28

12.1K 1K 322
                                        

Page 28

................Alhaji babba ya gyaɗama Jawaad kai alamar eh ita. Cike da mamaki Jay ya ajiye kofin hannunsa yana tsatstsare kakan nasa da idanunsa cike da sonjin ƙarin bayani.
      Murmushi Alhaji Babba yay masa tare da kamo hanunsa, “Daina tsareni da waɗanan idanun naka ba wani abu bameba, kawai inason sanin dangin mahaifinta ne”. Sassanyar ajiyar zuciya Jawaad ya ɗan sauke, kafin shima ya riƙe hanun Alhaji Babba da ƙyau a cikin nashi, “Baba nima inason saninsu, sonake kawai wannan ƙurar ta lafa itama ta sakejin sauƙine”. Alhaji babba yace, “Kayi tunani mai ƙyau, inason kayi ƙoƙari ka bincika, sannan yaya maganarka da mutanen gidanku? Da kuma maganar shi wanda kasa ya auri yarinyarnan ta wajen Ali?”.
     Murmushi Jawaad ya ɗanyi ya ɗauki furarsa zai cigaba da sha, ganin zai basar da zance Alhaji babba yace, “Nasanfa ka jini”. Ƴar dariya Jay yayi yakai kofin bakinsa, “ALLAH ka iya rigima kaima tsohon nan, karka damu ina sane da komai”. “Nasan kana sane da komai Muhammad, sai dai hankalina ya tashi matuƙa jin ba mutumin kirki bane habibun, kajifa wani suna da Nasiru ya kirashi dashi ranar”.
          Jay yay murmushi kawai batare da yace komaiba.

        Sun cigaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara ya fita, yaso zuwa asibiti, amma ganin dare yayi sai ya haƙura ya nufi gida abinsa. A gate ya tsaya ya tambayi mai-gadi ko gimban ya dawo?. mai-gadi ya tabbatar masa da bai dawoba, ya kira wayarsa kuma gashi tana ring amma ba'a ɗagaba.
      Sosai abin ya ɗaurema Jawaad kai, daga baya kuma ya ajiye tunaninsa akan inhar da safe bai dawoba zaisa abi bayansa garin nasu aga ko lafiya?. Da wannan tunanin yay shirin barci ya kwanta.

