Shafi na talatin da ɗaya............A ɓangaren Shahudah kam taci alwashin sai Jawaad yazo ya nemeta har inda take, dan a nata hasashen gwala rayuwarsa take a haka.
Tasan ɗunbin son da yake mata dolene ya jigatu da rashinta, shekaru biyar ta ɗiba masa cif, sai ya koma ƙaramin mahaukaci a kanta sannan ta bayyana a garesa.
A shirmenta ko ganin ta cinye shekaru biyu bai nemetaba baisa taji a ranta akwai matsalaba, a'a a ganinta kawai ya rasa hanyar da zai iya ganintane, tunda Mummy ta tabbatar mata Jawaad baisan inda takeba har yanzu.
Ita kuma duk motsin Jay Mummy tana sanar mata komai harma Aamilah da Salman, wani lokacinma harda Qaseem, ko dangane da tafiyar Jawaad Qaseem ne ya sanar mata komai.
A duk sanda akai mata zancensa danne zuciyarta kawai takeyi, amma kewarsa da ɗunbin begensa kullum sake mamaye zuciyarta yakeyi, batason ya kalleta matsayin mafi arha a mata shiyyasa tai dauriyar riƙe ajinta gam tunda ta ƙetaro kasarsu tai kunnen uwar shegu dashi, sai dai a kullum hotonsa shine abin kallonta, hakama duk wata kafar yaɗa zumunta datasan yanada accaunt a wajen tana bibiyarsa da sunan da ba nataba.
Ta kasa kula kowane saurayi, ta dai yarda kuyi abota amma ba soyayyaba, to kuma dama can dai gaskiya Shahudah bata iskanci, koshi Jay shaidane akan cikakkiyar budurwa ya sameta, dama can iskancinta baya wuce shan minti, amma bata yarda tarayya da waniba, takance wannan mallakin Jay ne tunma a wancan lokacin, to a yanzunma dai da harma yanzu take ɗauka da aurensa kanta tana taka tsantsan, sai dai fa iya shege da duk wani dandali na taruwar wayayyu tana a wajen babu abinda ya dameta, tunda bawai muhimmancin auren ta saniba balle ƙa'idojinsa, a ganinta duk abinda takeyi ƴancinta ya bata damar yin hakan, balle ta dawo inda babu ruwan wani da wani.A gurguje⛹♀😏
_________________________
BILKEESU
_________________________Rayuwa tai nisa, sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun zama yini, yini ya rikiɗa dare, kafin wani dogon nazari daren ya haɗa kwanakin da suka bada satittikan da suka dunƙulle wattani, sai gamu da shekara ɗai-ɗai har huɗu cif a makaranta, yanzu haka jarabawa biyu kacal ta rage mana kammala jarabawar ƙarshen zangon karatunmu na.
Abubuwa da dama sun faru, wasu a iya tunawa, wasu ko zuciya ta manta saboda hidimomin yau da kullum, mun kwankwaɗi madarar ilimi wadda muke addu'a da fatan ta zamewa rayuwarmu dana ƙasa damu alkairi.
Zakusha mamaki idan kukaji a cikin baƙin al'amuran da suka zoma rayuwata ciki harda soyayyar Yah Qaseem datai ƙarfi a tsakaninmu,
Hoo duniya makarantar makaho, kai mai idonma ba ɗage masa ƙafa takeba, wai ni Bilkisu ƴar baƙa mummuna ƴan ƙwalisar samari masu ji da ƙyawu da ƴan canji a aljihu irinsu yaya Qaseem keso? To lallai dai abin da mamaki, sannan yana buƙatar alamar tambaya, shin sone na gaskiya? Kokuwa sone na sha'awa?.
A wannan kaftawar da zamu farane kawai kowa zai iya fahimtar hakan, danni dai har yanzu baiji amsa tayinsa daga bakina ba.
Dan duk wani salon rayuwa da iya zama da jama'a a yanzu Alhmdllh na san gwargwadon ilimin da UBANGIJI ya bani.
Maza da yawa surar da ALLAH ya bani ke ɗibarsu zuwa gareni, ba wai ƙyawuba, duk da ƙoƙarin killace jikina da nake ban tsiraba a wajen mayu irinsu Yah Qaseem._________________________
Uzirin gaggawa ya sakani dawowa gida a weekend ɗinnan domin ɗaukar abinda na manta, babu wanda yasan da zuwana, dan motar haya na shigo.
Tun isowa gidan namu gabana ya faɗi, dan kuwa da motar ƴan sanda naci karo, na tura ƙaramar ƙofar gate na shi da sassarfa, dama dagani sai handbag ɗita.
