*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*
*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*
*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*
*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*
*ALBISHIRINKU KANAWA*
*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*
_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_
*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*
*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*
*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*
08033990209
*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽👌🏽
Page 52
................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima, suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?. Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu.
Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa.... Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone, inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin..★★★★★★
Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke, sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa.
Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi.
Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi, ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje, umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai.
Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka sanar musu.
Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa saƙon godiya da fatan alkairi.

KAMU SEDANG MEMBACA
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AksiTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...