Page 29
...............Yanzunma dai saida taje gab da yankewar aka sake ɗagawa, sai dai yanzu ba'ace komaiba, cikin ɗan zafi-zafi Jay yace, “A wane asibiti ne?”. Ɗan jimm wancan yay, sai kuma cayay General”. Yanke wayar kawai Jay yayi batare da shima yace komaiba, maida akalar kiran yay ga Jabeer, bigu biyu ya ɗauka, bayan sun gaisa Jay yace ya fiyo zasu fita. Iyakar abinda yace kenan ya katse kiran ya miƙe, rigar suit ɗinsa daya cire tun shigowarsa yay hanging a bayan kujerar zamansa ya ɗauka, tare da ƙaramar bindiga ya tura a gefen ƙugunsa ya fice.
Tare suka fita shi da Hafiz da Jabeer, dan Aliyu akwai aikin da yakeyi. Koda suka isa General hospital emergency suka nufa kai tsaye, tunda ance Accident can tunaninsu ya fara basu su duba farko. Hafiz ne yay tambaya duk da basu da tabbas ɗin cikakken sunan ɗan-Fir'auna bayan Habib, sudai ma'aikatan asibitin dake Emergency ɗin basu ganeba, amma alamun da suka gani na cewar su hafiz jami'an tsarone yasa doctor zagayawa dasu kaf gadajen dake cikin Emergency room ɗin suna dubawa, babu ɗan-fir'auna anan ɗin. Doctor yace, “To akwai dai wani da aka kawo tunda safe yayi accident, mun bashi ɗaki awa ɗaya data wuce, al'amarinsa akwai ruɗarwa, daga baya ƴan uwansa sukazo suka ɗaukesa duk da yana cikin mawuyacin hali”. Jabeer ne yace, “Suka ɗaukesa kamar ya? Baiji ciwo bane?”. “Yaji ciwo sosai yallaɓai, dan ko farfaɗowa ma bai gamayiba mundai dubasa babu karaya sai raunika?”. Kafin Jabeer ya sake magana Jay dake gefe yana latsa waya tamkar ba saurarensu yakeba yace, “Miye sunansa?”. Yay maganarne ba tare da ya ɗagoba, dan yasan idan har Dr Tayyeb ya gansa tsorata zai yaƙi faɗar komai.
Dr Tayyeb dai yasha jinin jikinsa akan Jay, sai dai da yake bai ganin fuskarsa da ƙyau sai ya daure yace, “Kamar dai Habibu ƙaura suka bada a jikin katin”. Jay baice komaiba dan ya fahimci dai ɗan fir'auna ne, sai kawai ya nufi hanyar fita. Ganin haka yasa su Jabeer yima Doctor sallama suka biyoshi. Acikin mota suka iskoshi, sai da suka shiga suma Hafiz yace, “Boss yanzu a ina zamu ganosa kenan?”. Jawaad da har yanzu hankalinsa naga waya batare daya ɗagoba yace, “Anguwar kuke”. Tada motar Jabeer yay sukabar asibitin batare da sun sake cewa komaiba, dan sun lura akwai abinda yakeyi mai muhimmanci a wayar.
Sun shiga Anguwar Kuke, inda Jay ya sanar musu dai-dai inda zasu tsaya, a tare suka fita a motar, Jawaad yay gaba suka bisa a baya har zuwa jikin jan gate, gidan bawani gidane mai ƙyauba, dan irin ginin da ɗin nanne, sai dai a da ɗin maishi ya kasance mai arziƙi, a rufe ƙofar take, hakan yasa Hafiz ƙwanƙwasawa. Kusan mintina biyar suna tsaye kafin a buɗe a fusace, kodamar tambayarsu suwanene su? wanda ya buɗe ɗin baisamuba Jay ya turashi gefe ya shige su Jabeer na biye dashi. Duk tsagerancin tsagera idan yay gamo da wanda ya fisa tsageranci nutsuwa ya keyi, hakan yasa saurayin bai iya cewa komaiba ya maida ƙofar ya rufe shima yabi bayansu dan ya gane Jawaad.
Ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya sakasu tsayawa cak a ƙofar falon, dan kuwa gungun samarine da adadainsu zai iya kaiwa goma tsai-tsaye da candles kunne a hannu sun zagaye katifar da Ɗan-Fir'auna ke kwance a tsakkiyar falon, dukansu idanunsu a rufe suke babu mai magana bare motsi. Jabeer da Hafiz ne kawai sukai magana tare da jan birki, Jawaad kam uffan baiceba sai kafawa matasan idanu da yay a ransa yana nazarinsu. Hannu yasa da ƙarfi ya bugi ƙofar falon, a take duk suka dawo hayyacinsu, suka juyo suduka suna kallonsa. Su Jabeer dai abin ya firgitasu, amma a mamakinsu sai sukaga Jawaad ya danna kai cikin falon kamar baiga abinda yake faruwaba. A baɗini shima kuma lamarin ya firgitashi, sai dai ya danne saboda shi mutumne mai kasadar tunkarar abu kai tsaye, ko aiki suka fita duk haɗarin waje baya shakkar shigewa gaba.
Cike da takun nutsuwa Jay ya ratsa ta tsakkiyarsu yana addu'a a ƙasan ransa har zuwa gaban katifar da ɗan-fir'auna ke kwance samɓal jikinsa duk raunika wasu ansa bandage, yay wani irin kukkumburewa a fuska saboda buguwar da yayi. Sai da yay masa kallon mintuna uku kafin ya ɗago ya kalli samarin da suma suka kafeshi da kallo tamkar zasu cinyesa ɗanye. Yi yay tamkar bai fahimci kallon da suke masaba, cikin Kakkausan lafazi yace, “Dami yay Accident ɗin?”. Wanda yake gaba gab da katifar sosai ne ya fara hure candle ɗinsa, sannan ya juya ga sauran yay musu nuni dasu zauna. Babu musu duk suka zauna ƙasa suka tanƙwashe ƙafafunsu hannayensu riƙe da candles ɗinsu har yanzu kuma a kunne. Sake maida dubansa yay ga Jawaad yace, “Yakamata mu fara sanin baƙonmu ai”. Sake ɗaure fuska Jay yayi, kamar bazai tankaba sai kuma ya gyara tsaiwa da faɗin “Nine na kira waya ɗazun”. Karon farko saurayin da babu alamar mutunci tattare dashi yay murmushi da cema Jawaad, “Hutawarka lafiya babba, haɗari yay da mashin yau da asuba, sai dai abin ya haɗa da mabiya sahu”. Jawaad tsaf ya fahimci ma'anar kalamsa, amma sai yay kamar bai ganeba yace, “Amma miyasa kuka ɗakkosa daga asibiti? Suwaye ke bibiyar sawun nasa?”. Gayen yace, “Babba! wannan wasane tsakanin rindunar mafarauta guda biyu, suntaɓo inda za'a maida gayya da gayyane, dolene tsakaninmu a fidda wanene sarki wanene bawa, zasu biya diyyar jini da jini karka damu, koma gefe kawai kasha kallo dan muna respecting ɗinka Babba, aishi sheri ɗan aikene maishi yake komawa, balle idan ka haɗu da waɗanda suka fika iya sherin, zamu zuba dasu muga wazai kwashe, idan har sukaci nasara a kanmu na rantse da jinin babata saina yanke kaina da hannuna da takobin da aikinta kawai shine shan jini”. Kafin Jay ya ƙara magana Ɗan-fir'auna yay wata irin mimmiƙewa da saki razananniyar ƙara data firgita su Hafiz dake a farkon shihowa Falon basu ƙaraso ba, shi kansa Jawaad sai da ya toshe kunensa. Abin mamaki sukam abokan ɗan-fir'auna ko gezau, saima sake miƙewa da sukai da candles ɗinsu a hannu suka kuma zagayeshi.
