Page 61
...............Cike da mamaki matuƙa Aamilah ke kallon Shahudah dake zaune gaban mirror'n ɗakin Mama Atika tana tsara kwalliya, taci jan wando da farar top ƙal mai ƙyau da akaima hoton zuciya a gaba, gefe kuma madaidaiciyar jikka ce mai azabar ƙyau da aka ƙawata da zanen furrani na zuciya.....
“Sister! Wai mi kikeyi hakane?”.
Ɗago manyan idanunta tai da sukasha kwalli ta kalli Aamilah, sake maida fuskarta tai ga mirror tana dai-daita janbakinta da yay mata ɗas a baki. “Harma tambayata kike Aamilah? Kin manta yau Valentine day?. A duk irin wannan ranar kema shaidace ai ina shiryama BB wani abu, sannan muɗan fita yawo koda dakene idan shi yace bai zuwa. Tunda matsalolin nan suka fara kema kinsan hakan bata kasanceba, to amma yanda aka maida auren nan namu ai wannan ranar ni tazomin a dai-dai, koba komai zan sake tabbatar masa yana nan daram a raina, a shirye nake kuma nai waje da waccan jakar baƙauya daga garesa da baƙin asirinta”. Cike da takaici ƙarara a saman fuskar Aamilah ta girgiza kai ƙwalla na cika mata idanu, “Sister yanzu nan duk tashin hankalin da muke a ciki keta soyayya ma kikeyi? Wlhy bantaɓa sanin akwai kunyaba a duniya irin jiya, hatta da ƴan gidannan kunyar haɗa ido nake da wasu dalilin halin da su Dad suka jefa kansu da mu, amma ke tun a daren jiya nagama kin ware kamar komai bai faru ba, ga Mom can kwance yanzu haka zazzaɓi ne ma a jikinta, wlhy badan su Uncle Sulaiman sun matsa fitar nanba nasan babu inda zataje. Duk shirmen Salman jikinsa a sanyaye yake tun jiya ya kasa fita ko ina yana tare da Mom, amma ke........”
Shahudah da kema Aamilah wani banzan kallo tunda ta fara maganar taja gajeren tsaki tana ɗaukar sosan hoda da ƙara gyara fuskarta. “Aamilah kenan, harma kece kike da bakin faɗamin ban damu ba? A kaf ɗinku nafi kowa shan kunya a al'amarinnan, dannice kullum mai posting pictures ɗin Dad a kowanne shafina, kinsan kuma yanda nake da ɗunbin fans. sannan a dukanin shafukansa hotunana yafi na kowa yawa a cikinku, wlhy tsabar baƙinciki gaba ɗaya shafukana na rufesu, ke a jiya saida na karya duka layikan na fasa wayar sannan na samu nutsuwa. Bayan wannan mikikeso nayi? Na rasa Dad, nakuma rasa BB a karo na biyu? Impossible dear, dolene na tsira da ɗaya, domin ina ƙaunar mijina. Nasan duk bayanin dazan miki ba fahinta zakiyiba tunda ba auren kikayi ba, dan haka karki bari a jimu a gidan mutane”.
Baki a matuƙar hangame Aamilah da Mama Atika dake a kwance tana duk saurarensu suke kallon Shahudah data jefa Cingam a baki tana ƙara gyara zaman gashin dokin dake a kanta da siririn mayafin data yafa. Juyawa tai tana kallonsu kanta tsaye, “Kumuje. dan nifa namafi son mu fara isa dan naga Maman BB sosai naga kuma kalar tarbar da zatamin. Sannan naɗan faracin uban yarinyarcan kafin zuwa dare na tare”.
Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, Aamilah ta taimakama mama Atika ta tashi zaune dan dama tuni ta shirya, badan tasoba zata bisu, sai dai kawai waɗanda suka bada shawarar zuwa gidan Alhaji babba a yau sunfi su da basa son zuwa rinjaye, batason kuma tace bazataje ba a fassara al'amarin da wani abu daban, ko aga kamar tana baƙin ciki da dawowar Bilkisu ne.
Sun iske mafi yawan jama'ar gidan suma duk sun fito harabar gidan, fitowarsu ta saka kowa ya zubama Shahudah idanu, dan taci wani uban dogon takalmine bayan ɗamewa datai cikin wando da riga. Uncle Sulaiman ya kalleta cikin ɓacin rai zaiyi magana Uncle Sadiq yay saurin riƙe masa hannu yana girgiza masa kai alamar karya ce mata komai, dan yasan yin maganar kan iya janyo wata fitina daban musamman ga mama Atika da tun jiya taketa datsama mutane magana a gidan tamkar ba uwace a garesu ba.
Haɗiye maganarsa Uncle Sulaiman yayi, badan yaso hakanba. A sauranma babu wanda yay yunƙurin cewa komai, sai dai sunata kallon Shahudah data toshe da baƙin eyeglasess ga cingam a baki tanata tauna hankalinta a kwance.__________________
ZAFAFA 2021
_______________Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...