Page 33
...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad, ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar maganinsa ne.
Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati, shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a yanzuba.
Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
Momy dake haɗama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table ɗin, gaba ɗaya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi, wani irin jin ƙarin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana mai dangwarar masa da kofin tea ɗin gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?”.
Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna, lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna, nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku aka harɗa komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!”. Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban ɗauki matakin ƙarshe akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!” ta ƙare maganar da buge table ɗin ta tashi tabar wajen.
Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyasa batasan mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
Aamilah dai baki ta taɓe ta cigaba da sauraren waƙarta dacin abinci, Shahudah ce dai ta kalli Dad ɗin bayan ɓacewar Mom a idanunsu. “Dad wai faɗa kukeyi ne?”. Huda tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma ƙanana a yanzun saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl ɗin data saka masa farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take zargin.

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...