Shafi na ashirin da biyar
Kuyi manage tau babu editing🤥😒
.............Wanka ya samu yayi da ruwan ɗumi danya rage nauyin jikin, sannan yay alwala ya fito, jallabiya kawai ya saka ya fito zuwa massallacin gidan dake a ƙofar kiga.
Ana idar da salla ya fice abinsa, dama yau a makare yazo, dan haka yay sallar a ƙofa-ƙofa, bai yarda tsayawa gaisuwa da kowa ba har kawunansa, ya gudo gida ya kwanta.
Duk yanda tunanin yaso masa tasiri barcin da ya keji sai yaci ƙarfinsa, kafin kace mi ya fara sauke numfashi a hankali alamar dai yayi nisa cikin barcin.A makare ya tashi zuwa office, dan haka yayta komai cikin hanzari harya samu ya kimtsa, yayi ƙyau sosai, ya fito yanata baza ƙamshi kamar ko yaushe.
Gimba da tun ɗazun yake gewayensa da tunanin ko lafiya?, yay saurin miƙewa daga wajensu mai gadi ya nufosa.
Sam babu walwala a fuskarsa, ɗaure take tamau babu sauƙi, kusan biyar daga matasan ƴammatan gidan da suka fito zasu wuce makaranta suka shiga gaishesa kowacce zuciyarta a narke da ƙaunarsa.
Hannu kawai ya ɗaga musu dan baijin zaima iya motsa bakin balle aje ga magana, da sauri Gimba ya buɗe masa motar saboda yau dai yasan babu wargi a wajen boss.
Shima sai da ya zagaya mazaunin direba sannan ya fara gaishesa.
Shiru Jawaad ɗin bai amsaba, Gimba ya kallesa ta mirror, yanda ya gansa kwance a jikin kujera idanu a lumshe ya tabbatar masa lallai akwai matsala.
Bai sake cewa komaiba ya tada motar suka fice daga gidan.
Sai lokacinne Jawaad ya amsa masa gaisuwar, tare da faɗa masa inda zasuje kafin Office.
Jin asibiti ya saka gimba tunanin ko baida lafiya ne?.
A ƙofar gida sukaci karo da motar yaran da aka bama Jawaad ɗin yanzu a Office saboda tsaro su huɗu, gilas ɗin motar kawai Gimba ya sauke suka matso suna gaisheda Jawaad ɗin cikin girmamawa.
Idanunsa ya buɗe yana ɗaga musu hannu, bayani ɗaya yay masa akan Sir Ahmad yace yau zasu fara gudanar da aikinsu, daga yanzu duk inda zai saka ƙafa dolene sai da su.
Numfashi kawai ya basu, yay musu nuni su shiga mota kawai.
Umarninsa sukabi, su ka rabu biyu kowacce mota mutum uku, ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta Jawaad tana a tsakkiya.
Shi sam baya buƙatar wasu securitys tare dashi, amma Sir Ahmad ya matsa sosai akan yabar barin Jawaad ɗin na yawo haka tun randa abin nan ya faru tsakaninsa da Qaseem.
Shigarsu asibitin suka samu waje sukai fakin, kasa daurewa Gimba yay ya juyo a ɗarare yace, “Boss ko baka da lafiya ne?”.
Idanu Jawaad ya buɗe a hankali kan gimba, sai kuma yay masa guntun murmushi yana girgiza kai alamar (a'a).
Duk da Gimba bai gamsu ba haka ya fito, Security ɗaya kuma ya buɗema Jawaad ɗin motar, yaja kusan seconds ashirin sannan ya zuro ƙafarsa ƙasa ya fito.
Baƙin eyeglasess ɗinsa ya ɗora saman ido alamar dai babu sassauci kenan, yana tafe suna take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.
Ganinsu kawai ya isa ya baka tsoro, gasu duk sunsha baƙaƙen suits da eyeglasses, fuskoki kam ba'a cewa komai saboda ɗaurewa.
Sun samu girmamawar mutane musamman ma'aikatan asibitin, duk da fuskarsa ɓoyayyar fuskace da ba kowa yasan matsayinta ba, amma yanayinsa da kwarijininsa sun saka mutane ganin girmansa a idanunsu, sannan yanayinsa ya tabbatar da ba ƙaramin mutum bane koda a hasashe saboda mazajen dake rufe da bayansa harda masu binduga a hannu su uku.
