20

11.9K 1.1K 674
                                    

Page 20

.................“Ya salam” Jawaad ya faɗa tare da ranƙwafawa ya ɗaga frame ɗin da hoton ke ciki, a bisa tsautsayi ya ɗaura hannunsa kan glass ɗin da ya maƙale kaɗan bai ida fitaba, yay tsini siriri, “ouch!!” ya faɗa yana yarfe hannunsa saboda shigar zafin bazata. Alhaji baba ya taso da hanzari garesa, hannun da yake yarfewar ya kama, abinka da jiki babu wahala tuni jini sai rige-rigen fita yake, abin mamaki har yana neman wuce girman ciwon da yajin. Daga Alhaji baba har Jawaad sai fitar jinin da yawa ta basu mamaki, dan sosai yake ɗiga a ƙasan tiles ɗin tamkar wanda yay wani uban yanka, Jawaad yay ƙoƙarin ajiye hoton saman drawer batare da ya kallesa ba sai kawai ya sake ɗora ƙafarsa akan glasess ɗin dake zube ƙasa. Da sauri ya ɗaga ƙafar tare da sake damƙe hoton a hannunsa yaja da baya yana faɗin,  “Yah ALLAH”. 
        Alhaji baba yace, “Subahanallahi sake takawa kayi?, to kaga zauna ina zuwa”. Zama Jawaad yayi ya ɗora fasashshen frime ɗin da ya rage katako da katin hoton kawai a cinyarsa yana tarbe ɗigar jinin hannunsa da ɗayan hannun wanda tuni jinin ya ɗiɗɗiga a hoton ma. Sai dai hankalinsa bai kaiba, har Alhaji baba ya dawo ɗauke da ruwan ɗumi a roba mai ɗan faɗi da guntun towel, a hannun kujerar ya ɗora ya kama hannun Jawaad ya saka a robar tare da jiƙo towel ɗin da ruwan zafi ya goge masa hannun tas dukda dai jinin yaƙi tsayawa har yanzu yana ɗiga, kamar yanda sukai hasashen ɗan yankan bawani mai yawa baneba,  tissue ya warwaro ya ɗora masa dai-dai yankan yana mai tsokanarsa da cewar, “Lallai cin kayan daɗinka yay yawa na wajena, kaga ɗan yanka kaɗan amma jini yayi rabin botiki”. Babu shiri Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, “Oh ALLAH, tsohon nan kana hawa kaina da yawa wlhy, idan yakai rabin botiki ai saidai a ɗiba naka a ƙaramin kenan”. Dariyar alhaji baba yake shima, ya durƙusa tare da kamo ƙafar Jawaad ɗin itama dake jinjin ya saka a robar, kwalbar data sokesa anan tana ciki, hakan yasa Alhaji baba shammatarsa ya cirota, “Ouch!!” Jawaad ya faɗa yana rintse ido dan yaji zafi, ciwon ƙafar yanada ɗan girma, Alhaji baba ya ɗaure masa dan su samu jinin ya tsaya.
         Batool ce ta shigo da sallama ɗauke da abincin kakan nasu. A tsorace take kallon jinin da ƙafar Jawaad ɗin, “Ɗan uwa garin yaya haka?”. Fuska yaɗan yamutsa yana kallonta, yace, “Tsautsayi mana”. Sannu ta shiga jero masa, ta ajiye basket ɗin ta ƙaraso ta amshi tsintsiyar hannun Alhaji baba danta share kwalban kamar yanda taga yana niyyaryi. Jawaad ya sake kai hannu zai ɗauke hoton daga cinyarsa dan yanason ya tashi yaje yay wanka, sai idanunsa suka sauka akan waɗanda ke jikin hoton, dukda jininsa dukya ɗan ɗiɗɗiga a jiki, hakan bai hanashi ganin fuskar mahaifiyarsaba ras a jiki, tayi ƙyau sosai tana murmushinta mai birgewa, ya maida idonsa akan ta kusa da ita, autarsuce da suke kira aunty Mammah, itama ALLAH yay mata rasuwa shekaru masu tazara bayan ɓatan mahaifiyarsa, haka kawai ya samu kansa da tsura musu ido harna tsahon lokaci, sai da Batool ta ɗauke hoton daga hannunsane ya dawo hayyacinsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana miƙewa. Batool dake kallon hoton tai murmushi da share guntayen hawayen da suka cika mata ido saboda tuno da Gwaggonnin nata guda biyu da suka rasa a ƙaddarar mutuwa da ƙaddarar taɓin hankali.
