62

11.7K 996 109
                                        

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 62

....................Wani irin tsuma jikin Jay ya keyi irin wanda kowama bai taɓa ganiba, idanunsa sunyi masifar rinewa abun tsoro, duk wata gaɓa ta jikinsa ta sake buɗewa, ƙwanjinsa ya kumbura hakama jijiyoyin kansa dana dukkan sassan jikin nasa. Da sauri Alhaji babba daya fahimci komai zai iya faruwa a wajen dan yasan wanene jikansa da zafin zuciyarsa. yay azamar riƙo Jay ya rungume a jikinsa, duk da neman ƙwacewa da ya keyi bai sakesaba. sai ma taimaka ma Alhaji babba da Uncle Sulaiman yay suka danne Jawaad ɗin yanda bazai iya tashiba duk yanda yaso hakan. Kuka kawai ya fashe dashi dan zuciyarsa tai masifar kaiwa maƙura, Alhaji babba ma kuka ya keyi. ya kalli su Dad yana faɗin, “Amma Ali ka cuceni, yanzu kunsan da wannan zaluncin da kuka aikata amma harka iya zuwa neman auren Rahmah a wajena?”.
        Cike da tashin hankali da tsoron Jawaad dake a cikin idanunsu ƙarara Dad yace, “Munyi hakane domin rufe sirrinmu, dan bayan mun gama aikata abinda bokanyarmu tace ga Abdul-aziz sai kawai mukaci karo da Rahama da Bilkisu a bazata duk suna kallonmu ashe, duk da munsan asirin dake tattare damu bazai bari su iya komaiba a kanmu hakan bai hana  hankalinmu mummunan tashi ba, a take muka aika ɗan aike wajen bokanya, mukuma mukabi ayarin masu kukan mutuwa da jimami. Kafin a gama kammala haɗa gawar Abdul-aziz muka sake samun ɗan saƙo daga bokanya akan bilkisu da Rahmah. andai rufe bakin Rahmah kamar yanda bokanya ta faɗa har abada bazata sake tuna abindama ta ganiba balle wani ma yaji daga gareta, Bilkisu kuwa babu yanda za'ai bakinta ya rufu sai dai ta haukace, hakan kuma bazai tabbata ba sai idan data farka za'a bata ruwan tsafin da bokanya ta aiko dashi. Musan mu bazai yuwu muyi hakaba, dan haka Nasir ya kawo dabarar zuwa ga Humaira (Mom) da Mama (Mama Atika) dan ya sakasu suyi mana wannan aikin ta hanyar daya dace tunda suma akwai nasu burin akan dukiyar Abdul-aziz........”
      Kuka mama atika da Mom suka fashe dashi. mama Atika tace, “Wlhy ALLAH ne shaidarmu baku sanar mana akan hakan zakuyima Bilkisu asiri ba, Nasir ya samemu lokacin da aketa shirin fita da gawar Abdul-aziz, mukuma isowarmu kenanma babu jimawa. Yace muyi ƙoƙarin bama bilkisu ruwan maganin, ta hakane kawai zamu sami damar mallake duka dukiyar da Abdul-aziz ya tar.......” sai kuma ta kasa ƙarasawa ta fashe da matsanancin kuka. Uncle Nasir ya kalleta shima yana kukan,
         “Ki ƙarasa mana mama, ai duk kece silar komai, kece kike mana huɗuba akan karmu yarda kowa ya fimu a ƴaƴan baba, kece kika saka ƙiyayyar Abdul-aziz a ranmu, a cewarki an auro uwarsa a bayan baya amma ɗanta yazo yafi kowa arziƙi a gidan harda ƴaƴanki, bayan kuma mune ya dace muyi wannan arziƙin saboda kece matar baba ta farko, mukuma mune ƴaƴan farko a gidan. A dalilin wannan huɗubar taki na jefa kaina a halaka, tun bana ɗaukar huɗubar Alhaji Ali da Alhaji Sadi har suka fara tasiri a raina, nidai burina kullum na wuce Abdul-aziz arziƙi dan na faranta miki rai. hakan yasa duk muguntar dasu Alhaji Sadi suka kawo shawarar a aikatama Abdul-aziz na dinga biye musu, har takai sunyi ƙokarin jawo Abdul-aziz cikin tafiyarmu, dan har wajen bokanya an kaisa da yaudarar zata bashi maganin sammune saboda magautan siyasa. Ko'a hakanma saida ya tirje, nine naita lallaɓarsa harya amince ya bimu, koda yaje yaga abinda muke nufin ɗorasa a take ya bijire mana ya kuma nuna ɓacin ransa mai tsanani akan hakan. Sai dai zukatanmu sun rigada sun bushe a lokacin. gani muke kamar zai tona mana asirine. dan haka muka gaza ƙyale rayuwarsa ta huta, duk wani burinsa na aikata alkairi ga talakawansa mun daƙilesa ta hanyar asiri da muzgunama rayuwarsa, kowane aiki munyi bake-bake a kansa tare da handame dukiyar da aka keɓe danyin ayyukan, daga ƙarshema bokanya ta bamu tabbacin jinin Abdul-aziz zai taimaki tafiyarmu, dan haka muyi amfani dashi, kafin hakan kuma dolene muyi fasiƙanci dashi. Jinin Abdul-aziz shine jini na farko da muka fara salwantarwa, dan da duk abinda zamuyi na tsafi da jinin dabbobi mukeyi. Amma nasarar da muka samu da jinin Abdul-aziz yasa burikanmu sake faɗaɗa, muka fara sadaukar da makusantanmu. Mama da humaira sune suka ɗurama Bilkisu maganin da bokanya ta bamu bisa taimakon Uwaisu, mukuma lokacin mun tafi bizne gawar Abdul-aziz.
          Sanda muka dawo mun iske bilkisu cikin hauka tuburan, hakan ba ƙaramin daɗi yay manaba kuwa, dan asirinmu kam dai munsan ya rufu kenan. Ni na bada babbar ƴata kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana, na kuma bada na Mama (Mama Atika) sai dai bokanya tace ba'a lokacin take buƙatar Mama ba, dan tana hango zatai mana amfani sosai a tafiyarmu, haka na musanya jinin Mama dana Mama Suwaiba da Mama Maryam, na kuma haɗa da matata ta farko. Shima Alhaji Ali aka buƙaci ya kawo, shi a take ya bada na Mamansa da ƙanwarsa, da ɗansa na biyu, sai dai kuma nace bai isa ya bada na ƴar uwataba (Mom), wannan dalilin yasa ƙungiya tai masa lamuni akace ya bada na wata matar idan yanada ita, kokuma ya ƙara aure, sai kuma jinin ƴarsa babba mace shima. Hankalinsa ya tashi dan yana tsananin son Shahudah, a lokacinma batafi shekara huɗu da wata bakwai da haihuwaba, yayta roƙo da neman alfarma akan zai canja da wani. Da farko Bokanya bata amince ba, sai bayan kusan kwana biyu dayin hakan ta bashi umarni akan ya auri Rahmah, hakan shine kawai zai kawo sake rufuwar asirinmu, sannan idan Shahudah ta girma yay ƙoƙarin haɗata aure da Jawaad, nanma zamuci moriyar hakan, indai ya aikata haka ƴarsa zata tsira da matarsa, idan Rahmah da ta haihu sai ya bada duk abinda ta haifa madadin Shahudah. Da wannan shawara da umarni yay amfani, na shige masa gaba ya samu auren Rahma ta wajen mahaifinta, dan lokacin Mama Maryam ta rasu. Tabbas badan baƙin asirin da mukaima Rahma ba bazata taba yarda ta auri Ali ba, duk da kuwa abinda ya faru kusan shekara bakwai a lokacin, amma  bata da wani zaɓi, dan ta ko'ina mun gama ƙulleta.
     Kafin auren Rahma da Ali ya tattara su Humaira ya bar ƙasar dasu, wannan duk yana cikin dabarun karta tada hankalintane akan za'ai mata kishiya, shi kuma Ali yana matuƙar sonta bayason tashin hankalinta. Sai da ya maidasu da kusan wata biyar sannan akai bikin, lokacin Bilkisu ta gudu daga gida saboda asirin da muka kuma tafka mata aka kai gidan Alhaji Kokino, burinmu haukanta ya nisan tata da gida har abada koda ƙasar waje ne ma taje. Badan Ali nason Rahma ya aura ba. bayan bikinsa da Rahmah itama ya ɗauketa daga ƙasar ya maidata Ghana da zama duk a cikin shirinmu, sai dai kuma acan ɗin saita gamu da wata ƙawa data tsaya tsayin daka wajen taimakonta da addu'oi ganin kamar batama cikin hayyacinta a rayuwar aurenta da Ali. ba komai yaja hakanba sai ganin yanda Ali ke gallaza mata, bata taɓa yunƙurin barinsa ba ko faɗama ƴan uwanta, sai dai tai kukanta ta share hawaye. gashi tana zuwa ta samu ciki kuma. Ganin matarnan zata buɗe mana aiki ya sake ɗakkota ya maido ta nan ƙasar, inda mukai zaman dakon haihuwarta....” Kuka ya sarƙe Uncle Nasir ya kasa cigaba, sai Dad da shima ke kukanne ya cigaba da faɗin,

ƘWAI cikin ƘAYA!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora