12

11.9K 1K 139
                                        

Page 12

.............Babu yanda na iya dole naja hannun Nabeelah muka nufi office ɗin, sai dai tunma a hawan farko aka dakatar da Nabeelah, ni kaɗai aka bari na wuce, kamar na fasa kuka haka naji, sai dai nayi mamaki a raina yanda babu wanda ya tambayeni mizanje yi?.
Office ɗin na nan tsaf, duk da yau ba'a gyaraba tunda baizoba babu wani datti, yau kam ban cuci kainaba saida nagama ƙare masa kallo gabas da yamma kudu da arewa, hatta da hotunan saman tebir ɗinsa sai da na gama kalleso, tsabar jan magana irin tawa na zauna saman kujerarsa ina gwada yanda yake zama, nakai kusan mintuna huɗu ina shirirtata kafin kira ya shigo wayar da ya bani, ƙurama wayar ido nayi tamkar mai tsoron ɗauka har sai da ta kusa katsewa sannan na ɗauka nasa a kunne batare da nayi maganaba. Daga canma shiru anƙi cewa komai harna tsahon sakanni.
"Baki iya sallama bane?" muryarsa ta daki kunnena a bazata, idanu na zaro waje dan wlhy banyi zaton shi bane, nace, "Sorry Sir" bai amsa minba sai cewa da yay, ki buɗe ƙaraman drawer na jikin table akwai faran leda da kwali a ciki ki ciroshi" na amsa da "to". Ina ƙoƙarin jawo ledan kwalin ya fita a ciki, hakanne ya sani cirosu ɗai-ɗai shi da ledan, haka kawai na tsinci kaina dason karanta abinda aka rubuta a kwalin, dan da alama na magani ne, shaf na manta da wayar a kunne take bai kasheba, na hau karatun rubutun jikin maganin ina faman zaro idanu saboda fahimtar danai maganin na miye. Daga can Jawaad da yaji a jikinsa akwai abinda ta nutsu takeyi wanda ya ɗaura zarginsa akan maganin cikin sanyin murya yay magana saboda cikinsa dake murɗa masa a lokacin, "Bincike kike mini?" a bazata naji maganar tasa, shiyyasa na saki kwalin ƙasa batare dana shirya ba, cikin rawar baki, nace, "A...a'a sir" shiru Jawaad baice komaiba idanunsa a lumshe yana faman cizon lip ɗinsa na ƙasa, sai da ya lafa masa sannan ya sake maida hankali akan wayar, nikam duk a tsorace nake, gani nake tamkar ya gane mi nakeyi, cigaba yay da lissafo min duk abinda yake buƙata, na sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya jin yabar waccan maganar, na ɗauka kwalin maganin na maida a ledar ina cigaba da ɗaukar duk abinda yace, inda kuma ya faɗa anan nake ganinsa, bayan na haɗasu na zuba a wata leda baƙa na fito.

A ƙasa na iske Nabeelah ta cika tai fam da haushi, taban dariya, hakan yasa na murmusa ina kamo hannunta, ƙwafa tai tace, "ALLAH yayanmun nan ko, saina rama abinda yay min". Nace, "Miyay miki?" ta sake yin ƙwafa, "Bakiga yasa a hanani shiga office ɗinsa ba, ALLAH nima duk randa na fara aiki bazan bari yazomin office ba". Yanzunkam kasa jurewa nai saida na dara, "Oh Nabeelah yaushe ya hanaki shiga Office ɗinsa, jami'anmu dai sun hanaki".
"Kutt wlhy bakisan halinsaba ne, nasan shine yace karsu barni". Nace, "To kiyi haƙuri, Yaya yayi laifi". Tunanin zamu dawo yanzu da oga Jabeer yasa ban shiga ko inaba, Mun isa wajen Gimba ya ɗaukemu muka koma, yanzu kam a falon ƙasa muka iskesu harda su Aliyu, mamaki ƙarara na gani a idanun Rose saboda ganina, a tare na gaishesu gaba ɗayansu na ƙarasa gaban sarakin dake kwance a doguwar kujera, cikin girmamawa na ajiye ledan da keys ɗin da wayar a table ɗin dake gabansa nace, "Gashi". Idanunsa dake rufe ya buɗe ya zubasu a kaina, "Dama tare da Nabeelah na aikeki?" yay maganar yana hararata. Ƙasa nai da idanuna ina girgiza masa kaina alamar a'a. Ƙwafa yay ya ɗauke kansa, ganin hakan yasani barin wajen da nufin bar musu falon ma.
"Waye zai ɗauke miki kayan nan". juyowa nayi, kafin na ƙaraso wajensa Rose dake zaune a kujerar dake inda ƙafafunsa suke ta miƙe ta ɗauki ledan da cewar, "Ƙyale shashasha boss ina za'a kai?". Banza yay bai tanka ba, niko na sake juyawa zan fita. "K! Ina wasa dake ko?". Nazata da Rose ɗin yake hakan yasa nai yunƙuri cigaba da tafiyata Aliyu ya kirani.
"Momi zoki amsa ki kai masa sama kinji". "To" nace, na dawo na miƙama rose dake ɗauke da ledan hannu alamar ta bani, wata banzar harara ta zubamin ta dangwarar da ledar ƙasa ta koma ta zauna, bance da ita uffanba na ɗauka ledar da keys ɗin na nufi sama, dama duk abinnan da ake tuni Nabeelah ta haye tunda muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.
Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, "Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa" dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. "Wai Rose kina nufin sonta yake?". Da sauri tace, "Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa".
Hafiz yace, "Humm" Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, "Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?". Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, "Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun". Cike da jin haushi Hafiz yace, "To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai". Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now