Bilyn Abdull ce🤙🏻Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️.
Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum), alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci.😘👌🏻
_____________________________________
BOOK ONE
Shafi na biyu
_____________________________________............Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan mutane, gata fara tas tamkar wata aljana.
Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da niyyar tashi ma.
Kusan mintuna arba'in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen kumatunsa.
Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi.
Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya can ƙasan maƙoshi yace, "Kinyi salla?".
Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, "Haba bb, kamun laifi maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya".
Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji daɗinsa sosai gaskiya.
Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba tana yaye bargon da take ciki.
Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata yafi kama da na masu jajayen kunnuwa.....
Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa.
Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba.
Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita.
Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, "Saura idan kinje canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar".
Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take faɗa.
Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi.
Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH....
A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa.
![](https://img.wattpad.com/cover/220260947-288-k27914.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AçãoTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...