FART ONE END
Shafi na arba'in😌
.............Ina ƙoƙarin shiga gida kiransa ya sake shigo mani, ɗagawa nai da nufin faɗa masa ganinan zuwa gidan, amma sai naji yana magana mai alamar ba'a gidan yakeba..
Ya bani umarnine akan na duba ɗakinsa akwai wasu takardu ɗaya daga cikin jami'inmu zaizo ya amsa, na amsa masa da to kafin na yanke wayar na ida shiga da hanzari.
Kamar yanda ya umarta hakan nayi, ina fitowa na iske wanda aka turo ɗin yazo, shima yana sama dani, dan haka nai masa gaisuwar girmamawa kafin bashi takardun na koma ciki.
Duk da na iske su Mummy a falo ban iya zama ba, gashesu kawai nayi na shige ɗaki abuna, dan ina buƙatar samun filin yin tunani akan abinda muka tattauna da Amina.
Sosai komai yake neman ɗaure kaina, duk da kuwa Alhmdllh yanzu na samu ilimi sosai game da bincike, dan ko a wajen horaswa da muka samu, nafi maida hankalina anan sosai, alamu sun nuna Qaseem da Salman basa gida, shin akwai wanda ya dawo daga baya kenan s cikinsu? Ko kuwa kuku zan zarga kai tsaye ne? Baba mai gadi tsoho ne, duk da dai tsufansa bai kai ace bazai iya aikata makamancin hakanba, to amma miyasa zan zargesa ne? Lallai ya dace nama fara bincikarsa akan shiga da fitar kowa a wannan ranar.
Da wannan tunanin naɗan samu nutsuwa, amma koda nai shirin barci na kwanta sai ya gagara, babu abinda nake sai saƙawa da kwancewa tare da tunanin iyayena._______________________________
Washe gari litinin muka tashi da shirin aiki, tunda na gama shiri naga harna shiga kicin ina shan tea Yah Qaseem bai shigoba nasan bai kwana gidaba jiya kenan?.
Tea ɗin kawai na iya sha na fito, babu wanda ya tashi har yanzu a mutanen gidan.
Nai addu'a na fita tamkar yanda na saba. Yau kam sai driver nabi, muna isa tamkar jira na samu saƙon kira.
Na nufi inda ake kiran namune na haɗu da Yah Qaseem, murmushi mukaima juna, na gaishesa cikin girmamawa tamkar yanda na saba.
Shima ya amsamin da kulawa yana tambayata yaya gidan?.
“Alhmdllh Yah Qaseem, yaya aikin naka? Ai ni bansan baka kwana gidaba sai yanzu da safennan?”.
Yace, “Oh, wannan wace irin matace dani? Ban kwana a gidaba amma sam bama ta saniba”.
Haka kawai sai maganarsa ta sakani jin kunya, naja baby hijjab ɗina na rufe muskata ina murmushi, matsowa yay kusa dani gab tamkar zai shige mini jiki, ya kai bakinsa dai-dai saitin kunnene yana faɗin, “Baƙauya”.
Baya na ɗan ja saboda kusancin da muka samu yayi yawa, na janye hijjabin zan bashi amsa karaf idona akan mutumin ga, gabana yay wata masifaffiyar faɗuwa saboda cin karo da wata shegiyar harara daya watsomin, tuni fara'ar fuskata ta ɗauke baki ɗaya saboda bugun da ƙirjina yakeyi.
“K lafiya?”
Ƴah Qaseem ya faɗa cikin tsareni da idanu.
Cikin rawar baki da hadiye yawu da ƙyar nace, “B..babu k..omai”.
Idanunsa ya ɗauke da ga kaina ya maida saitin inda nake kallo, sai dai yana juyawa shi kuma yana shigewa Office.
Sake juyowa yay gareni, “Wai haushi kikaji dan nace miki baƙauya?”.
Murmushin ƙarfin hali nai masa ina girgiza kai, nace, “A'a yayana”.
