17

13.6K 980 71
                                        

Shafi na goma sha bakwai


.............A gaggauce yay shirin cikin Suit kalar ruwan goro mai duhu, sai rigar ciki data kasance ruwan bula mai haske, yanada kaya a gidan, saboda duk randa Shahudah ta haɗa masa zafi to nan ne wajen fakewarsa ya samu nutsuwa, shiyyasa yake da abubuwan amfaninsa.
     Turare ya fesa kaɗan ya fito yana ƙoƙarin ɗaurama hannunsa a gogo, rigar suit ɗin ta sama rataye a hannunsa dan bai sakaba.
     Su Aliyu dake zaune a falo cikin shirin fita suma suna jiransa duk suka miƙe idonsu a kansa.
        Jabeer ya kama hannun da Jawaad yake ɗaurama agogon yana ƙarasa ɗaura masa.
      Bai musaba ya miƙa masa hannun yana maida hankalinsa ga Hafiz.
      “Hafiz ka kulafa sosai, dan ƙaninsa ɗinnan shegen wayone dashi, duk wani motsinsa inda yake zuwa, da wanda yake mu'amula da dai komai nasa ku sani, a koda yaushe yakan nuna yanason yayan nasa fiye da kansa”.
      Ya ƙarasa maganar dai-dai Jabeer na gama ɗaura masa agogon, yace, “Thanks”.
     Kai kawai Jabeer ya ɗaga masa, sukai ƙoƙarin ficewa.
    Jawaad na gaba suna binsa a baya su uku, dolene ka gansa su burgeka sosai, dan kallo ɗaya zakai musu ka tsinkayo tsantsar jarumtar aikinsu a fuskokinsu.
       Gimba ya gaishesu cikin girmamawa, sannan ya buɗe ma Jawaad mota ya shiga.
       Suma sauran kowa mota ya shiga, Jabeer shi kaɗai, Hafeez ma shi ɗaya.
         Sai Aliyu da ya shiga kusa da Jawaad zasuje gidan Alhaji kokino tare.
      Shiru Jawaad na kwance a bayan mota, kansa kwance jikin kujera. yayinda idanunsa ke buɗe yana kallon titi.
     Dai-dai danja ta tsayar dasu idonsa ya sauka akan wata mahaukaciya dake tsaye bakin titi tanata soshe-soshe, kafeta da idanu yayi ko ƙyaftawa bayayi, Gimba da Aliyu da basusan mike faruwa ba suna ɗan magana jefi-jefi, gimba yaja motar sukai gaba.
     Jawaad yasa handkherchief ya tsane hawayen da suka cika masa idanu, yanajin kewar mamansa sosai, irin yanda bakinsa ma bazai iya furtawa ba, ya lumshe idanunsa yana magana a hankali akan laɓɓa wanda inba kusa da shi kakeba bazakajiba.
         “Boss mun iso”
Gimba ya sake maitawa Jawaad da yay nisa cikin tunani sam baisan harma sun samu damar shigowa harabar ƙaton gidan Alhaji kokino ba, Aliyu da gimba harsun fita a motar sai shi kaɗai.
        Numfashi mai nauyi Jawaad ya sauke yana kallon Gimba da idanunsa dake a rine da damuwa?.
     Baice komaiba ya ziro ƙafafunsa ya fito, agogonsa ya ɗan kalla kafin ya maida kallonsa ga dogon ginin benen gidan,
        “Ali muna buƙatar ai mana iso fa”.
    “Yes Boss, ai mai gadin ya shiga ya sanar musu ma”.
     “Ok” Jawaad ya faɗa yana tura hannayensa biyu cikin aljihun wandonsa kamar maijin sanyi.
        Kusan mintina uku sai ga mai gadin ya dawo, shine yay musu jagora har ƙaton falon baƙi dake a cikin gidan, sannan yay musu sallama ya fita.
        Zamansu baifi na mintina ukuba wata dattijuwa ta shigo ɗauke da ƙaton tire, ta ajiye sannan ta risina ta gaishesu, cikin kulawa Jawaad ya amsa mata.
     Tana fita babban yaron Alhaji kokino ya shigo cikin kayan barci, da alama ma tasoshi akayi daga barcin, dan yanayinsa ya nuna hakan.
     Hannu ya bama Jawaad suka gaisa tare da Aliyu da Gimba, sannan ya samu waje ya zauna hankalinsa akan Jawaad.
        “Yallaɓai ko an samu wani ƙyaƙyƙyawan news ne haka?”.
         Jawaad dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya girgiza masa kai yana gyara zamansa, “Babu wani labari mai nuni da nasara abokina, yanzu ma munzone dan inason ganawa da dukkan jama'ar gidannan idan babu damuwa”.
       “Babu damuwa yallaɓai, barama kaga naje na tattarosu”.
      Kai Jawaad ya jinjina masa cikin lumshe idanu, ya miƙa hannu ya amshi system ɗinsa dake a hannun Aliyu, saman cinya ya ɗorata yana ƙoƙarin kunnawa. A haka jama'ar gidan suka fara shigowa cikin sallama.
       Jawaad bai ɗago ya kalli kowa ba a cikinsu, danne-dannensa kawai yake a lap-top.
        Kowannensu mazauni ya samu, budurwar da tunda ta shigo idonta ke a kan Jawaad ta miƙe daga inda ta zauna tana faɗin, “A yallaɓai ko shayi ai kwasha, dan da alama kunyo sammakon barin gida”.
         Ɗan murmushi Aliyu yay kawai, Jawaad kam ko motsi baiyiba balle zancen ɗagowa, zata fara ƙoƙarin haɗa shayinne Aliyu ya ɗan kalleta yana girgiza kansa, “No Please barsa kawai”.
      Da sauri Uwargidan Alhaji Kokino dake ƙoƙarin zama ta katsesu da faɗin, “A'a haba dai, in kuka ƙi kuwa bazamuji daɗiba sam”.
     Murmushi kawai Jawaad da ya kallesu yayi, amma baice komaiba, dan haka shema'u ta cigaba da haɗama su Jawaad shayin, cike da yanga ta kalle Jawaad kamar shi kaɗai kawai take gani a wajen tana faɗin, “Asa shuga da yawa?”.
        “Spoon ɗaya ya isa” Jawaad yay magana a taƙaice ba tare daya kalleta ba.
         Koda ta kammala tazo miƙa musu sai da fara bama Jawaad, saboda neman magana saida tai yanda hannunsu ya gogi juna, hakanne ya saka Jawaad ɗago idanu ya kalleta, yanda ta kafesa da natane ya sakashi yin luuu da nasa cikin salon isa irin na mazan da suka isa ya janye daga nata yana faɗin, “Thanks” a hankali.
     Tai murmushi saboda jin daɗin godiyar da yay mata, wajen zamanta ta koma bayan ta bama Aliyu da Gimba suma, inda take facing ɗin Jawaad da har yanzu bai kai shayin bakinsa ba yana cigaba da danna lap-top ɗinne.
     Amaryar Alhaji kokino ce ƙarshen shigowa cikin shiga ta alfarma, ta samu waje nesa da kowa ta zauna.
       Sai lokacinne Jawaad ya janye system ɗin daga saman cinyarsa yana maida hankalinsa garesu.
        Shayin yakai bakinsa kafin ya basu dukkan nutsuwarsa yanayin gyaran murya.
         “Zakuyi mamakin cewar da nai a tattaromin ku duka, so amin afuwa idan na shiga rayuwarku da yawa. Dama dai akan maganar Alhaji ne, maganar gaskiya a koda yaushe lamarin nan sake rikitar damu yakeyi, musamman idan mukai dubi da lafiyar ALLAH suka baro filin jirgin, ku kuma gashi kunce bai shigo gidannan ba, sai labarin rashin ganinsa aka kawo muku”.