Bayan wasu mintuna ɗan-Fir'auna yay shiru sai numfashi yake da sauri-sauri, kafin kuma a hankali ya nutsu waje guda numfashin na komawa normal. Sake komawa sauran sukai suka zauna, na ɗazun nan dai me ya sake magana, “Babba karka damufa, nasan akwai harƙalla tsakaninka dashi, zai miƙe nanda kwanaki kaɗan tunda gashi ya farfaɗo, alfarmar da muke nema gurinka kawai likitan dazai dinga zuwa gida kullum yana duba masa waɗanan raunikan”. Cikin haushi Hafiz yace, “Kai kushiga hankalinku, kufaɗa mana abinda ke faruwa?”. Kafin wancan yace wani abu Jay yay wani munafukin murmushi da yima Hafiz magana da ido ya ɗauke kansa tare da nufar hanyar fita. Hafiz ya sake kallon Ɗan-Fir'auna yana mai girgiza kansa, “Shikenan za'a kawo muku likita”. Shima yana gama faɗa yabi bayan Jay ransa a ɓace. Jabeer da baice komaiba sai nazarin kayan dake cikin falon shima yabi bayansu..
Kusan a tare suka fito, suna shiga mota Jabeer yace, “Boss miyasa za'a kawo musu likitan da suka buƙata? Bayan dukkan alamun mutanen banza ya bayyana a garesu”. Numfashi jawaad ya sauke a hankali yana kallonsu, “Wato Jabeer kowane aiki akwai salon da yake zuwa da shi, waɗannan yaran da kake ganinsu duk a tafin hannuna suke, dan duk wani binciken daya dace na kammala yinsa a kansu, mubisu a sannu domin samun abinda muke buƙata yanda ya kamata”. Kai duk suka jinjina masa cike da gamsuwa, dan sunsan bazai jefasu a hanyar da bazasu ɓille ba.
Sunbar anguwar Hafiz da Jabeer nata tattauna al'amarin, Jay kam dai yayi shiru, dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake tattaunawa da zuciyarsa. Jabeer yace, “Wannan duniya nada abin mamaki da al'ajabi da bantsoro, rayuwar waɗannan mutane ta ƙanƙanin lokaci kawai ka gani ta isa saka zuciyarka tsorata da sake tsarkake girman ALLAH”. Cike da damuwa Hafiz yace, “Yaran nanfa kamar ba ainahin musulmai baneba ma, sannan dagani kaga ƴan Cultism”. Jay dai duk dai yana saurarensu, har suka iso station, office ya wuce ya cigaba da aiki biyu, na office dana zuciyarsa. Kalaman abokin ɗan fir'auna yaketa harhaɗawa waje guda da nazarinsu.
