34

12.1K 1.1K 272
                                    

Page 34

...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki kinji”. Jikina har rawa yake  saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”. Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina, “Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi, tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
         Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa, babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci, bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma yasin😤).
          Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
     Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin “Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
           Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, duk ƙawayena sun zama nasu suma.
            Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora