Page 42
..................Inda mai naman nan yake ya tsaya, batare da yayi magana ba ya miƙama mai-naman 1k tare da nuna masa naman. Kallonsa yay a ƙufule, “Haba malam, ya zakazo waje babu ko sallama ka miƙomin dubu wai na baka nama? An faɗa maka ni irin sakarkarun masu saida naman nan ne da kuke rainama hankali, nibanma taɓa ganinka a gidannan ba, kai wane?”. Jay ya danne takaicinsa cikin salon maganar kurame yay masa nuni wai shi bebe ne”. Mai nama yace, “Oh to yanzu naji batu, kasan rainin tsagerun gidannan ne bazan iya ɗaukaba shiyyasa kaima nai zaton kalarsu ne, na duka kake so?”. Kai Jay ya jinjina masa. Mai nama ya fara yankowa yana sawa a takarda da raira ƴar waƙarsa ta shata mai taken “Natsaya ga annabi Muhammadu.......” Jay dai kallonsa yake da nazarin wajen harya kammala yanka masa, amsa yay da masa godiya ya juya zai tafi, sai kuma ya juyo da sauri irin kamar yayi mantuwar nan. Ƴar takarda ya ciro a aljihun wandonsa ya miƙama mai nama. Mai nama ya amsa da faɗin, “Miye kuma wannan? Nifa kunsan ba wani boko nayiba amma kuyitamin wani lagude-laguden jaraba. Kai Hamusu zo duba mi ya keso kuma?”. Wanda aka kira Hamisu dake gaban lemuka ya amsa da “To baba”. Takardar ya amsa ya duba sannan ya kalli mai naman, “Baba wai gidan Ɗan Alhaji ya keson a nuna masa”. Shiru mai naman yay yana kallon Jawaad, mikuma ya tuna oho masa sai ya washe baki, “Af to inaga irin abokansa ne daya ɗan gayyato, kasan yau zaiyi ajo”. Jinjina da hannu Jay yayma Mai nama irin ka gane ɗinan. Mai-nama ya sake washe baki da nunama Jawaad wani gida dake can kusan ƙarshen layin. Cikin alamar maganar kurame yayma Jay yay masa godiya da nufar inda aka nuna masan.
Rufe gidan yake dan haka ya ƙwanƙwasa, sai da yay sau kusan baƙwai sannan akazo aka ɓuɗe cike da masifa.
“Wai wane shegene yake bugama mutane gida haka? Sai kace ya bada ajiya ko an ci masa bashi, idan akai haƙuri dai ai zan fito ba sai ansama lokacina ido b.....” hankaɗa shin da Jawaad yay ya koma baya ya hanashi ƙarasa maganar, zai sake magana Jay ya ɗaura hannunsa saman baki yace, “Shiiiiii”. yana ɗaga rigarsa bindiga ta bayyana, jiki na rawa ɓaleru ya saka hannu ya toshe bakinsa yana faman zare idanu. Ƙofar Jay ya maida ya kulle bayan yay wurgi da ledar naman daya shigo da ita, ya sake kaima ɓaleru wani bahagon bugu tare da damƙo wuyan rigarsa ya miƙar dashi tsaye. Batare da yay magana ba ya nuna masa hanyar cikin gidan. Jikin ɓaleru na rawa ya shiga kaɗa kai tamkar wani ƙadangare.
Gidane madaidai ci yasha tiles har a jikin bango, ga hasken wutar Genretor da alamu suka nuna na gidan drama ɗinne aka jawo masa har nan, ƙofar dake buɗe suka shiga, budurwar dake kwance saman katifa tsirara ta miƙe da sauri zaune tana jan bedsheet ɗin saman katifar ta ƙudundune kanta ciki zata zabga ihu.......
“Idan baki rufemin shegen bakin kiba saina ragargaza ƙasusuwanki wlhy!!”. Jay yay magana cikin kaushin muryar da ta saka budurwar cusama bakinta bedsheet ɗin tana zare idanu hawaye na ƙwarara, jikinta sai rawa yake.