Ƙaramar dariya yayi ya dungure min kai tare da zagayeni ya wuce abinsa da faɗin, yaje gida sai ya dawo.
Ko a dawo lafiyar ban iya ce masaba, na kuma kasa ɗaga koda ƙafata a wajen saboda tsabar yanayin dana tsinci kaina.
“Haba Bilkisu! Ke kin cika matsala wlhy, tsayuwarmi kuma kike anan?”.
Nannauyan numfashi na sauke jin muryar Ummie a kusa dani, taja hannuna ba tare da ta sake magana ba zuwa inda ake jiranmu.Sosai mamaki ya kamani ganin inda ta kawo mu, zan iya kiransa Office kai tsaye, amma mazauna cikinsa da zasuyi amfani da shi aƙalla mutane goma cif.
Tunda naji zuciyata ta dai-daita nasan baya wajen, dan haka nakai dubana ga kowa, iya dai mune da aka tara ranar, tare da yallaɓai Hafiz.
Ya gyara tsaiwarsa yana mana bayani yanda zamu fahimta sosai.
“Wannan Office ne da zai kasance na musamman ga waɗanda boss ya aminta da ƙwazonsu, dan haka sai kowa ya duba, idan kaga sunanka to kana cikin waɗanda ya zaɓa, idan baka ganiba to ba hakan yana nufin bazai iya aiki da kai bane ko bai yabama ƙoƙarin kaba, kawai dai kasan a ranka hakanne mafi alkairi a gareka”.
Duk cikin girmamawa muka amsa masa.
Ni kasama dubawar nayi, sai Ummie ce tabi sauran itama tana dubawa, inajin wasunsu suna murna, alamar dai sunga sunayensu.
Nima a bazata naji Ummie ta rungumeni tana faɗamin ni da ita duk muna ciki.
Ban san miya saba, banji baƙin cikiba, kuma banji wani murnaba, kawai dai nayi murmushi ne dan karta zargi wani abu..
A cikin mu goma ɗinan bakwai mazane, mu uku mata, ni Ummie sai ɗayar mai suna Divine.
Komai na wajen an yisane da tsari, dan an saka mana shingai da kowa bazaiga abinda ɗan uwansa keyi a sashensaba sai idan yaso hakan.
Naji daɗin yanda aka saka Ummie kusa dani, duk da ba'a layi ɗaya mukeba wajen zamanta yana kallon nawa, sannan mune ƙarshen bangon wajen.
Duk wanda yake cikin wannan tafiya yayi farinciki, saɓanin ni da bansan manufar zaɓin da zuciyata ta ɗauka ba.
Shigowar Yah Qaseem station ɗin ya samu labari, bansan dalilinsaba naga ya fara faɗa tamkar zai cinyeni ɗanya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba.
Tun ina saurarensa da mamaki na koma al'ajab, daga al'ajabi nakoma ban haushi, har takai abin ya bani tsoro, danni bansan minene laifina a cikiba? Kuma ince nan wajen aikine, bamu da dalilin cewar sai inda muke buƙata za'a zaɓamana.
A cikin masifarsa ta yau ne nakeji cikakken suna mutumin nan, wato *_Jawaad Abdul-aziz yusif_*.
Ni dai bance ƙalaba har yaci jarabarsa ya tsire, daga ƙarshe yace na fitar masa a office.
Na fito ina share hawayen da suka ziraromin babu shiri, sai shi kuma naci karo da shi.
Tafiya yake a fusace tamkar wani ingarman doki, yana ƙoƙarin saka bindiga a aljihun wandonsa na baya, yayinda su yallaɓai Jabeer ke take masa baya suma fuskarsu babu walwala.
Yana ƙoƙarin shiga motar da aka buɗe masa ne ya ɗago, sai ko idanunmu cikin na juna.
Saurin janye nawa nayi ina kauda kai, a ƙasan zuciyata ina mamakin miya fusatashi har hakane?.
Bani da mai bani amsa, dan haka sai ma tashin motarsu na jiyo.
CITEȘTI
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcţiuneTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...