Sai ƙalilan da ba'a rasaba da zasu iya sanin fuskar, musamman tsananin kamar da yake da mahaifinsa.
Tsaye yay dai-dai saitin matar da ke a reception ɗin, duk sai ta rikice, Jawaad ya kalli gimba dake gefensa a ƙasan maƙoshi yace, “Office ɗin Doctor Tayyeb”.
Gimba ya juya ga matar yana maimaita mata.
Kai ta shiga gyaɗa masa baki na rawa tana faɗin, “Ok ok Sir” tai maganar tana ƙoƙarin kiran wayar ogan nata Doctor Tayyeb.
Basu san mi ake cemata daga canba, tanata dai ƙoƙarin masa bayanin dazai fa himta amma da alama cewa yake bazai samu ganinsu ba....
Tsawa ɗaya daga securitys ɗin Jawaad ɗin wani ya daka mata, hakanne ya sakata sakin wayar jikinta na tsuma, Gimba yace ta haɗasu da wanda zai kaisu Office ɗin ko ita ta fito ta rakasu.
Duk fa wannan dambarwar da ake Jawaad na tsayene yana saurarensu hannayensa duka biyu a cikin aljihu, nazarin asibitin da mutanen dake kaikawo a cikinsa kawai yakeyi, duk da ma tun shigowarsu kowa ya nutsu waje guda dan yanayinsu ya nunama kowa dama ba ababen wasa bane balle a gansu a ɗauke kai.
Wata Nurse ce tai musu rakkiya har Office ɗin, tana ƙoƙarin yin knocking Jawaad ya ɗaga mata hannu alamar kar tayi.
Ja baya tai kanta a rissine alamar girmamawa a garesa.
Gimba ya tura ƙofar Jawaad ya shige kansa tsaye, yayinda yaransa suka jeru a ƙofar kamar waɗanda sukazo kama ɓarawo😂.
Takun takalman Jawaad suka saka Doctor Tayyeb saurin matsawa daga jikin budurwar daya ƙwakume a Office ɗin yana lalubewa, itama Nurse ce, sanye takema da Uniform ɗin asibitin.
Wani wawan tsaki Jawaad yaja yana ɗauke kai daga garesu, Budurwar dukta ruɗe sai duƙar da kai take cikin alamun jin kunya da firgici, shi kansa Doctor Tayyeb ɗin a firgice yake, ganin Jawaad a asibitinsa da kuma abinda yaga yanayi da ƴar mutane.
Sai faman sinne kai yake yazo ya zauna a mazauninsa yanama Jawaad ɗin barka da zuwa.
Jawaad da bai tankashiba ya jeho masa tambaya mai rikitarwa,
“Wannan shine abinda kakeyi da ƴaƴan al'umma shiyyasa ka salwantar min da ciki?!!”.
Yanda Jawaad yay maganar a matuƙar kausashe ya saka jikin Doctor Tayyeb ɓari, bakinsa na rawa yace, “Yal...Yallaɓai wl... Wlhy kaji na rantse ban san komai akan maganar nanba, matarka ba zubar da cikinta taib.....”
Da ƙarfi Jawaad ya buga tebir ɗin gaban Doctor, wasu abubuwan suka zube, wasuko tsalle sukai suka canjama kansu muhallin zama.
“Mara mutunci, zaka cigaba damin wasan kwaikwayone kokuwa zaka sanarmin gaskiyar batu kafin na fasa ƙwalwarka da bindiga?!”.
Doctor Tayyeb daya manne da bayan kujera zufa na karyo masa ya share gumin goshinsa, “Yallaɓai please Calm dawn, wlhy bansan komaiba, yanda na musu bayani shine gaskiyar magana, mahaifartace bata da ƙwarin riƙe ciki.....”
Miƙewa Jawaad yayi yana wata ƴar dariya da tafa hannayensa, ya tako zuwa gaban kujerar da Dr Tayyeb yake, a saman tebir ɗin ya zauna suna fuskantar juna, ya ajiye ƴar ƙaramar bindigarsa daya ciro a aljihu ya ajiye gefrnsa.
