Page 16
...............Napep na samu na tare nai tafiyata gidan Inna zainabu. Can nai zamana mukasha hira da Lawusa da a yanzu muke ɗasawa har bayan sallar isha'i sannan na nufo gida.
★★★★★
Bayan an buɗe taro da addu'a Uncle Nasir ya fara jawabi kamar haka. “Kamar yanda kowa ya sani mun fara tattaunawa akan maganar zaman Jawaad babu aure a kwanakin baya, har takai mukai masa tayin cikin yaran gidannan ko akwai wadda ya keso, sai dai ya nuna a lokacin zaiyi tunani, tun daga wancan lokacin ban sakeji daga gareshiba, to magana ta gaskiya mun gaji da ganinsa yana yawo a gari haka ana zaginmu, shi kansa bama girmansa bane, ƙannen-ƙannen bayansa ma gasunan duk da iyalansu har da ƴaƴa, yakamata Jawaad kaima kanka faɗa, dan lokaci bawai zai zauna jiranka baneba, kai kaɗai Abdul-aziz ya haifa, zamuso ganin ƴaƴanka a duniya kamar yanda mukasan da yanada rai zai ɗokantu da haka shima. A wannan karon ba shawara muke bakaba, umarnine, shiyyasama mukazo da Alhaji Baba domin ya zama shaida, tare da iyayenka, dolene a wannan karon kayi aure, ka zaɓi mace ɗaya a cikin ƴaƴan gidannan koma fiye da ɗayar mukuma zamu aura maka”.
Jawaad da kansa ke ƙasa yay guntun murmushi domin son ɓoye ɓacin ransa, batare da ya ɗagoba yace, “Uncle ku gafarceni, bazan jaku da nisaba, duk cikin yaran gidannan bazan iya auren kowaba, dan kallon ƙannena nake musu tamkar ciki ɗaya...” da sauri Uncle Uwaisu yace, “Ai tamkar kace, bawai hakan bane, tunda babu ta inda ALLAH ya haramta maka, Jawaad bamason shirme, garama ka zaɓa komu mu zaɓa maka, kokuma ka ɗauki zaɓi na biyu, wato ka maida matarka ɗakinta kuje kuyi haƙuru da juna tunda yarinyarnan ta horu kuma tana sonka”. Yanzu kam kasa daurewa yay saida ya ɗago kansa ya kalli Uncle Uwaisu, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda gargaɗi da Alhaji Baba yay masa da ido, kansa ya maida ƙasa yana sauke ajiyar zuciya.
Uncle Sulaiman yace, “Son!” ɗago kai Jawaad yay ya kalli Uncle ɗin nasa da yake matuƙar so saboda ƙyawun halinsa, yace, “Na'am Uncle”. “Ko Kanada wadda kake sone?”. Ƙasa Jay ya maida kansa yana motsa laɓɓansa, sai dai babu maijin mi yake cewa, Uncle Taheer ya katsesa da faɗin, “Kai muke saurare Jawaad”. Batare daya ɗagoba ya girgiza musu kai alamar a'a. Shiru falon ya ɗauka kowa ya zuba masa idonu, shi kuma yaƙi kallonsu. Mama Zuhurah da bata da yawan magana tace, “To Jawaad ya kakeso ayi kenan? Yanzu kai kafijin daɗin kullum aita zaman meeting akanka akan maganar kaƙi aure, ka rufa mana asiri ka fidda kanka damu iyayenka daga zargi da zunɗen al'umma kaji, ƴar uwarka na sonka, tayi nadamar kuskuren datai a baya, kayi haƙuri a maida aurenku kaji”.
Ɗagowa yay zaiyi magana fitowar Shahudah ta katse masa hanzari, gabansa taje ta durƙusa tamkar yanda Mama Atika da Mom suka kitsa mata, ta fashe da kuka tare da kama ƙafafunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta da harshen turancin da tafi ƙwarewa ya cinye tace, “Bb dan ALLAH ka gafarceni, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, nakumayi alƙawrin bazan sakeba, na yarda zan haihu maka yara komai yawan da kake buƙata yanzun, idan ka barni mutuwa zanyi wlhy, dan ALLAH ka ceci rayuwata Bb...” hannunta ya ture daga saman ƙafarsa yana hararta, “Kima daina ɓata lokacinki, indai haihuwace bana buƙata daga gareki Hudah, karki damu kije kicigaba da cin moriyar ƙuruciyarki kinji, indai nine kima saka a ranki baki taɓa sanin mai kama daniba dan mun rabu kenan”. Fashewa tai da matsanancin kuka yanzunkam fiye da da, dan har ƙasan ranta kalamansa sun masifar sosa mata zuciya, ta dafe kanta dake juya mata, babu zato sai kawai ganinta ƙasa sukai ta yanke jiki ta faɗi. Gaba ɗaya ƴan falon da suka zuba musu ido suka miƙe, shi kansa Jawaad ɗin kallonta yake, dan ya zata salon iskancinta ne, sai daga baya da aketa jijjigata babu alamar rai tattare da itane ya fuskanci babu wasa a lamarinta, gaba ɗaya falon ya rikice, dan iya ƙoƙari anyi Shahudah taƙi farfaɗowa, Mom sai kuka take da sambatu.