_____________________________________

             Su Dady sun karɓi baƙuncin surikinsu habib, duk yanda Dad yaso su Momy su zauna basai sunzo falon baƙiba hakan ya gagara, dole ya barsu sukabi bayansa, ba ƙaramin tashin hankali Shahudah ta shigaba da ganin wanda ake kira wai matsayin mijinta, daka gansa kaga cikakken tantiri marajin magana, cike da isa ya zauna a kujerar da aka nuna masa sai wani cika yake da batsewa.
        Ya kafe Aamilah da Shahudah da kallo yana wani lasar laɓɓa tamkar tsohon maye, ko kunyar su Dad bayaji, dama daya shigo babu wanda ya gaida, bama su ishesa kallon arziƙiba.
      “Wace cikar tawa anan?” yay maganar cike da gadara. Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, sai Shahudah da Aamilah da suka zuba masa wata shegiyar harara. Ya bushe da dariyarsa mara daɗin ji yana faɗin,  “Dama ace ana auren yaya da ƙanwa wlhy da duk haɗawa zanyi hhhhh! Dana kwashi gara aradu...” cike da tsiwa Aamilah da tafi Shahudah jin hausa tace, “Uwarkane garan shege mai suffan aljanu.....” wata wuta data gitta ta idanunta mai stars ce ta hanata kaiwa ƙarshe, lokaci ɗaya jinta da ganinta ya ɗauke baki ɗaya ta zube a jikin Dad daya tarota. Babu wanda yaga sanda Ɗan-fir'auna ya ƙarasa gaban Aamilah sai ƙarar maruka sukaji kawai.
     A fusace Dad yace, “Kai ƙaramin ɗan tsagera, wanene ubanka da har zaka mararmin yarinya a gabana?”. Kallon dad ɗan fir'auna yay ya watsar, kafin cike da gadara yace, “Sanin ubana a gareka dattijo ai tamkar yankewar numfashinka ne, dama kun kiranine domin kuci zarafina komi? kunga dalla malamai ku bani matata na wuce na fasa zaman....” da sauri Uncle Uwaisu ya taresa cikin lallashi yana bashi haƙuri, amma fir ƴaki sauraren kowa, Aamilah dai ta farfaɗo da ƙyar bayan an zuba mata ruwa, Shahudah na rakuɓe lungun kujera sai tsiyayar da hawaye takeyi jiki na rawa, harga ALLAH tsoronsa takeji, a ranta kuwa ayyanawa take ashe Bilkisu baturiyace, dan ɗan-fir'auna ALLAH ya bashi baƙi, wanda daga gani kasan shaye-shaye ya sake taka rawar gani wajen ƙara masa shi. Da ƙyar suka samu ɗan-fir'auna ya zauna bayan an saka Shahudah da Aamilah sunbar falon, Salman kam yay laƙe kamar baya falon (hege yaga maza🤣😜).
          Duk yanda su Uncle Nasir sukaso lallaɓa ɗan-fir'auna akan ya saki Shahudah yace shifa sam baisan wannan zanceba, dan yanzuma da shirin ɗaukar matarsa yazo yana buƙatar abinsa, tunda yana zamansa aka kawo masa tallansu. Har ƙasa Momy ta duƙa tana kuka da roƙonsa amma sai dariyar wulaƙanci da cusa haushi yake musu.
        “Kungafa kubar ɓata lokacinku akan roƙonama, tayaya kuke tunanin zanyi sake da wannan babbar kaddarar ne haka, yo ko shugaban ƙasa ai nafishi hura hanci yanzu akan wannan cikar tawa, ku manta kawai a saimin royal bed zan kama hayar gida aje aimin jere gobe, babu damuwa idanma kunkai sati danshi shiri wuyane dashi, ko a hotel mayi amarcin satin guda kafin ku kammala surukai..” ya ƙare maganar da miƙewa yay salute nasu zai fice. Da sauri Dad yace, “Nawa kake buƙata a biyaka ka sakarmin yarinya?”.
      Tsayawa ɗan-fir'auna yayi, ya juyo yanama Dad wani matsiyacin kallo maiban tsoro, sai kuma ya bushe da dariya tare da dawowa da baya. Yace, “Zan iya amsar kuɗi na saketa pale, tunda yanzu na auri ƴarka ka zama pale ɗina nima, ammafa kasani saina ɗanɗana kona sati ɗayane dan yawuna ya biya, a shiryata da safe nazo na amshi kayata, nanda sati biyu saiku cakemin naira miliyan hansin na baku ƴarku, idan haka bai mukuba kuma banida matsala, iyakaci inta mata ciki duk bayan wata tara ta ringa juyen jajayen ƴan dugwi-dugwi irinta, koba komai na samu surukai masu kuɗi nima nan gaba tunda naga jar fatar ake yayi yanzun” ya wani ɗage musu gira cike da barikanci yay ficewarsa.
           Babu wanda bai jiƙe da zufaba a falon, tun fitar ɗan-fir'auna babu wanda ya iya magana sai kuka Momy dake tashi. Salman ya miƙe cikin raɗa-raɗa yace, “Wlhy kuyi ƙoƙari ku biyashi, dan wannan dagani zai iya take mutum ya yanka tamkar ya yanka kazar gidan gona, ku rufa mana asiri dad dan kuwa su momy sun kwaso mana bala'i, wlhy barin ƙasarnan zanyi idan an gama watandarku na dawo zaman gaisuwa”. Ya ƙare maganar da ɗai-ɗai yana kallon ƙofa, da gani kasan a tsorace yake (Kana bani yaji Salman🤣, lusarin banza😠).

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now