57

14.1K 1.3K 209
                                        

Page 57
          
___________________________________
SHAHUDAH
___________________

                 Saukar su Umm-Anum ƙasar haihuwarta tayi dai-dai da komawar Shahudah gida. Mom da Aamilah ne kawai a gidan, Dad ya fita tun bayan barin su Jay gidan. Waya Mom keyi da Mama Atika. A take ta saki wayar ƙasa ta tarwashe bisa tiles jikinta na tsananin tsuma.
         Shahudah da ke cikin wani yanayi kamar ba'a hayyacintaba ta ƙaraso cikin falon tana tangaɗi ta zube saman carpet. Da ga Mom har Aamilah zubewa sukai a gabanta jikinsu na rawa, sai kuma Aamilah ta miƙe da sauri taje ta leƙa waje. Babu kowa sai maigadi daya taimakama Shahudah ta shigo ya juya zai koma wajen gate. Komawa falon Aamilah tayi bayan ta rufe ƙofar ruf ta garƙama mata key. Ta koma wajen su Mom da gudu tana faɗin “Mom ita kaɗaice fa wlhy babu ɗan iskan”.
     Mom tace, “Nashiga Uku ni Aysha, Shahudah daga ina kike haka? Miyayi miki ne?”. Bata da mai amsa mata waɗanan tambayoyin dan Shahudah sai faman lumshe idanu kawai take. Mom ta ƙanƙameta a jikinta ta fashe da kuka tana jama ɗan-fir'auna mugayen addu'oi. Suna cikin haka akai knocking ƙofar, duk ɗagowa sukai suka zubama ƙofar falon ido kawai, sai dai daga Mom ɗin har Aamilah babu wanda ya iya motsawa. Shiru ba'a sake bugawar ba, hakan yasa suka share suka maida hankalinsu ga Shahudah.
        Salman dake buga ƙofa ganin ba'a buɗeba sai ya zagayo ta kitchen, shikansa ba ƙaramin mamakin ganin Shahudah yay ba, jikinsa har rawa yake wajen ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa Shahudah ta dawo.

        Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dad a hargitse kamar zai tashi sama, yanda yake buga ƙofar kawai kasan babu lafiya, Aamilah ta buɗe masa tana matsawa ta bashi hanya, da sauri ya shigo. A gaban Shahudah ya durƙushe tare da maido kanta jikinsa idanunsa na kaɗawa lokaci guda dan ɓacin rai. “Shine ya kawota?”. Yay tambayar yana kallon Mom. “Nima ban saniba Dadynsu, shigowarta kawai muka gani ita kaɗai. Leɓe Dad ya taune da ƙarfi, ya kalli Salman dake tsaye cikin damuwa shima, “Kai Salman kiramin Dr Tayyib, ke kuma Aamilah kiramin maigadi, ai bazai rasa sanin wanda ya ajiyeta ba”.
         Babu jimawa maigadi da Aamilah suka dawo falon, cikin girmamawa Maigadi ya rusina yana gaida Mom. Bata amsa masaba, sai Dad ne ya jefa masa tambaya, “Yaya akai Mamana ta dawo gidan nan?”. “Wlhy Alhaji ban saniba, kawai naji nishin mutumne a jikin gate, shine na leƙa nama zata ko yaran nanne masu addabama mutane, sai naci arba da ita kwance jikin gate ɗin, sai kuma ƙurar mota da nake zargin a ita aka ajiyeta”. Ran Dad ya ƙara digunzuma sosai, yay ma maigadi nuni da hannu alamar ya tafi kawai.
     Maigadi na fita Dr Tayyeb na isowa gidan, bai zaman ɓata lokaciba ya shiga bama Shahudah taimakon gaggawa bayan an kaita ɗakin Mom an kwantar a gado. Duk wani taimakon da ake buƙata Dr Tayyeb ya bata, ya kuma tabbatar musu da cewar babu wata matsala normal zata farka insha ALLAH, ruɗanine ya sakata shiga wannan halin kawai. Hakanne ya basu ƴar nutsuwa, har suka kira su Mama Atika suka sanar musu dawowar Shahudah ɗin.

          Normal Shahudah ta farka a safiyar yau kamar yanda Dr Tayyeb ya sanar musu, kasancewar ɗaki ɗaya, gado ɗaya ta kwana da Dad da Mom sai suka baibayeta da tambayoyi akan abinda ya faru da ita?. Tsaf ta kwashe yanda akai ta sanar musu.
         “Dad ashe shiɗin ba mijina bane, tunda ya tafi dani wani gida ya kaini kawai ya ajiye bamma sake ganinsaba sai bayan kwana huɗu, ya sanarmin a randa aka ɗaura mana aure a ranar Bb ya saka shi ya sakeni, yace dan kawai yana ganin mutuncinsa yay hakan, amma badan Bb bane wlhy ko za'a kashesa bazai sakeni ba, kuma koda ya sakeni badan na taɓa zama matar Bb ba da bazai ƙyaleniba sai ya ketamin mutunci, wai Bb yana da kimar da bazai iya mu'amulantar abu shima yayi hakanba, Mom wlhy Bb mutumin kirkine, dan ALLAH ku bashi haƙuri mu koma aurenmu kamar da, ALLAH yanzu na amince zan haihu ko nawa yake so”.
     Mom da Dad da mamaki ya cika suka kama hannayenta cikin nasu, cikin zafin rai Mom tace, “Zaki koma gidan Jawaad kuwa Shahudah, zaki koma kodan shegiyar yarinyar can tasan asirinta aikin banzane, namiki alƙawarin a yau ɗin nan basai gobe ba za'a maida aurenku da Jawaad”. “Mom da gaske? Dad kaima kuma ka yarda da hakan?”. “Ɗari bisa ɗarima kuwa mamana, duk abinda kikeso a duniyarnan saikin samesa ko minene shi, duk abinda Momynku ta faɗa kisa a ranki ya gama tabbata”. Rungume Dad tayi tana fashewa da kukan jin daɗi, suma suka rungumeta cike da so da ƙauna harma da tausayinta.
          Gari na ƙarasa wayewa Mom ta ɗauki Shahudah suka tafi family house ɗinsu.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang