_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿♀️🙋🏿♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._
_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._
_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_
_1_
_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_
_2_
_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_
_3_
_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_
_4_
_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_
_5_
_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_
_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_
Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,
Guda hudu 4 Kuma 500,
Guda uku 3 Kuma 450,
Guda biyu 2 Kuma 400,
Guda daya akan 300.
Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*+234 903 234 5899*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
*09033181070*
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALOTEAM#ZAFAFABIYAR🔥
Page 60
...............Umm-Anum na kuka tana dariya duk a lokaci ɗaya ta nuna tv'n da yatsanta manuniya, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu. Kowa ya gagara cewa komai sai kallonta kawai da suke. Ta share hawayen da suka gama wanke mata fuska tana kallon Ummah babba. “Mariya a kaini wajen baba”. Da ƙyar Ummah babba ta iya gyaɗa mata kai a hankali. Bata ƙara cewa komaiba ta gyara mayafin jallabiyar ta data naɗa tamkar yanda larabawan Saudia keyi, Batool ta ɗakko mata takalmanta zuwa gabanta, dafa Batool ɗin tayi ta saka dan ƙafarta ciwo take mata kaɗan-kaɗan, tun jiya bata gama saki ba har yanzun.
ta maida dubanta ga su Uncle Sulaiman dake tsaye tamkar sojoji, har yanzu babu wanda ya iya gaskata ruɗani da al'ajabin da idanunsu ke gani a zahiri da magiji. Hannayenta🙏🏻 ta haɗe waje guda tana ɗan murmushi, “Ku gafarceni, ganin Mahaifina a yanzu gareni yanada matuƙar muhimmanci”. Bata jira amsarsu ba ta raɓasu ta wuce abinta Batool da Anum da Nabeelah sukabi bayanta.
Da kallo suka bita tamkar wasu wawaye harta fice ita da zugarta. Ummah ƙarama da babba suma sukai yunƙurin bin bayansu. Uncle Sulaiman ne ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki da rawar murya yace, “Hajiya Mariya a ina kuka samu Bilkisu? Tun tsahon wane lokaci kuma?”. Kanta ta girgiza masa tana share guntun hawayenta itama, “Bani da ikon amsa waɗan nan tambayoyin Alhaji Sulaiman, inaga mu bari har sai lokacin da Yayah taso hakan da kanta, na tabbata zatazo ta sameku har gida insha ALLAHU. Mun barku lafiya”. Ta ƙare maganar da kama hannun Ummah ƙarama suka fice suma.
“Uncle wacece ita ɗin wai?”. Shahudah da idanunta ke lullumshewa saboda hajijiyar da take gani ta tsananin tashin hankali ta faɗa tana dafe bango. Saurin ruƙota matar Uncle Sadiq tayi jikinta na rawa itama. “Shahudah!!” ta faɗa daɗan ƙarfi ganin jikin Shahudah ya fara saki alamar neman suma takeyi itama. Ruɗewa ɗakin ya ƙarayi, masu share hawaye suka ƙara ƙarfafa kukansu da sauti, yayinda wasu suke zubewa ƙasa daɓar tsabar shiga ruɗani da abinda ake nunawa har yanzu daga gidan tv.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...