Shafi na ashirin da takwas
https://youtu.be/HFjVgQVnmn0
MANHA HAUSA NOVEL'S👆🏻
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
✍🏻ALƘALAMI TV👆🏻
Please and Please my dear fans, wannan sune chennals namu a taimaka dan ALLAH aje ai mana subscribing, zasu dinga kawo muku daɗaɗan novels namu babu ko sisinku, ga abubuwan gyaran jiki da ƙaruwa ta fannoni da dama, dan ALLAH a daure a nuna hallaci, hakan zai sake ƙaramin ƙwarin gwiwar baku ƙwai cikin ƙaya a kullum, dan zai tabbatar min kuna biye dani, kuma kuna sona har yanzu, dan ALLAH kar ayi sanya, a danna mana subscribe, idan liks ɗin baya nunawa kuyi Searching ɗinsu ta Accaunt ɗin youtobe zasu nuna muku Please & Please😢🙏🏻🥰🥰💃🏻__________________________
*_BAYAN SATI UKU_*
_BILKEESU_............Babu abinda zancema Ubangijina sai godiya, domin kuwa jarabawa na tafiya yanda ya kamata, sai dai ƴan ƙalubale da ba'a rasaba, a yanzu haka abinda ya rage mana bai wuce sati ɗaya ba kacal mu kammala, muɗanyi hutun sati biyu daga nan muyi neco.
Gaba ɗayanmu mun maida hankali, sannan muna taimakon juna, musamman ma ni da suke taimakawa ta kowanne fani.
Yau ma mun fito a gajiye, kowa sai yaƙe yake saboda yunwar dake cin hanjin cikinmu, hostel muka nufa kamar waɗanda aka zanema ƙafafu.
Ummie tace, “Ni yanzuma bama kaje ɗakinba, ka rasa abinda zakaci shine matsalar”.
Rebecca tai dariya da faɗin, “Kina nufin yau ma bazakici abincin da akai ba?”.
“Wlhy bazan ciba, nifa badan kun hananiba da tuni na daɗe da kai report ɗin abinda na gani jiyan nan, ai insha ALLAHU daga jiya harna bar skull ɗinnan bazan sake cin abincin da akai a kitchen ba”.
Dariya duk muka saka mata.
Nace, “Haba ta wajena ki ɗan sassuta, daga jiya kin gani sai kuma akace shikenan kullum za'a cigaba da gani, wannan ɗinma nasan by mistake ya shiga ALLAH”.
Nazifa dake gefena tai saurin faɗin, “Barta Bily, kartaci, wlhy yunwar cikintama ta isheta, ita ɗinnan mayyar son cin doya, duk randa akayi zamuga bazataje ta amso ba da gaske?”.
Ummie ta harari Nazifa tana faɗin, “To ƴar sa ido, duk bin ƙwaƙwƙwafinki ƙyayi ki barni, dan zan tabbatar muku da maganata”.
“ALLAH ya bada iko” cewar Zuhrah.
Duk muka amsa da amin muna dariya, da haka muka ƙarasa hostel.
Sheƙawa da gudu Zuhrah tayi ta fara shiga ɗakinmu tana faɗin, “Nizan fara wanka ehe”.
Ƙarasa shiga muma mukai, Nace, “Kai Zuhraty kin sanfa yanda nake, Please ki barni na fara”.
Shigewarta tai da sauri tana min gwalo, “Ai dama saboda ke ne zanyi fes ɗin, karda ki gogamin nima na ɓule yau”.
“Zaki sani ai, insha ALLAHU gobe sai muna tsaka da jarabawa kiji ya zubo....”
“Wlhy ke muguwace Bily” cewar Rebecca dake cire kayanta, Nazifa da Ummie kuma suka saka dariya.Haka muke a koda yaushe cikin nishaɗi da kulawa, nakanji tamkar na ɗauki wasu shekaru masu yawa tare dasu ne, dan wanda bai saniba ya gammu zaiyi tunanin tun yarinta muke a haka, ba ƙaramin sakin jiki nayi dasuba suma kuma hakan, idan kaga faɗa a tsakaninmu sai dai rashin fahimta, mukan zauna kuma mu warware da wuri kafin abun yay mana tsamari, Nazifa ma tuni ta fara sakin jiki dani, duk da dai ba kamar su Ummie ba hakan bai dameni ba.
Sai da duk mukai wankan sannan mukaje muka amso abinci, amma banda Ummie datai alƙawarin tabarci har ta wuce.
Irin wannan farin cikin dana samu daga garesune ya sake kawoma rayuwata canji da farin ciki, jikina ya murje tamkar ba'a makaranta nakeba, duk da babu wanda ya taɓa busting ɗina hakan baisa naji ɓacin raiba, amma dai ina kewarsu su duka.
A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi mun kammala waec, a ɗan hutun da muka samu kafin fara neco ne ya sakamu sake komawa kan karatun rayuwa.
Dan kuwa ƙawayena sun sake buɗe mun wasu shafukan koyan salo-salo dake maida mace mai aji da tsaftatacciyar wayewa, niko na nutsu wajen bin komai daki-daki ina haddacewa......

VOUS LISEZ
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...