Page 22
...............“Bazai yuwuba, Ka gaggauta fita!! Ka gaggauta fita!!!” na jiyo wata murya mai amo sama-sama tana amsa kuwwa a cikin ɗakin lokacin da numfashin ke gab da barin gangar jikina. Daga haka ban sake fahimtar komaiba dake a cikin duniya sai wayar gari nai na ganni kwance a ɗakin Momy.
A hankali na shiga buɗe idanuna da sukaimin nauyi, na shiga bin ɗakin da kallo daki-daki, dan bamma fahimci inda nakeba da farko saboda zan iya irga shigowata ɗakin Momy a tsawon zama gidan, da ƙyar na tashi zaune ina sake mamakin abinda ya kawo ni nan ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Momy ɗakin.
“Yauwa kin tashi Bilkisu?”. Kaina na ɗaga mata a hankali, saboda jikina yaymin wani masifar nauyo, na buɗe baki da ƙyar nace, “Momy miya faru na ganni anan?”. Hankalinta nakan ciro abu a cikin drawer ta bani amsa, “Za'a gaya miki daga baya, tashi kije ɗakinki kiyi wanka”. Da “to” kawai na amsa mata na sauka jikina duk yana wani masifar ciwo, ga tunani fal raina, wani abin mamakinma na sake tararwa a folon ƙasa, dan kuwa cike yake da dangin Momy, na gaisar da waɗanda zasu iya jina na wuce ɗaki kaina na kuma ɗaurewa. Akan gadona dake mugun yamutse na fara sauke ido, ‘Kowaye yay masa haka kuma?’ na ayyana a cikin raina, dukda banajin daɗin jikin sai nai tunani bara na fara share ɗakin, gadon na shiga kakkaɓewa, ƙarar faɗuwar abu naji kamar ƙwandala a ƙasa lokacin dana ɗaga zanin gadon, dube-dube na fara, sai dai banga komaiba, sharewa nai kawai na gyarashi tsaf, nakoma shara. A wajen shararne na sharo abinda ya faɗi ɗazun ashe wajen gado ya shige, Wuri ne kalar ja, sai dai wannan yafi wurin dana sani girma, haka kawai na samu kaina daƙin maidashi a sharar, saima na jefashi cikin jikkar islamiyya ta dake kusa dani, na cigaba da sharata. Da ƙyar na kammala aikin na lallaɓa bayi nai wanka, ganin baƙona ya tafi saina haɗa da wankan tsarki. Ina shiri ina mamakin barcin danai daga daren jiya zuwa safiyar yau ace bamma farkaba kamar yanda na saba a lokacin sallar asubahi dukda bana salla, yanzu hakafa sha biyu ma, ni saima yanzu maganar zuwa aiki tazomin a rai, gaba ɗaya wani iri nakejin kaina tamkar birkitacciya, wayata na shiga dubawa, sai dai kuma ban gantaba, ƙarasa shirin nai da tunanin naje ɗakin Momy na duba ko tana can idan na gama. Sallamar Momyn ce ta kacemin tunani na juya ina kallonta. taci kwalliya cikin rantsatstsen lase ɗan ubansu sai walƙiya yake, ga gwalagwalai ta zuba a wuya da hannu, taimin murmushi irin wanda tsahon zamana da ita ban taɓa cin karo da shiba sai yau, “Bilkisu irin wannan kallo haka” kunya naɗanji, dan haka na murmusa ina mai duƙar da kaina, nace, “Kinyi ƙyaune Momy”. “To nagode sosai” tafaɗa tana zama a bakin gadona da ajiye ledan data shigo dashi a hannu. takai dubanta gareni, “Kinga cire waɗannan kayan waɗanan zaki saka, nasan akwai tambayoyi fal ranki, karki damu zamu baki dukkan amsoshinsu zuwa dare idan baƙi sun tafi, fatanmu dai kizama maiyin biyayya a garemu kamar yanda kika saba, batun zuwa aiki kuma yau bazaki jeba”. Shiru nai kawai ina kallonta, sai kuma nace mata, “To momy, wayata fa?”. Miƙamin tayi tana faɗin “kin ganta nan, dama anata kirankima kuwa tun ɗazun”. Amsa nayi, itakuma ta miƙe ta fita. Da kallo na bita kaina na sake ɗaurewa da abubuwan da ban saba ganinsuba sai a mafarki, ganin ta ɓacema ganina saina sauke nannauyar ajiyar zuciya, wayar na duba, miss calls kam da yawa harma bansan dawa zan faraba, Yah Qaseem, Ummie, Amina, harma da Numbers ɗin da bansan na wanene ba, kafin nayi wani yunƙuri kira ya shigo, sunan Masarauta danai saving ne ya fito ɓaro-ɓaro a jiki, ɗagawa nai muka gaisa a mutunce kamar ranar, daga ƙarshe take sanarmin bayan an sakko massalaci zasuzo kawomin cards ɗina, murmushi nayi ina mata godiya, kafin mu yanke wayar. tunanin yaya zanyi na shigayi, dan yakamata ace koba komai nai musu tarba ta girmamawa ko badan gidan da suka fitoba, to amma yanda gidannan ke cike ta ina zanma fara nikam? Wlhy gaba ɗaya yau kaina ya ɗauki zafi, sam tunanina baya tafiya dai-dai dana sauran mutane. Kasa yin komai daya dace nayi, nai zaune a inda Momy ta barni, niban canja kayan datace ba, bankuma miƙe na nemawa baƙin abinda zasuciba idan sunzo balle kuma cikina dake Masifaffen ƙugin yunwa kamar zanci babu. Ina a wajen har ƙarfe ɗaya ta buga, tashi nai jiki a sanyaye na ɗauro alwala, gabana sai wata iriyar muguwar faɗuwa yake wadda ban taɓa jiba, idan girata ta haggu ta harba sai ta dama ma ta harba, sai kuma inji wata faɗuwar gaba ta biyo bayansu. Haka nai sallar azuhur batare dana fahimci abinda nama karanta a sallarba, dan wasu irin mugayen halittu na rinƙa gani suna zuwa gabana, haka dai na dake raina na cigaba da sallar inata faman kwarar da zufa tamkar wadda take a cikin ruwan zafi, a sujidar ƙarshema sai naji wata iriyar muguwar dariya a ɗakin tamkar za'a fasashi, sai kuma aka fashe da kuka, zuwa can aka kuma saka dariyar datafi ta farko. Na kasa ɗagowa daga sujidar ma gaba ɗaya tsahon lokaci, saida naji an taɓani ne a baya da magana kamar muryar Ummie sannan ALLAH ya bani ikon ɗagowa. Shiru naji ɗakin ya ɗauka sannan bana ganin komai a gabana harna kammala na shafa addu'a. Na sauke idanuna akan Ummie dake zaune da a bakin gadona tana latsa waya, sai dai na kasa cemata komai saboda wani irin yanayi da nakejin kaina mai masifar tashin hankali, jina nake tamkar ana kunnamin garwashin wuta a jiki........
“Bily! Bilyy!!” na tsinkayi muryar Ummie na faɗa tana girgizani. Kallonta nai na amsa da ƙyar, dan bansanma tazo kainaba, bana gane komai a yanzu bana kuma fahimtar komai hatta da kaina neman suɓucemin ya keyi. Tace, “Na shiga uku, Bilkisu lafiya kike kuwa? Wai mike faruwane haka?”. “Ban saniba nima Ummie” nai maganar hawaye na ziraromin akan kumatu. Kafin ta samu damar jehomin wata tambayar muka jiyo matsananciyar hayaniya ta kaure illahirin gidan tamkar ana faɗa. Mu duka kallon ƙofa mukai, hakan yay dai-dai da bugo ƙofar da aunty Shahudah tai hannunta ɗauke da wuƙa tana kuka.
A tare muka miƙe da Ummie, dan lokaci ɗaya wani ƙarfi yazomin da bansan daga inaba kuma, ganin kaina tayo da wuƙar saina zaro idanu waje ina faɗin, “Au...aunt...aunty Shahudah lafiya? kuw....” bankai ga ƙarasawaba ta kawomin suka tana faɗin, “Wlhy kasheki zanyi, tsinanniya jinin asara jinin masifa, jinin tsafi....” wani mugun tsalle nai na kauce mata, amma dukda haka saida taɗan yankeni a damtsen hannuna. Ɗakin ya cika sai ƙoƙarin janyeta ake tana ihu da tabbacin yaufa ita saita halakani.
Bansan hawaba bansan saukaba kawai naji aunty Aamilah da wasu ƴammata sun rufeni da duka sukuma, tun ina ƙoƙarin kare kaina harna gaza dan sunfini yawa, gashi kuma bayan Ummie babu mai yunƙurin karɓata.
ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...