Zan shigo ƴan sandan zasu fita, dan haka suka bani hanya saboda na riga na kawo jiki, koda na shigo sukuma sai suka fice, na bisu da kallo kafin na maido kan Amina dake ta faman kuka ga mamanta itama tanayi.
Sai Dad da Mummy dake tsaye sunata faman faɗa akan maza su Amina su fice musu da ga gida, inba hakaba zasu bama ƴan sandan da suka fice dama su tafi dasu.
Gaba ɗaya ban fahimci yaren kowa a cikinsuba, na sake maida dubana ga Yah Salman dake kan mota zaune yana wani munafukin murmushi, Aamilah na daga gefensa tana latse-laste a waya.
Nai saurin ƙoƙarin riƙo hannun Amina da suke ƙoƙarin fita, amma sai ta fisge a fusace harda bigemin hannu ta fice.
‘Lallai akwai matsala’ na ambata a zuciyata ina binsu da kallo har suka fice......
Kiran da Dad ke minne ya katse tunanina, na sauke ajiyar zuciya ina nufarsu hankalina duk a tashe da tunanin mi akaima Aminar?.
Ina isowa gabansu Dad abinda ya fara faɗamin shine, “Ƴata rabu da waɗancan masherantan mutanen kinji, dan ba mutanen arziƙi bane masheranta, duk ƙyautatawar da mukaima rayuwarsu sai suka ƙare da nemanmu da sharri”.
Duk da bansan kan al'amarinba sai naji kalamun dad basumin daɗi ba, dan haka nai murmushin yaƙe kawai ina faɗin, “Wani abune ya faru Dad?”.
Kafin ya bani amsa Mummy ta katsesa da sauri, “Daga shigowarki Bilkisu, ki shiga ki huta mana koma minene zakiji daga baya”.
Kaina kawai na iya ɗaga mata, suka shiga ni kuma nabi bayansu.
Dad dake zama a kujera yay min tambayar lafiya nida nake ƙoƙarin zana jarabawa ta ƙarshe nazo gida?.
Sai da na durƙusa a gabansu na gaishesu sannan nai masa bayanin abinda ya kawoni.
Ganin ya gamsu da maganatane ya sakani miƙewa na nufi ɗakina, dan duk tunanina a dagule yake da abinda na gani, sam zuciyata ta kasa yarda su Amina ne basu da gaskiya. Akwai dai abinda tabbas shi Dad bai saniba an ɓoye masa.
Har nai wanka na fito domin cin abinci wannan lamari na sukata, babu kowa a falon na wuce kicin, a can ɗinma ban samu kowa ba, to dama wa zan gani? Amina ce dai da kuku kuma ga ayanda na iske gidan.
Babu komai a kicin ɗin, amma da alamun dai anyi abinci, fitowa nai dan na san yana Dani, ilai kuwa a can na hangosa, tunani baisa hankalina ya fara kaiwa canba.
Ɗiba nai na koma ɗaki kawai, duk da uwar yunwar da nakeji sai kuma nama kasa cin abincin, dan laumata ɗaya jal na ajiye cokalin ina sake karanto damuwar dake tattare da Amina.
Amina ta taka rawar gani a rayuwata ta gidannan, dan ta soni a lokacin da kowa ya tsaneni, ta ƙaunaceni a lokacin da kowa ke ƙyanƙyami na, to ni tayaya yanzu zan sami nutsuwa a halin da take ciki?.
Bani da ikon fita gidan a yanzu, amma nayi alwashin zuwa anjima ko a sacene sai naje gidansu Amina.
Da ƙyar naci rabin abincin dana ɗebo, na zuba tagumi ina cigaba da saƙawa da kwancewa.Bayan sallar isha'i na fahimci gidan yayi shiru, a hankali na leƙo falon, babu kowa a ciki, yau ko tv ma ba'a kunnaba, cikin sanɗa na nufi kicin, ta ƙofar baya na fita a hanzarce zuwa harabar gidan, nanma sai da na wawwaiga na tabbatar babu mai kallona sannan na nufi gate.
Baba mai gadi ya taso yana tambayata ina zanje, saurin masa alamar yay shiru nayi, murya ƙasa-ƙasa nace, “Gidansu Amina zanje baba, dan ALLAH ko wani ya tambaya karkace na fita, duk da nasanma da wuya asan bana nan”.
Kansa ya ɗagamin, ni kuma na fice da sauri...............✍🏻ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...