Jawaad ya maida kallonsa ga ɓaleru da duk hankalinsa ke kan wayoyinsu dake zube a ɗan table na glass ƙarami dake gefe. Ƙafa Jawaad yasa ya taɗesa ya faɗi ƙasa tim, cikin zafin nama ya shiga sauke masa maruka a fuska da hannu bibbiyu. A take ji da ganin ɓaleru suka gushe, gashi babu damar yin ihu yana tsoron bindiga. Sai da Jay ya jigatashi da maruka ya tabbatar ya fita hayyacinsa sannan ya barshi. Budurwar daketa gunjun kuka da faman ɓoye fuska ya kalla, “K zoki kashemin duk wayoyin nan....”. Kafinma yakai ƙarshe harta miƙe zaram tana damƙe bedsheet ɗin da ƙyau jikinta na rawa, wayoyin uku manya ta kashe sai ƙarama ɗaya. Yace, “Ina taki?”. Nuna masa ɗaya daga cikin manyan tayi, ukun kuma tace, “N..na nashi ne sauran”. Ɗauke kai Jay yay batare da ya sake cemata uffan ba, ya ɗauki Coc dake ajiye yanata raɓar sanyi ya ɓalle murfin, saman fuskar ɓaleru daya suma ya juyeshi, a take ɓaleru ya kawo numfashi. Wani marin Jay ya sake sauke masa a fuska. Take ya dawo hayyacinsa ya fashe da kuka yana share jinin da yake fita daga hancinsa yana sauka masa kan baki, “Dan ALLAH malam minai maka kake min irin wannan dukan? Idan kuɗi kakeso ko nawane zan baka, nidai karka kasheni dan girman ALLAH, kag.....” sake wanka masa wani marin Jawaad ya ƙarayi tare da ɗora ƙafarsa ɗaya kan katifar ya ranƙwafo kansa da nuna masa fuskar wayarsa. “Wanene wannan?”. Ɓaleru da jikinsa ke rawa ga jini nata fita masa ta hanci da gefen baki yace, “Ni...ni ban sanshi ba wlhy”. “Baka sanshi ba! Kace baka sanshi ba?!!”. “Eh wlhy oga bamma taɓa ganinsa ba”. “Yayi ƙyau” Jay ya faɗa yana miƙewa da tattare hannun rigarsa sosai yay sama. Har Ɓaleru ya fara murna an barsa sai kawai ji yay Jay ya cakumo masa wuya ya miƙar dashi tsaye da ƙyau. Mahaukacin duka ya shiga masa da babu algus, yanda yake bugun nasa zai tabbatar maka zuciyar ƴan mazan a wuya take. Sam baya sauraren roƙon da ɓaleru ke masa da kukan karuwarsa. Saida yay masa lilis sannan ya hankaɗashi ya faɗa saman katifar kansa ya daki bango Ƙummm!!!!. Dafe kan Ɓaleru yay da sakin wata wahalalliyar ƙara, saiga jini sharrrr. Jay ya sake cakumo wuyansa ya shaƙesa da ƙyau da hannu guda, ɗayan kuma ya sake nuna masa hoton Gimba dake tare dashi da suka ɗauka a gidan gonarsa wani zuwa da suka taɓayi tare. Yace, “Har yanzu dai baka sanshin ba?!”. “Dan ALLAH ka tausayamin oga ka daina dukana karka halakani na sanshi, Abokina ne sunanasa Gimba garinmu ɗaya”. Ɗauke fuskarsa Jay ya sakeyi da mari yana faɗin, “Ɗan iska kake son maidanine da?”. “Na tuba dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake maka ƙarya ba”. Miƙewa Jay yay tsaye ya kaima Ɓaleru harbi a ƙafa da tofa masa yawu, sai faman huci yake, jiyake tamkar ya kashe banzan nan ko zaiji sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...