Game dani kuma Nabeelah?". "Lah bafa wani abu mara ƙyau bane naga kamar kin ruɗe". Ajiyar zuciya naɗan sauke duk da bawai na gamsu da amsar tata bane, na sake miƙewa na nufi kitchen. Abincin dana shirya a kuloli na fara fiddowa, ganin hakan Nabeelah ta taso ta tayani muka shirya komai. Falon muka sake dawowa muka zauna, Nabeelah ta fara zubamin surutu, nidai nawa murmushi ne, wani gurin kuma nakan jinjina wautarta sosai. zamanmu baifi da mintuna goma ba su Ummah suka fito, miƙewa nai ina musu sannu. Fuskokinsu ɗauke da murmushi suka amsamin suna zama. Ina fara zuba musu ruwan dana ajiye ya shigo falon da sallama.
Tsokanarsa suka shigayi da faɗin ga ango ga ango. Yay murmushi mai sauti cike da girmamawa yace, "Sannunku da zuwa Ummahs, har ina tunanin kiranku a waya sai kuma na duba naga nama bar wayar a gida".
Ummah ƙarama tace, "Wlhy Go-slow ne ya riƙemu Son, amma da tuni mun iso ai". Ledar hannunsa na amsa ina masa sannu murya ƙasa-ƙasa, ban jira amsarsaba ko kallonsa nabar wajen.

Jay daya ɗan bita da kallo ya zauna yana amsa gaisuwar da Nabeelah ke masa, kafin ya gaida iyayen nasa da keta tsokanarsa yayi ƙiba a kwana uku kacal. Shidai murmushi kawai yake musu bai iya cewa komai.
Nabeelah data san halin kayanta kuwa tuni ta miƙe tabi bayan Bilkisu dake kitchen tana wanke fruits ɗin daya shigo dashi. Tare suka ƙarasa suka fito.

Koda nazo na sanar musu cewar ga abinci sai Ummah babba ta hau faɗa akan miyasa zan fara girki, ai sai nayi sati biyu sannan. Murmushi nidai nakeyi kawai kaina a ƙasa, shima dai banji yace wani abu ba. Sai da ta gama faɗanne sannan naji ya bata haƙuri da cewar, "Ummah karki damu ai gara tayi, dan bazai yuwu muyita wahal dake ba". Ummah tace, "Minene wani abin wahala anan, aida nasan zatai girkin dana kira nace karma ta fara".
Shidai ya lallaɓasu akan suzo suci abinci, daga baya saita cigaba da faɗan. Dariya Ummah ƙarama da Nabeelah sukayi jin furcinsa, nima dai saida na murmusa. Ni da Nabeelah muka zuzzuba musu abincin yanda kowa yake buƙata, Nabeelah ma ta zuba nata ta zauna, niko sai nai ƙoƙarin barin wajen, hannuna Ummah ta kamo ta zaunar dani a kujerar kusa da ita, "Maza zauna kici abinci, kina nufin mu kaɗai zakima wannan wahalar". Kaina a ƙasa nace, "Ummah ai na ƙoshi, in ALLAH ya kaimu anjima zanci". Bata saurareni ba ta hau ɗiba da cokalinta ta fara bani, bazan iya mata musu ba, dan haka dole na ringa amsa a kunyace, Nabeelah nata mana dariya ƙasa-ƙasa dan tana tsoron yi yaci ƙaniyarta. Dana ɗago saina kamashi yana kallonmu, hakan yasa na ƙara takura sosai. Ummah bata barniba saida ta tabbatar cikina yayi ƙat da abincin nan, suma sukaci sosai suna santi da sakamin albarka da yaba ƙoƙari na.
Bayan mun kammala Nabeelah ta tayani gyara wajen, shi kuma ya zagaya dasu lungu da saƙo na gidan, inajin yanda suketa yaba gidan da jinjina halin girma irin nasu Ummu, a yanda suka hidimtamin babu dangin iya babu na baba sun cancanci yabawa mai girman gaske da ƙyaƙyƙyawar addu'a.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Onde histórias criam vida. Descubra agora