19

13.2K 993 76
                                    

Shafi na goma sha tara


..........A wannan tsakanin kam sai abubuwa suka sake rikice musu a gidan, dan salo-salo na rashin mutunci Shahudah ta ƙaro take tsulama Jawaad, shiko sai ya watsar da ita tamkarma bai san da ita a gidanba, yama koma ba kullum yake kwana a gidanba, gara yaje gidansa da su Aliyu suke yay kwanciyarsa acan, idan suka takura masa da tambayar lafiya yace Shahudah bata nan ne.
    Tun suna yarda da zancensa har suka fara zargin akwai dai wata a ƙasa, amma tunda bai basu damar saniba sai basu takura ba, sun dai ɗauki aniyar tayasa da Addu'a.
         Cikin hikimar UBANGIJI sai yay ma Jawaad maganin Shahudah ta hanyar jarabtarta da laulayi mai azabar tsiya, dan takai yanzu ma sai da taimakon wani take iya wasu abubuwan, shi sai bai duba abinda take masaba, a duk lokacin da ta nema taimako yakan taimaketa inhar yana gidan.
         Abu ɗayane har yanzu ta kasa samu a gareshi, shine sakin fuska, gaba ɗaya tabar ganin haƙoransa a waje, baya wata doguwar magana da ita, idanma yanaji da shariyar sai yazo gidan ya fice bai tanka mataba, tun abun baya damunta harya fara yanzu, dan kuwa tana tsananin buƙatarsa a kusa da ita kuma, sai dai dukkan damar hakan ya toshe mata ita.
      Inhar a gidan ya kwana da safe zai leƙa ɗakinta yaji yaya jikinta?, zai kuma tambayeta abinda take buƙata, inhar ta faɗa zaisa a sayo mata.
     Idan kuma da dare ya dawo koda ya isketa a falone zai tambayeta yaya ta yini? tana buƙatar wani abu? Iya amsar data bashi zai saurara yay wucewarsa ɗaki, yana shiga yake kullowa dan karma ta shigo masa. Ba ƙaramin zafi hakan yake mataba, harma tanaji tamkar taje ta zubar da shegen cikin taga ƙarshen iskancinsa.
      Sai dai zuciyarta na tuna mata gargaɗinsa na ranar, yayi rantsuwa da inhar ta zubar ta tsinka igiyar aurensu duka uku, tasan wanenen Jawaad, tasan kuma zai iya tunda har ya hau dokin zuciya akan hakan.. 
      Ita shaida ce akan haƙurinsa, sannan kuma tasanshi inhar yay zuciya da abu akansha fama kafin ya waiwayesa, a zahiri mutane sukaga sauƙinsa yayi yawa, amma saika nutsu dashi zaka fahimci murɗaɗɗen halinsa na ra'ayin riƙau, mahaifiyarta kace mata haka mahaifin Jawaad yake, dan haka dukkan hallayar Jawaad na ubansa ne, ya kuma kwaso wasu daga uwarsa, dan itama lumbu-lumbu take wutar ƙaiƙayi.

       A yau dai kam lamarin nasa ya mata tsanani, dan ko mama Atika tabi duk hanyar da zataga Jawaad yaƙi bama kowa damar hakan hatta da kawun nansa, saima Qaseem ne ya samu damar gaggaya masa magana a kan Shahudah a office, sai kuma Jawaad ya manna masa hauka ya sharesa tamkarma bai san da shiba.
      Waɗannan abubuwa suka taru akan Shahudah sukai mata yawa, dan haka ta shirya zuwa gida kozata samu sassauci dan yau tana ɗan jin jikin da sauƙi.
     Dama ita babu tambayar fita a tsarinta, shirin ta tayi ba tare data nema izininsa ba, shi dama baya gidan, a office ya kwana yau.
        Shirinta tayi cikin wando da riga jeans da top baƙa mai adon stones an runbuta *Beauty* da manyan baƙi da su, tayi ƙyau dan ƙyau, saboda farar fatarta na ɗaukar wankan ƙananun kaya da kalar baƙi, cikin a lafe kamar babu ɗa a cikinsa, yau dai ba'a samu damar zane fuska da kwalliya ba, fauda kawai aka shafa sai lipsgloss, ƴan arziƙin na kusa kuma, aka saka kimono tare da yafa siririn gyale akai, sai dai an saki rigar ba ɗaureba, hakan yasa taketa jan ƙasa a baya, ga glasess baƙi da aka toshe fuska dashi, ta dai fito asalin ƴar gayenta lamba ɗaya kuma shafin farko a jaridar manya.
        Da kanta taja motar, yayinda kiɗa mai taushi ke tashi daga sifikun.

_______________________
BILKEESU
_______________________

  
           Tun a harabar gidan nake tsarkake sunan ALLAH, dolene akira dukiya jarabawa ga bawa, yanzu mai wannan muhallinma dan yace ya manta da danginsa ai bakaga laifinsa ba, wani dai saikaga tamkar alƙalamin rubuta ƙaddarar rayuwarsa a hannunsa yazo.......
        Zungurata da akaine ya sakani dawowa hayyacina babu shiri, harara ta gallamin da jan tsaki, “K dalla baƙauyar banza ki wuce muje, kin wani zauna kallon gida, halan yau kika fara ganin irinsa?”.
       Bance komai ba, sai bin bayanta da nayi kawai.
      A falonma dai akwai abin kallo da bakima bazai iya lissafowaba, abinda kawai zan iya faɗa hotunan masu gidan da aka ƙawata adon falon dasu, a yanda naga hotunan da alama yaran nasama sun zarta biyu, dan kuwa bayan waɗan na gani ga mutane uku kuma a hoto, namiji haɗaɗɗen saurayi maiji da kansa, sai ƙyaƙyƙyawar budurwa da tafi dukkan ƴan gidan asalin ƙyawu, saikace wata jinin larabawa, dan nikam bazan ce baturiya ba, dan ba ƙyawunsu nake ganiba, sai dai shigar tatace kam sak ta turawan ce, sai hoton namiji again da bazai wuce shekaru goma sha biyarba, hoton dai da gani tsohon hotone.
     Na sake waigawa ko zanga inda yake babba sai dai babu.
      Tunda muka shigo kawu saman bene ya haye, hakan ya saka hajiya binsa itama.
       Suma duk sai suka shige ɗakunansu aka barni ni kaɗai a falon tamkar mayya, hakan baisa naji rashin daɗiba, koba komai nasamu damar yima falon kallon tsaf ai.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now