Page 15
To yau page ɗin ƙwai cikin ƙaya na ƙuɗine, duk wanda ya karanta ina roƙonsa dan girman ALLAH ya biya da addu'ar ALLAH ya kawo mana iyakar tashin hankalin dake damun wasu yankuna namu na arewaci, dan ALLAH ina roƙon har ƴaƴanmu ku saka suyi wannan addu'ar a dukkanin sallolinsu biyar na wannan yinin, domin addu'ar yara abuce mai muhimmanci a garemu mubar sakaci da ita, idan baki aureba ki roƙa mana jama'ar gidanku suyi da kanninki, duk da munsan anayi dama, sai dai ina fatan wannan ta zama ta musamman domin ALLAH, dan ALLAH kar'a manta, kar'a manta, kar'a manta.
Ya rabbi ka kawo mana ƙarshen waɗanan tashin hankali, ya ALLAH ka ruɓanya rahamarka da rangwame a garemu, ya Rabbi ka yafe mana kurakuranmu, ya Rabbi kaimana maganin abinda bazamu iyaba harma da wanda zamu iya ɗin, ya rabbi ka taimaki bayinka dake cikin gararin rayuwa da hali na buƙatar agaji, ya rabbi ka kawoma muhallansu zaman lafiya, kasaka kwanciyar hankali a zukatansu suma su sami cigaba da rayuwa a yankunansu kamar kowa, ya rabbi ka kawoma ƙasarmu zaman lafiya baki ɗaya da dukkanin duniyar musulunci, ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa kasa ta zama rahama a garemu duniya da lahira🙏🏻😭.
Idan kasan bazaka biyaba karka karanta, bayin ALLAH na buƙatar tallafin addu'oinmu, dan girman ALLAH karmu wofantar da lamarinsu saboda mu muna barci a gidajenmu da iyalanmu bayan munci mun ƙoshi, ba'a zahiri kawai nakeson ayiba har abaɗi ma ita mukafi buƙata😭.
Masu 6am sunyi winning, wannan shine zaizama lokacin posting ɗinmu kafin na daina fushi da kamfanin masu yellow'n tambari 🙄🙄🙄.
................Daga ni har shi kallonsa mukai. Nidai na sauke idanuna da hannuna a hankali ina haɗiyar yawu da ƙyar. Kamal yace, “Haba malam ya haka?” Jawaad bai tanka masaba, sai wayar daya daddana alamar wani abun yayi a ciki ya miƙa masa. A ƙufule Kamal ya amsa yana faɗin, “Wanan rainin wayone ai, ya zakazo ka shiga abinda bai shafeka ba?”.
Ban jira amsar da boss zai bashiba nabar wajen nidai, saboda wata muguwar harara daya makamin dan ya cire madubin idonsa.
Jawaad ya maida kallonsa ga kamal yace, “Karka damu ka kira Number dana saka maka zaka sameta”. Kamal yay ɗan shiru alamar nazari, sai kuma yay saurin taɓa hannun Jawaad dake shirin barin wajen, Jay ya juyo yana kallonsa, sai dai baice komaiba. “Sorry, dan ALLAH ko ƙanwarka ce dai?” wani munafukin murmushi Jawaad yayi tare da ɗagema kamal gira ɗaya sannan ya wani juya kansa da lumshe ido yabar wajen. Sam Kamal bai fahimci komai daga yaren na Jawaad ba, sai dai kuma ya haƙura akan zai nema waje ya zauna harsu tashi tafiya ya bisu a baya, dan shifa yaga matar aure.Tsaye yazo ya sameni ina waya da Zuhrah, baiko kalleni ba yaja kujerar da ya fara zama ɗazun ya sake zaunawa yana maida glasess ɗinsa a ido kamar ma ya manta dani, nima ɗin dai ƙasa-ƙasa nake satar kallonsa yanda nasan bazai fahimtaba ina wayata, a ƙasan raina inata tunanin komi ya cema Kamal? Number wa kuma ya saka masa a waya? Dan nidai nasan baisan tawaba. Zuwan ɗaya daga ma'aikatan wajen ne ya sakani janye idona a kansa, umarnin kwashe kayan wajen ya basa tare da sake kawo wasu, dai-dai lokacin da muka ƙarisa wayar, sai da yabar wajen ne cikin dauriya nace masa, “Ina kwana sir”.
Shiru bai tanka minba, saima ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ɗauke kansa, duk a tsorace nake, gani nake zaimin faɗa akan ganina da Kamal, amma har aka sake kawo abinda ya saka ɗin baice dani komaiba.
Ni kuma har lokacin ina tsaye duk da ƙafafuna sun gaji haka na fuske abina, shiko ya buɗe sabon Popcorn ɗin da aka kawo ya hau ci yanayi yana danna waya, baifi ɗiba uku ba wata mata mai sanye da hijjab har ƙasa da niƙaf ta iso wajen, sallama tai mana, na amsa mata, shiko bangama ya motsaba har sai da taja kujerar gefensa ta zauna, sai da ta ɗage niƙaf ɗin tana gaishesa sannan na fahimci wadda muke jirace.
Batare da ya amsa mata gaisuwarta ba yace, “Kinsan irin ɓata mana lokacin da kikai?” haƙuri ta bashi. Kallona yay ya ɗauke kansa batare da yace komaiba, hakan ya sakani gyara kujera nima na zauna.

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...