Page 5
.............Duk Kasa cewa komai sukai, sai idanu da suka zubama Jawaad tamkar wani bakonsu.
Rose da zuciyarta ke tafasa akan rashin kallonta da jawaad baiyiba ta kasa daurewa, ta dubesu baki ɗaya a wani yanayi, “Boss wai mike fauwane? tai maganar cikin harshen turanci da tsare Jawaad da idanu tana fatan ta dace yanzun.
A mamakinta yanzunma dai ƙin kallonta yayi, sai Lap-top ɗinsa ya miƙa mata kawai, ya koma ya zauna tare da ɗaukar tab.. Ɗinsa ya shiga tafa saƙo da hanzari.
Gani nai Aliyu ya ɗago ya kallesa, yay masa wani salo da ido tare da cije baki, murmushi Aliyu yayi kawai ya maida kansa, kafin ya miƙe yabar falon, hakama Jabeer da Hafiz duk ya tura musu suma, Hafiz shima tashi yay ya fita, Jabeer kuma ya koma kusa da Rose dan kawai ya ɗauke hankalinta da aikin da Jay ya bata itama.
Bayan fitar su Aliyu da kusan mintuna tara ya miƙe yabar falon ya nufi bedroom ɗinsa. Sai da ya kulle ƙofar kafin ya ciro ƙaramar wayarsa yay kiran Hafiz.
“Hafiz yaya? An dace kuwa?”.
“Ba'a daceba Boss, amma ga shawara mana?”.
“Micece shawarar taka?”.
“Mu bincika kowanne manhajar yanar gizo ko zamu dace wani ya ɗauka, kasan yanzu ba'a raba mutane da ƴan ɗauke-ɗauke a waya, maganar gano wanda ya kaima su B.G kuma ba abune mai sauƙiba ace yanzu da gaggawa, sai dai mu canja shawara ta wannan gaɓar”.
“Na fahimceka Hafiz, yanzu kayi duk yanda ya dace, amma inaji a raina koma wanene yakai wannan bayanan yana da kusanci damu Hafiz, amma banason zargin kowa”.
“Boss zargi dolene, kuma koma wanene ya daɗe a jikinmu, a sannu zamu cinmasa da ƙarfin ƙudirar UBANGIJI, dan shine ke haska mana hanya a dukkan lamuranmu”.
“Insha ALLAHU Hafiz, yanzu dai sai na jika”.
Yana yankewa yay kiran Aliyu shima, sai dai daga ɓangaren Aliyun an dace, dan ya turo masa dukkan bayanai akan Bilkisu da abinda ya shafi shigowarta hukumar tasu, da horon data samu, da ƙwazon data nuna tun a wajen horaswa, alaƙarta da Qaseem, sai dai babu wani bayani kafin zuwanta gidansu Qaseem ɗin, hakkanne yaɗan tsayama Jawaad a zuciya, har yakejin dolene ya sake binciken, dan karfa nan gaba ta zame masa ƘWAI CIKIN ƘAYA kuma kamar yanda ƴan bayan fage ke hasashe.Daga ɓangaren Hafiz ma an dace daga baya, dan kuwa cikin amincin ALLAH ya samo bidiyon faruwar komai tun daga lokacin da Bilkisu ta kaima motar masu laifin caffa kafin zuwansu, har zuwa sanda abubuwa suka lafa.
Yaci karo da Bidiyon ne a wani chennal na youtobe, bayan ya shiga manhajar Google yay Searching, sai dai abinda ya bashi mamaki yana kammala sauke video'n akan manhajar ta youtobe wanda ya ɗora ɗin ya saukeshi daga accaunt ɗin, hakan sai yay bala'in ɗarsa mamaki a zuciyar Hafiz, harya kasa haƙuri ya kira Jawaad ya shaida masa.
Murmushi Jay yayi yana shafa kansa, “Ba abin mamaki bane Jabeer, musamman idan mukai la'akari da babu wata kafar yaɗa labarai da dama ta saki bidiyon mai tsawon hakan, sai wasu ɓangarori da dukansu iya inda muke musayar wutane kawai”.
Hafiz yace “Hankalina sam bai kaiba sai yanzu kam, koma miye yake a ɓoye ALLAH zai bayyanashi ai, mudai domin ALLAH mukema ƙasarmu aiki, duk mai yunƙurin daƙilemu kuma ALLAH zai mana maganinsa”.
“Insha ALLAHU kuwa Hafiz” Cewar Jay cike da takaici.Kafin dare duk sun haɗa bayanan da ya kamata akan maganar, sun tura iya waɗanda Sir Ahmad ya umarcesu zuwa Office ɗin, L.G, sauran kuma sun adana a wajensu domin ya zame musu hujjar kare kai, hatta da bidiyon suma gutsira sukai suka tura, sauran kuma suka adana a wajensu.
___________★__________
SHAHUDAH
_________________________________Tunda suka fara zuwa gidan rasuwarnan sau ɗaya taga Jawaad, harga ALLAH ita kuma dominsa take zuwa, a tunaninta idan suka haɗu zai matuƙar rikicewa da ganinta, musamman ma yanda ta sake canjawa da ƙyau mai ƙayatarwa, sosai ta gama shirya shika-shikan rama dukkan abubuwan da yay mata kafin ta yarda da buƙatarsa ta komawa gidansa.
Sai dai abin mamaki da al'ajabi dukkan tunaninta sai bai zama gaskiyaba, dan kuwa ko a randa suka haɗu kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, komai kuma a kan idanun Mom ya faru, dan suna a falon mama Atika ne a washe garin rasuwar ya shigo da baƙi su Sir Ahmad da sukazo gaisuwa. Sarai idanunsa sun gane masa Shahudah, amma sai ya ɗauke idanu cikin nuna halinsa na ko'in kula da abu.
Abin ya sosa mata rai sosai, amma saita danne da yaƙinin ƙila yayi hakane saboda ganin suna cikin jama'a. Koda suka koma gida sai basuyi maganar da Mom ba, saboda kowa ya dawo a gajiye wajen bacci yafi buƙata. Washe gari kuwa kwalliya tayi ta musamman dan Jawaad nanma babu sa'a, dan har dare da suka baro gidan bata sakashi a cikin idanunta ba, washe gari kuma suna isowa gate ɗin gidanne motar Jawaad ɗin ke fita da alama ya nufi office ne. Waɗanan akasin da akaita samune suka jefata a cikin damuwa har yau ta kasa daurewa.

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...