Dole aka kwashi Shahudah zuwa asibiti da gaggawa kuwa, dan wasunsu harsu fidda ran da gaske ta mutu.★★★★★★★
Tun a gate baba maigadi yake sanarmin ai babu kowa a gidan duk suna asibiti aunty Shahudah babu lafiya, hankalina ya tashi sosai, dan haka nai azamar tsayar da mai napep ɗin dake shirin juyawa dan harma ya fara tafiya, shiga nayi na sanar masa asibitin da baba magadi ya sanarmin an kaita. Asibitine mai ƙyau dan na kuɗine, kasancewar bansan ina zan nufaba sai nai kiran aunty Aamilah, saidai bata amsa ba, na sake kira nanma babu amsa, maida kiran nai kan Yah Qaseem, sai da ta kusan tsinkewa sannan ya ɗaga, faɗa masa nai gani a asibitin a ina suke?. Muryarsa a sanyaye yace na jirasa yazo ya shiga dani.
A yanda na gansa kawai na tabbatar akwai babbar damuwa dangane da aunty Shahudah, kasa daurewa nai na shiga jera masa tambayoyi. Amsa ɗaya na samu daga garesa, shine ta farfaɗo, sai dai sun mata allurar barci, sun kuma hana kowa ganinta sai banzan Jawaad ɗin da taketa sambatun kira. Ta bani tausayi matuƙa, dan na sake fahimtar tsananin son da takema Boss.
Duk sai da na gaida waɗanda na tarar a wajen, sannan na tambayesu ya mai jiki, sai dai babu Boss babu dalilinsa a wajen, zama nai kamar yanda suke zaune jigum-jigum, kusan mintuna biyar sai naji ƙamshin turarensa. Ɗago kai nai dan tabbatarwa, karaf kuwa muka haɗa ido dashi, ya dalla mani harara sannan ya ɗauke kansa tamkar baiyiba. Nima janye nawa nai, dan nasan laifina dai bai wuce tafiya bada izininsa ba. Cikin nutsatstsiyar muryarsa dake tattare da alamun gajiya naji yana faɗima Uncles nasa da matansu ya kamata su tafi gida su huta, tunda dai Doctor yace bazasu bari a gantaba har sai zuwa safiya.
Cike da nazari nake satar kallon yanda wasu suke masa kallon harara dajin haushi a kaikaice, amma a zahiri suna amsashi cike da kulawa, sai al'amarin nasu yay masifar ɗaure min kaina, to amma abinda babu ruwanka ai daɗin kallo garesa, dan haka nai ƙasa da kaina kawai ina sauraren mahawarar da suke akan wanda zai zauna ya kwana, ance Mom taje gida Aamilah ta zauna, sai dai ita aunty Aamilah ta tubure akan tsoro takeji ta kwana asibiti, da sauri Salman yace, “Kedai wawuyace Aamilah, to sai wannan yarinyar tazauna ku kwana ai”. Yay maganar yana nunanu. Da sauri Yah Qaseem yace, “Itakuma aikin tafa? Itadai Aamilah da babu inda take zuwa itace ta cancanci kwana da itan”. Shiru kowa yay, sai kuma daga baya wasu sukai na'am da batun Yah Qaseem ɗin, na saci kallon Boss da uffan baiceba, yama ɗauke kansa daga garemu tamkar baisan mimukeyiba, nikam lamarinsa kan bani mamaki wani lokacin gaskiya.
Wata mata da nake ƙyautata zaton cikin matan Uncles ɗin nasune ta kawo shawaran haɗa Aunty Aamilah da ɗaya daga cikin yaran gidansu ɗin da wata dattijuwar mai aiki, akan wannan shawarar aka zauna, dan haka duk sai muka fara shirin tafiya. Har mun fito baki ɗaya Mom tace gaskiya bazata iya tafiyaba, itama anan zata kwana, duk kallonta mukai da mamaki, sai kuma naga tsoro akan fuskokin wasu, dan koni naji wani iri saboda ganin Mom na sharar ƙwalla, nasan yanda ƴan gidanmu ke masifar son aunty Shahudah, hakan ya samo asaline saboda so mai tsanani da Dad ke nunamata kasancewar sunan Mahaifiyarsa taci, sai naji a raina kamar zamu iya rasa aunty Shahudah, duk yanda aka lallashi Mom taƙi aminta da hakan, sai kawai aka barta. jinai wani iri, dan tundafa Mom zata zauna nikaɗaice mace zan kwana a gidan, nima da sauri nace to zan zauna a asibitin, da sassafe sai naje gida.
Harara Yah Qaseem ya dallamin da cewar bazan zaunaba gida zani. Niko na fara roƙonsa akan ya barni, shikuma yaƙi saurarena, kowa kuma yaƙi saka mana baki. Na kalli inda Boss yake tsaye a jikin mota hawaye na gangaromin akan fuska, sarai nasan duk yanajinmu, amma yayi kunnen uwar shegu da kowa, harna yanke ƙauna daga taimakon kowa na tsinkayi muryarsa yana faɗin,
“Ita Aamilah ta fito ku wuce gidan tare mana, dan sunmayi yawa anan tunda Mom zata zauna, na tabbata sai ma'aikatan asibitin sunyi ƙorafi”. Harararsa Yah Qaseem yayi, sai dai baiyi maganaba.
Uncle Nasir ne yay na'am da shawarar Jawaad, dan haka ya aika aka kira Aamilah. Naji daɗin hakan da samun nutsuwa sosai. Daɗin da najine ya sakani matsawa inda yake nace, “Thanks you Sir”. Banza yaymin tamkar bai jiniba, sai daƙilar waya yake abinsa, na ɗaga ƙafafuna zanbar wajen naji yace, “Uhm”. Kallonsa kawai nai sau ɗaya nabar wajen zuwa motar Yah Qaseem daketa antayomin harara tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa.

VOCÊ ESTÁ LENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AçãoTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...