Wani mugun yawu Dr Tayeeb ya haɗiya idonsa akan bindigar, Jawaad ya katsesa da faɗin, “Wannan itace tambayar ƙarshe dazan maka, ya rage naka ka bani amsa dai-dai kokuma ka sakemin ƙarya. Miyasa kabi ra'ayinta ka zubarmin da ciki?”.
Doctor dake lafe jikin kujera tamkar magen datai karo da kura a daji ya haɗiye wani yawu mai kauri idonsa akan bindigar Jawaad daya ɗauka yake jujjuyata a hannu, tabbas yasan Jawaad zai iya aikata komai, shiko da baida laifi gara ya fidda kansa a cikin wannan bala'in tunkan kwaɓarsa tai ruwa, saboda kuɗin Aamilah bazai halaka kansa ba a wofi.
“Yallaɓai kayi haƙuri ka ajiye bindugar na rantse duk abinda kake buƙata zan sanar maka shi”.
Cikin wani salo da murmushin mugunta Jawaad yasa ɗanyatsa ya tura eyeglasess ɗinsa sosai yana faɗin, “Good boy, ashe kasan dokar”.
“Sosaima kuwa yallaɓai” Dr Tayyeb ya faɗa yana jinjina kai tamkar ƙadangaren jangwala gwaja yaga shinkafar manja🤪.
Ajiye bindigar Jawaad yay yana ranƙwafowa kaɗan hannayensa harɗe a cinyarsa da yake zaune da ita a tebir ɗin, ɗayar kuwa tana ƙasane a jiye, “Ina saurarenka”.
Nanma kai Doctor ya jinjina masa, “Maganar gaskiya yallaɓai lafiyar mahaifarta ƙalau, zubar da cikin akai, sai dai wlhy kaji na rantse maka bani nai mata aikinba, andai kiranine kawai na ceto rayuwarta”.
Sosai zuciyar Jawaad ke tsitstsinkewa, ya zare glasess din idonsa yana zuba ma Doctor wani hargitsatstsen kalo, “Uhmyim, wato zubarwa akai? Amma miyasa ka zaɓi faɗar abinda ba haka yakeba? Haka aikinka ya koya maka?”.
“Wlhy A'a yallaɓai, kuskurene ka gafarceni”.
Sauka Jawaad yay daga saman tebir ɗin yana taku a hankali yana faɗin, “Maybe na iya yin hakan idan na tabbatar babu saka hannunka a ciki”.
“Wlhy da gaske nake babu hannuna, bankuma san komai a kaiba”.
Komawa Jawaad yay ainahin kujerar daya fara zama ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana aza hannunsa ɗaya a tebir ɗin yace, “Doctor Tayyeb ka sanni na sanka tun lokacin daka fara aiki gidan Alhaji Ali, karka kuskura a wannan karon ka tsinci kanka a harƙallata, dan wlhy bazan maka ragiba, na kamaka da ƙaryar farko ta faɗar sakamakon abinda ba haka yakeba, kasa a ranka ba'a min ƙarya a shani a banza, yanzu zan tafi, a koda yaushe kuma zan iya nemanka a office ɗina, zaɓin kane kazo akan lokaci koka ɓatamin lokacin”.
“Insha ALLAH zanzo yallaɓai, kuma bazan sake kuskuren maka ƙaryaba akan duk abinda zaka tuhumeni a kansa”.
“Good” Jawaad ya faɗa yana miƙewa da ƙoƙarin tura bindigarsa ta baya, bai kuma tankama Doctor Tayyeb ba ya fice a office ɗin.
Bai cema su Gimba komaiba yay gaba suka sake rufa masa baya har inda suka ajiye motocinsu, buɗe masa akai yanzunma ya shiga ya zauna sannan suma duk suka shiga suka bar asibitin a sukwane.
Haɗiyar zuciya kawai Jawaad keta faman yi, shi kaɗai yasan mi yakeji da yanda ƙirjinsa ke zaɓalɓalar azabar kunar zuciya, shi Shahudah ta zubarma ciki dukda gargaɗin ta da yay akan karta aikata hakan?.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...