Misalin biyar da wasu mintuna na yamma yaɗan fita wani waje, yanason zuwa ainahin inda suka taɓa haɗuwa da ɗan-fir'auna a ranada Gimba ya kawo masa zancen abinda ya gani. sai dai kuma hakan bata samuba saboda yana hanya kira ya shigo wayarsa daga balarabe, a amsa kuwwa ya saka wayar ya amsa masa sallama da gaisuwar da yake masa. “Ka isa garin nasu ne?” yay tambayar wa balarabe. Daga can muryar balarabe cike da damuwa yace, “Ganima harna dawo Alhaji, tun inacan naketa kiranka baka ɗagaba. sai dai baizo gidanba ma ashe, kuma mamansa tace har waya sunyi lokacin dazai taso”. Babu shiri Jawaad ya taka burki, yace, “Kana nufin canba gidaba tun ran juma'ar?”. “Eh wlhy Alhaji hakane”. Mutuwar zaune Jawaad yay a cikin motar, gabansa sai wata irin mahaukacin faɗuwa yake, cikin rawar jiki ya ɗauka wayar ya katse kiran balarabe ya fara laluben Jabeer. Yana ɗagawa ko sallama bai masaba yace, “Jabeer maza dubamin daga ina Gimba yake a halin yanzun?”. Daga can Jabeer yace, “Ƙila matarsa ta riƙesa bata gaji da ganin kayantaba”. A tsawace Jawaad yace, “Jabeer kabar wasa mana!!, ka nemomin yaron mutane Jabeer Please”. Ya ƙare maganar a hankali tamakar zai fashe da kuka. Hankalin Jabeer ne yay matuƙar tashi, baƙaramin girgiza zuciyarsa tayiba da jin yanda Jawaad yay magana da tsawa da sanyin murya kuma a ƙarshe. Jabeer yace “Yi haƙuri, yanzu kana Office ne?”. “Gani nan zuwa” kawai ya iya cemasa ya yanke wayar. Reverse yay tare ya figi motar da shegen gudu ya koma station.
A office ɗinsa ya iske Jabeer na jiransa, har wani jiri-jiri yakeji saboda tashin hankali, sai da ya zauna sannan Jabeer yace, “Mike faruwa da gimban?”.
“Jabeer nima ban saniba, ranar juma'a ya tafi weekend amma bai dawoba, shinefa nasa a bisa aga ko yana lafiya, amma sai aka tararma baijeba”.
Cikin ɗaurewar kai Jabeer yace, “Ya salam to ina yaje shiko? Yanzu abinda zamuyi bara mu bibiyi layin sa, ina fata kunyi waya dashi bayan tafiyar tasa?”. Kai kawai Jawaad ya girgizama Jabeer, yana faɗin, “Na kirashi jiya amma bai ɗagaba”. Jabeer yace, “Tunda dai kiran ya shiga zai taimaka mana”. Wayar kawai Jay ya miƙama Jabeer baice komaiba. Gaba ɗaya Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai faman zagaye office ɗin yakeyi, Jabeer kuma nata ƙoƙarin ganin ya samo inda gimban yake, a haka Aliyu da Hafiz suka shigo suka samesa harma da Rose da dawowarta kenan daga tafiya. Haka suka duƙufa su huɗu suna taimakawa Jabeer. Inda alama ke nuna musu wayar gimba na nan ɗinne ya tada musu hankali har suka kasa aminta suketa sake ninƙayar bincike. Cikin girgiza kai Jabeer yace, “Kai abinnan akwai rikitarwa, mizai kaisa wannan dajin mai haɗari? Inaga bara nai magana da kamfanin layinan dan muna buƙatar bayanan da yafi haka”. Hafiz yace, “Hakan shine zai taimaka mana Jabeer, danni kainama ya kulle gaba ɗaya”.
Jawaad dai yama kasa cewa komai, zaune yake kawai tamkar butunbutumi. Aliyu ne yay kiran wanda yake musu aiki a kamfanin layin da gimba ke aiki dashi, bayan sunyi magana ya ajiye wayar Jabeer ya tura musu Number gimba.
Ganin magriba tayi Aliyu yace, “;
Boss ka kwantar da hankalinka, ni ina ganin ko wasune suka Kidnapping ɗinsa bazasu kaisa wannan jajejinba, kawai sunyi hakane domin rikita mana tunani, idan muka kwantar da hankalinmu zamu fahimci komai cikin sauƙi, yanzu dai Ma'aruff ɗin yace daganan zuwa safiya zai turo mana komai, inaga muje muyi salla da addu'ar ALLAH ya kuɓutar dashi a duk inda yake, a kuma hannun duk wanda yake”.
A tare suka amsa da amin har Jawaad.
Koda suka fito daga salla Jawaad ya tafi gidane kawai cike da matsananciyar damuwa, bai shiga gidaba sai da yay sallar isha'i.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...