44

17K 1.3K 656
                                    

Page 44

Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
          Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘


....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama, Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.

★★★★★★

         Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad, ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”. “Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin sanarma maman.
       Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito. yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan, mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
         “Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
            Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”. “Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama, kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”. “Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”. “Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”.  “ALLAH ya bada iko to, drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”. “Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama, binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
      Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna, Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari, kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan ne?”. “A'a babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
     Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi, bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”. Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now