            Koda Jawaad yay wanka ya kimtsa ya fito bai zauna cin abincin da Batool ta kawoba, sai ya ɗauki hoton daya fasa zai tafi dashi akan zai sabunta masa glass, babu yanda Alhaji baba baiyiba amma yaƙi ya ajiye. Cikin tsokana Batool tace, “ALLAH yasa ba sace maka zaiyiba Alhaji baba”. Harararta Jawaad yay ya fice, batare da ya jira amsar da Alhaji baban zaiba Batool ba.
     Maimakon ya nufi gida kamar yanda yay niyya sai kawai ya wuce office, ta waya ya kira Gimba yasanar masa shi yana office anjima yazo ya samesa zasu fita. Cike da girmamawa gimban ya amsa masa sannan suka ajiye wayar.
      Koda Jawaad ya shiga station kai tsaye office ɗin Jabeer ya nufa, shima da alama bai jima da isowarba, ya ɗago yana kallon Jawaad daya shigo office ɗin da sallama, murmushi yay masa, shikuma Jay ya hararesa yana ƙarasowa ya zauna a kujerar dake gaban tebirin ɗin.  Hannu ya miƙa masa sukai musabaha, murɗe hannu  Jay yay har saida Jabeer yay ƴar ƙara, ya fisge yana hararsa da faɗin, “ALLAH kai mugune na bugawa a takarda, ciremin hannun zakayi boss”. Murmushi Jawaad yayi yana miƙa masa key ɗin motarsa da faɗin, “Gobema ka sake yin gulma”,.  Jabeer ya sake hararsa yana juya hannunsa, “Kasan ALLAH Jay, yau da ace ba sunan momine da itaba da akanta zan rama, ALLAH ya ceceta kuwa”. Murmushi Jay yayi yana taɓe baki, yace, “Kaje ka rama mana ina ruwana, Am sorry jiya na maka tsawa, rainane duk a jagule kaikuma kazo zaka sake cazamin kai da naka shiriritan”.
        Murmushi Jabeer yay yana shafa kansa dajin ƙaunar abokin nasa cikin rai, “Ni dama ban ɗaukesa komaiba, nasan wanene Jay ɗinmu idan yay fushi, ina fatandai itama Momin tamu ka bata haƙuri, dan na koma office ɗinka kusan 3:45 na isketa tana kuka”. Haɗe fuska da lumshe idanu Jay yayi yana sauke numfashi, “Ai  yarinyarnan bata da kunya. manta da zancenta, ina fatan su Hafiz sun iso, dan inason muyi magana”. Kamar yanda ya buƙata sai Jabeer ya bar zancen bily, ya amsa masa da, “Okey bara na kirasu to, nasan duk sun iso yanzun”. Gyara zama Jay yay, yayi shiru har Jabeer ya gama kiransu. Babu wani jimawa sai gasu duk sun shigo, saida suka gaggaisa sannan kowa ya nema wajen zama, Aliyu da idonsa ya sauka akan yatsan Jawaad dake naɗe da bandage yace, “Boss miya samu hannun kuma haka?”. Hannun Jawaad ya kalla yana ƙaramin tsaki, “Wlhy Aliy wani ɗan ciwo naji, shinefa Alhaji baba yaymin wannan naɗin”. Dariya duk sukayi, Hafiz yace, “Shi ka kaima fushin jiya kenan?”. Hararsa Jay yayi amma baice komaiba.
          “Kunga ku ajiye shiritarnan taku muyi magana yau inada aiki a office saboda jiya banyi komaiba”. Duk hankalinsu suka maida gareshi, Jabeer ya direma kowa kofin coffee daya haɗo, “Thanks ” Jawaad ya faɗa yana ɗaukar kofin, suma su Hafiz sukai masa godiya, Jawaad yakai kofin bakinsa sanan ya janye idonsa a kansu, sai dai yay matuƙar canja fuska saboda maganar da zaiyi tana zafarsa a cikin rai, “Guys dolene yarinyarnan tabar cikinmu a wannan karon, bazan iya cigaba da zama da itaba ta isheni haka nan”. Kallon juna suka shigayi kowa da tsoro akan fuskarsa, Aliyu yay ƙarfin halin faɗin, “Wa kake nufi a cikinsu boss? Kasan yanzu sun zama su biyu”. Kallon Aliyu yayi tamkar bazaice komaiba, sai kuma cikin takaici yace, “Rose nake nufi”. Shiru sukai duk suna jinjina zancen a ransu, kafin Hafiz yace, “Banƙi ta takaba Boss, sai dai hakan zai iya zama wata matsala daban, duk da bansan ainahin abinda tai makaba na kula tanason takurama rayuwar mami ne, abinda kuma na fahimta itafa gani take son Mami kake gaskiya shiyyasa take duk waɗanan abubuwan”. Tsaki Jawaad yaja yana yamitse fuska cike da takaici amma baice komaiba. Suma shirun sukai basu damu da rashin bada amsarba, dan a ganinsu idan son Bilkisu yake wataran ai dole ta fito fili ko. Jabeer ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Gaskiya boss hakan ba shine mafitaba, na farko Rose tasan sirrikanmu da yawa, yaƙi take akan soyayyarka a yanzu, idan kace ta barmu zaitai amfani da wannan fushin ta koma cin dunduniyarmu, munada muhimman ayyuka a ƙasa waɗanda munyi zurfi sosai na kaiwa ga nasara, sune zata fara harin ɓatawa, karka manta zagaye muke da maƙiya, ƙaramar ƙofar da za'a kutsa cikin mutuncinmu kawai ake nema dama, magana ta ƙarshe kuma Rose zatabi duk hanyar da zuciyarta ta ƙawata mata ta cutar da mai sunan mom batare da munsan tayaya ta shirya hakanba, kaga kuwa tako ina korarta ba mafita zata bamuba, domin iyakar gudunmu dai bai wuce kabi ta ƙasa kasa aimata transfer ba, duk nisan da kake tunanin zatayi damu ALLAH saita dawo koda ta hanyar saka wanine yay mata aiki kuwa”.
      Dukansu sun gamsu da maganar Jabeer. Aliyu yace, “Maganar Jabeer fa gaskiyace Jay, sawa tabar cikinmu ba mafita bace, gara ace muna ganin duk motsinta, sannan ni a ganin idan kanason Mami ɗin miza hana ka fito ka bayyana mata kawai a wuce wajen, da zafi-zafi ake bugun ƙarfefa a wannan zamanin”. Fuska sosai Jawaad ya haɗe, cikin nuna halin ko in kula ya wani taɓe baki yaƙi cewa komai a karo na biyu kan maganar Bilkisu. Duk idanu suka zuba masa na mamaki, sun rasa miyake ɓoyewa. Sai da ya shaƙi iska dan kansa sannan yay magana, “Kuna ɓatamin rai da shirmennan naku, kunefa dalilin shigowar wannan yarinyar cikin tawagarnan, amma miyasa kuke son maida zancenta wani abu daban, to inagama ba rose bace ta cancanci yin nesa damu, Miemaa zansa aima transfer, ince dai shikenan”.
     Da sauri Hafiz yace, “Ba shikenanba, yarinyarnan yanzune ta fara aiki, ƙwazon data fara nunawa yana buƙatar a cigaba da horar da ita akan gaskiya, munji ba sonta kakeba, kuma insha ALLAH babu mai sake maka wannan maganar, inaga kawai mu zauna dasu ita da Rose kajama Rose dogon gargaɗi akan wannan haukar tata mara tushe, domin munutsu mu fuskanci sauran ayyukan dake gabanmu, yanzu aikinan da muke wlhy yanada matuƙar sarƙaƙiya da haɗari, amma gashi muna wasa dashi, sai dau ku yaya kuka gani?”. Jabeer dake wani shegen murmushi yana satar kallon Jay yace, “Hakan yayi nidai a wajena, gara a bar mana Miemaar mu muyita kwasar albarkacin sunanta”. Hafiz da Aliyu sukai dariya, dan sunsan shaƙiyancin Jabeer ne ya motsa, Jawaad kam uffan baiceba, saima miƙewa da yayi yay musu sallama ya fita.
     Yana fita duk sukayi dariya, Aliyu yace, “ALLAH Jabeer kasama boss ido da yawa, nakula son ƙureshi kake kawai,, ka barshi yasha iskar duniya malam”. Nanma dariyar sukayi, Hafiz yace, “kunga nima bara na koma Office, gayenan addu'armu kawai yafi buƙata”. “Hakane kam” cewar Aliyu dake miƙewa shima.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Onde histórias criam vida. Descubra agora