      “Hakane kam yallaɓai, mu kanmu mun rasa yanda zamu kwatanta al'amarin gaskiya”.
        Kai Jawaad ya jinjina yana duban Amaryar Alhaji.
      “Hajiya kece kuka dawo da Alhaji daga tafiya ai?”.
     Zamanta ta gyara sannan cikin isa tace, “Tabbas tare muka dawo, sai dai shi gida aka wuto da shi, ni ko gidanmu na wuce saboda uzirin san zuwa na duba mahaifiyata da bata da lafiya, mun rabu dashi akan zaije gida ya kimtsa shima sai ya zo yaga jikin nata”.
        Jawaad yay murmushin gefen baki a zuciyarsa ya furta “Kamar yanda aka shirya kenan”, a fili kam sai ya jinjina kansa yana maida hankalinsa ga Uwargidan Alhaji da fuskarta kawai ta isa ta nuna maka tsagwaron damuwarta.
          “Maganar gaskiya Hajiya a yanda nazarina ya nunamin Alhaji ya shigo cikin gidannan, cikin abu uku kuma tilas ɗaya ya kasance”.
       Kusan gaba ɗayansu zuba masa ido sukai cikin wani irin zumuɗi, suka haɗa baki wajen faɗin, “Yana cikin gidannanfa kace yallaɓai?”.
       “No, ba ayanzu nake nufiba” Jawaad ya faɗa yana miƙewa riƙe da kofin shayi a hannu, tamkar malami da ɗalibai haka ya tsaya musu ƙikam dan ya samu damar nazarin fuskar kowa a falon.
        “Cikin abu uku dana ambata dolene a samu ɗaya kuwa, na farko shine, ko dai an shaƙama Alhaji wani abu an barsa a motar da aka ɗakkosa sannan aka sanar da ɓatansa gareku, da ga baya kuna cikin wannan ruɗanin aka sake fita dashi daga gidan, kokuma ba'a fitan dashiba yana cikin gidannan har yanzun, ko kuma tunma a hanya drivern sa ya bada ƙafar da akai canjin motar da aka ɗaukesa da wata, ina nufin da haɗin bakinsa a ciki, dama duk wanda suke tare a wannan lokacin
       Cikin fusata Amaryar Alhaji Kokino tace, “Ban gane mi kake magana akaiba ɗan saurayi, ya zakayi jam'u akan duk wanda yake tare dashi?”.
         Jawaad ya rumtse hannunsa da ƙarfi yana feso numfashi mai zafi, dan ya fara hasala da maganar hajiya Amarya, amma kasancewarsa gwanin ƙwarewa akan aikinsa sai yay azamar dai-daita kansa, “Hajiya ke ai babuke a ciki, saboda tun a filin jirgi kuka rabu kikace? To miye haɗinki ma da tawagar wanda sai da suka shigo har gida dashi?”.
       “Hakane” ta faɗa aɗan daburce.
       Kusan da yawansu lamarinta sai da ya basu mamaki, amma sai basuce komaiba.
    Jawaad ne ya katse musu tunani da kiran sunan Gimba.
    Gimba dake daga can gefe yana aikin nazarin kowansu yay saurin faɗin, “Yes Boss”.
       “Kiramin mai gadin gidannan”.
    Da sauri gimba ya fice, Jawaad kuma ya sake kallon budurwar ɗazun Shema'u data haɗa musu shayi yace, “Zan iya ganin ma'aikatan gidannan duka?”.
      “Mizai hana boss” tai maganar da salonta na jan hankali.
     Idanunsa ya janye yana faɗin, “Wannan ƴar matsalace” a saman laɓɓansa.......
     A mamakinsa sai yaji tace, “Mi kace?”.
     Kai ya girgiza mata alamar babu komai.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Onde histórias criam vida. Descubra agora