4

12.2K 1.1K 135
                                    

  Page 4

...............Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana batare daya bar danne-dannen tab... Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”. Yay tambayar cikin nuna halin ko'in kula balle su sami ƙwarin gwiwa akan ya jisun.
      Duk kallonsa sukai da mamaki saboda yanda sukasanshi dason mutum mai himma, amma yanda ya amshi maganar ya matuƙar basu mamaki a yanzun.
      Jabeer ne yace, “Yarinyar jiya daka bama jini mana Jay”.
       “Humm” yace kawai ya sharesu bai sake tankawa ba, tsawon mintuna duk sun zura masa idanu suna jiran ƙarin bayani, dan sunyi tsammanin fara jin yabon yarinyar da ga bakinsa ma kafin su su furta, amma ya share kamar ya manta dasu ma a office ɗin.
        “Wai boss lafiya kuwa?” Hafiz yay tambayar a wani yanayi.
    Sai yanzune ya ɗago ya kallesu su duka, kallo irin a taƙaice ɗinan ya janye mayatattun idanunsa masu cikar gashi da haske tamkar madara, ya taɓe baki kaɗan kafin ya miƙe daga wajen ya nufin kujerarsa ta zama, dan da suna zaunene a rukunin kujeru da'aka shirya a office ɗin domin hutawa ko ganawa da baƙi na musamman. 
        Sai da ya zauna sosai ya juya kujerarsa tana fuskantarsu kafin yace, “Abun harinmu a yanzu shine mutuwar jami'inmu da sir Ahmad yamin bayani, minene shawararku akan hakan?”.
          Aliyu ne ya samu damar faɗin, “Bincike akan shi ɗin wanene? Tunkan fara aiki a wannan hukumar har zuwa farawar tashi, tare da sanin masu bashi gudunmawa akan aikin da yazama sanadinsa, da kuma sanin a ƙarƙashin wa ya samu umarnin”.
         “shawara mai ƙyau” Jawaad ya faɗa yana lumshe idanu da kwantar da bayansa jikin kujerar yana lilawa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi, kusan sakanni biyar kafin ya sake ɗagowa yana kallonsu da nazartarsu.  Ya ɗauke idanunsa tare da sake komawa jikin kujerar ya kwanta, “Idan an sallamota daga asibiti zatayi bincike akan dukan bayanan Aliyu”.
        Cikin matuƙar mamaki suka kallesa, cikin harɗewar harshe Jabeer yace, “wai kana nufin yarinyar?”.
     Kallonsa kawai yay ya janye idanu, sai dai baice komaiba. Sun fahimci amsar kenan, dan haka Aliyu yace, “Amma boss baka ganin aikin zai mata girma? Musamman idan mukai dubi akan shine na farko?”.
         Cikin halin ko in kula ya taɓe baki, ba tare daya kallesu ba yaja wasu takardu dake saman tebir ɗin nasa yana faɗin, “Maybe hakan, maybe kuma ba hakan baneba, naga kuma da kanku kun yarda da ƙwazonta, to miye kuma na kokwanto yanzun?”.
      Babu wanda ya sake cewa komai. sai dai a ƙasan ransu duk sai suka kasance cikin nadamar kwarzanta ƙwazon yarinyar da yawa irin haka, dan a ganinsu bata kai ƙwarin da za'a sakata a irin wannan babban aikin hakaba mai haɗari, musamman idan sukai dubi da ko rose data daɗe a cikinsu baya bata irin wannan damar.
      Takardar da ya maida hankali a kanta ya ɗago saitin Hafiz, “Hafiz wanene da wannan bayanan haka?”.
      Tasowa Hafiz yay ya dawo gabansa, ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana mai amsar takardar, nazarin mintuna biyu ya ɗago kai yana kallonsa, “Akan case ɗin yaron nan da aka samu makamai a shagonsu ne, Aliyu ne akan binciken kuma”.
     Jawaad ya maida kallonsa ga Aliyu, hakan ne ya saka Aliyun tasowa ya nufosu shima.

              __________★★__________
                           BILKEESU
     _________________________________

                 Wani irin mayataccen ƙamshi ya shiga rige-rigen zirarawa cikin ƙofofin hancinanmu yayinda muke shiga motar da boss ya turo ɗaukarmu, batare da kowannenmu ya fargaba muka tsinci kawunanmu da lumshe idanu muna sake buɗe hancunan namu sosai. A haka yaja motar muka bar asibitin, tabbas wannan ƙamshine daya cancanci ajiyeshi a ma'ajin zuciya da ƙwaƙwalwa saboda ya kasance na musamman, bansan miyasa na kirashi na musammanba, sai dai kawai zan iya fassara hakan da kasancewarsa na musamman a duk lokacin da hanci ya shaƙa koda ba namuba. Naji tamkarma kar motar ta tsaya ace na daina shaƙar wannan ƙamshin, sai dai babu yanda zanyi dan hakan tilasne. A wannan yanayin muka isa gida, ya ajiyemu a gate ya juya, mukuma muka shiga ciki bayan mun masa godiya.
      Mun iske gidan babu kowa, suna gidan rasuwa su duka, dan haka mukai zamanmu dagani sai Ummie da tace boss ya bata umarnin ta zauna dani harna warke tun a jiya. Ban tambayeta daliliba, kamar yanda itama bata kawo komai a rantaba game da hakan, sai dan tana ganin ya fahimci bani da wadda nakeda kusanci da shi sama da ita a station ɗin namu.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin