ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce
shafi na goma
...........Wani siririn fito ya saki yana mai kallon kowacce kusurwa ta gidan.
Hakanne ya saka yaransa fahimtar jama'ar gidan ya kema kiranye.
Mai-tawaga, babban yaronsa ne yay magana cikin muryarsa mai kama da ƙattan farkon ƙarni, ga amo gata a matuƙar buɗe.
Kafin kace mi jama'ar gidanmu sun fara yo waje da gudu-gudu.
Muma dai ayari mukabi, duk da Firdausi taso yin tirjiyar ƙin zuwa, sai da inna tai mata magana sannan ta biyo bayanmu dan dole.
Kowa tsaye yay a ƙofar ɗakinsa yana jiran ƙarin bayani, abunda zaisa kaji tausayinmu kuwa hatta da mazan gidan sun koma mata maza, dan kuwa suma sunzo sun jeru a cikinmu, bayan kuma mafi yawansu sun girmi Jazugan, harma da waɗanda zasu iya haihuwarsa.Har yanzu yana a bakin ƙofar tsaye, yana jingine a jikin bango dukkan hannayensa na cikin aljihun wando three queater ɗinsa a zube, rigace armless mai zanen tutar ƙasar Amurika a jikinsa, hakanne yasaka bayyanar ƙaton bandejin da aka naɗe damtsen hannunsa dashi, tabbacin yaji ciwo a wajen kenan.
Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonmu, sai kuma ya fara takowa yana wani rausayar layi irinta marasajin maganar gayu, fito ya fara rairawa yana cigaba da tinkaromu.
A gabana yazo ya tsaya cak.
Wata irin bugawa zuciyata tayi, tare da yin zallo tamkar zata fito, nai wuƙi-wuƙi da idanu kamar an tsamo zomo daga ruwa, addu'ar da nake ƙoƙarin haɗowa a harshena sam ta kasa haɗuwa......
hijjab ɗin dake jikina ya cikuykuye ya maidashi iya wuyana, yakamashi a hannu tamkar zai shaƙeni ya jani zuwa tsakkiyar gidan yana cigaba da fitonsa, Saikace wanda ya sayo akuya a kasuwa.
Duk da bansan warin giyaba inada tabbacin warinta ke tashi a jikinsa.
Yanda jikina ke rawa ina hawaye da ƙoƙarin bashi hakurine ya sashi kallona cikin razanarwa, ya ɗora yatsansa saman bakinsa yana faɗin “Shiiiiii”.
Duk da hawayen basu bar kwaranya ba dole haka na gumtse bakina kuwa.
Ƴan gidanmu duk sun tsorata, innar Firdausi kam ta kasa kallonmu, saima naga kamar kuka takeyi.
Ya gyara tsayuwarsa mai kama da zai ɓalle biyu yana dakama jama'ar gidan tsawa.
“Kowa ya ɗago ya kalleni, dolene yau na nuna muku real jazuuli, ina son ku ɗauki darasi akan wannan mara kunyar yarinyar, yanzu ni har nakai matsayin da zan saka wani aiki a duniyarnan yaƙi min? Wato ɗaga ƙafar da nake mukune har take bama wasu lasisin bijiremin ma........”
“Kai wanenen da baza'a bijire makaba, wawa kawai sauran giya da wiwi, mikake takama dashine shin? Da har kake tunanin sai an bika dole? Ko ka ɗauka tsoronka akeji....”
Firdausi ce a matuƙar hasale take wannan maganar tana nuna Jazuuga, takowa tai inda muke ta fisge hannun Jazuga daga hijjab ɗina a rikice..
Gaba ɗaya jama'ar dake wajen babu wanda bai zaro idanun mamaki ba, sai dai saukar ƙarar marin da ɗaya daga cikin yaran Jazuga suka saukema Firdausi ya kuma sakamu sake firgicewa.
Gaba ɗayansu sukai ribdugu akanta suka hau duka.
Hakan ya sakani fashewa da kuka ni da inna mukayo kansu, amma ni sai Jazuga ya fisgi hannuna ya nufi ɗakinsa dani.
Kuka nake ina tirjewa, shima yana jana a matuƙar fusace.
Ai sai gidan ya kuma ruɗewa da koke-koke.Inaji ina gani ya kaini ɗakinsa, babu ko tausayi ya hankaɗani kan gadonsa, ihu na shiga kwarawa iya ƙarfina, amma babu mai ceto.
Inaji ina gani jazuga ya fara ƙoƙarin shiga mutuncina, UBANGIJI sam bai kasance azzalumin sarkiba, hakanne yasaka kawo wani haske a rayuwata, dan kuwa ina lalubawa sai ga ƙarfen da bansan kona mineneba, jawosa kawai nayi na maka masa akansa.
Wata razanannniyar ƙara mai firgitarwa ya saki, kafin yay luuu zuwa gefe, jini kuwa tuni ya ɓalle har a jikina.Ihun Jazuga ya saka yaransa barin dukan Firdausi data gama fita hayyacinta sukayo cikin ɗakin.
Su duka kansa sukai suna kiran sunansa, da wannan damar nai amfani wajen fitowa da ga ɗakin da gudu, dukkan illahirin jikina rawa yakeyi, dan kuwa nasan tabbas na kasheshi.
Ban saurari dukkan masu min magana ba cikin ƴan gidanmu, dan kuwa hannuna da gaban ƙirjina duk jinine, nasan mafita ɗaya ta ragemin shine nabar gidan. Hakan yasa na zaɓi ficewa ba tare da nasan ina na dosaba.

STAI LEGGENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AzioneTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...