Page 53
.................Bayanan da Dattijon nan na tashar garinsu gimba ya kawo masa yay dai-dai da dukkanin hasashen Jay, abin sosai ya ƙara bashi mamaki da tsoro, babban mamakin shine minene alaƙar Hajiya Safara'u (Maman yara) da gidan Alhaji kokino tunda a gidansu ta fara aiki? Sannan minene dalilin da yasa ta turo masa gimba?. Bibiyar rayuwarsa take bisa umarnin wasu ko kuwa umarnin kanta ne?. Malam shehu shine ya haɗashi da gimba lokacin yana neman driver, dan malam shehun shine drivern da aka fara nemo masa kasancewar shi mutumne da baison tuƙi, kasancewar ya gansa babba yace a canja masa da yaro, dan bayason yaga babban mutum mai shekaru kamar na mahaifinsa ace yana aiki a ƙarƙashinsa gudun watarana kar wani dalilin ɓacin rai ya shigo ya aikata abinda bai daceba a garesa. Haka malam shehu ya kawo masa gimba a cewarsa ɗan garinsu ne, shikuma sai ya samawa malam shehu wani aikin a gidan gonarsa wanda bazai wahala ba, to a yanzu dai shekarun malam shehu kusan huɗu kenan da rasuwa, dan shekara uku da wasu watanni kaɗai yay yana aiki a gidan gonar ALLAH yay masa rasuwa dama yana da hanta.
Hannun da ya tallafe kansa da shi ya janye yana furzar da huci. Yanzu idan yace zaije garin su gimba yamma tayi, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yaɗan lumshe idanu, lokacin ma tashi yayi, yanason su wuce gida da wuri kodan Bilkisu, ga kuma aikin da yake son suyi ma a gidan. Yaɗan fara tattare kayansa akai knocking ƙofar. Batare da ya kalli wanene ba ya bada izinin shigowa.
Ƙamshin turarenta da yajine ya sakashi ɗagowa ya kalli ƙofar, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci a matuƙar gajiye take, ya ɗauke idanunsa yana murmushi a ransa. Takardun hannunta ta ajiye bisa tebirin nasa tana faɗin, “Barka da yamma Sir”. “Yarinyar nan kin fara rainani wlhy” ya faɗa yana tura takardun daya haɗe cikin briefcase ɗinsa.
Bily dake ɗan murmushi tace, “Rufamin asiri, ina ni ina raina shugabana”. Baice komai ba ya ɗauki takardun data ajiye ɗin, “Na minene?”. “Oga Hafeez ne yace na kawo maka ka saka hannu, yace dan ALLAH yanzun”. Rufe file ɗin yay ya ture gefe, “Ku wlhy ku barni na gaji, sai dai ya bari sai idan ALLAH ya kaimu gobe danni kam nama tashi”. Agogon hannuna na kalla sannan na kallesa, biyar da minti tara fa”. “Koma babu minti tara ne bazanyi ba, kije ki shirya mu wuce, idan kuma na barki anan to?”. Ɓata fuska nai batare dana ce da shi komai ba na juya zan fita, harna kama ƙofar zan buɗe na tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Habawa yarinya badai gida zamu ba, zakiyi min bayani ai”. Idanu na lumshe da buɗewa a lokaci guda, kafin naɗan juya na kallesa, “To nama fasa binka, gidan Ummah zanje na kwana”. Da hanzari na buɗe ƙofar na fice ganin ya taso, sai da na tabbatar na sauka ƙasa sannan na dafe ƙirjina dake bugawa da sauri-sauri ina murmushi, juyawa nai na kalli saman sannan nabar wajen zuwa office ɗin oga Hafiz dan na sanar masa abinda yace.
★★★★★★★★Muna shigowa gida ana kiran sallar magriba, ɗakinsa ya nufa nima na nufi nawa, wanka na farayi sannan nai sallar magriba, bayan na idan na zura doguwar riga kawai na fito, kitchen na nufa dan na duba abinda zan samar mana muci kasancewar ya faɗamin Sadiq yayo cefane da rana. Ina fara ƙoƙarin ɗaura abu mai sauƙi da bazai takura mana ba ya shigo kicin ɗin, kallonsa nai da masa sannu, ya amsa yana mai kallon agogon hannunsa, “Miemaa bara naje yarinyar nan ta kirani inaga an dace”. Nace, “To ALLAH ya tabbatar da hakan, sai ka dawo”. Matsowa yay ya sumbaci goshina da faɗin “Amin nagode, sai na dawo”. “ALLAH ya tsare” na ƙara faɗa ina maida hankalina ga aikina shi kuma ya fice.
Dawowarmu gidan sai tunanin ganin wallet ɗin ɗazun ta sake dawomin cikin rai, ina aiki ina sake juya al'amarin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dan danan na kammala, na tanaji abinda zamuyi breakfast da shi dana tashi sai haɗawa. Shirya namu abincin nai a dining na saka hijjab na fita na kaima maigadi nashi. Sannan na dawo nai sallar isha'i, na gaji hutu kawai nake buƙata, amma yaya na iya, gaskiya a kwai wahala ga mace mai aure ace kuma tana aiki, yanzu mu biyu ne kawai fa, to inaga nan gaba ƴaƴa sun ƙaru kuma fa? Mace daban ce a rayuwa, na tabbatar ba kowanne namiji bane zai iya juriyar da mu mata mukeyi wlhy, ki duba dasun dawo aiki wanka kawai zasuyi suci abinci su huta, mace ko kota dawo ɗin wani sabon aikinma zata taras, harma shi kansa ya ƙara mata da wani a bayan fage, hakan kuma bazai hanata tayi sammakon tashi ba da safe. (Mata kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban aduk lungu da saƙo na duniya, ALLAH ya ƙara muku martaba da kwanciyar hankali a duk duniyar da kuke. “Maza banda jealous kuma👻dan gaskiya na faɗa🙈”. lol😂).
Bai shigo gidan ba har tara saura, lokacin harma naɗanyi barcin wasu mintuna a falon. Jin ana shafa min kai na buɗe idanuna a hankali, cikin nasa suka shige, yana tsugunne gaban kujerar da nake kwance, hannunsa ɗaya a sumar kaina ɗaya ya riƙe hannuna dana ɗaura saman ciki yana murzashi. Murmushi yay min nima na maida masa murtani, cikin muryata da taɗan sirka nace, “Sannu da dawowa”. Kansa ya ɗagamin yana mai lumshe idanusa, kafin ya tura yatsunsa cikin gashin kaina da faɗin, “Ya kamata aima kan nan kitso Zinaraina, kar yazo ya lalace aimin asara”. Na ɗan jinjina kaina ina murmushi da yunƙurawa zan tashi, taimakamin yay na tashi zaune sosai, sai da na zauna da ƙyau sannan nace, “An dace?”. Ni kaina yanda nai maganar cikin kalar tausayi sai da na bama kaina dariya, yay murmushi shima yana miƙewa tsaye da zama a kusa dani, “Idan kika koma kalar tausayi sai ki zama wata saliha dake”. “Lah!, to ni ina da tsiwane?”. “Eh mana, sai mutum ya zauna dake yake ganewa ai, a nesa ba'a gane Fitsararriyace”. Nace, “ALLAH kana gani”. “Nima ALLAH kana gani” ya faɗa da dungure kaina da ɗoramin ƴar ƙaramar jikka saman cinyata. leƙa jikkar nai, ganin wayoyi huɗu a ciki ya sakani jin wani ɗanyan farin ciki, bansan sanda na rungumesa ba ina dariyar jin daɗi. Shima rungumeni yay yana dariyar. Ɗagowa nai da sauri, cike da farin ciki nace, “Kai amma tayi ƙoƙari wlhy, yaya akai ta samo mana?”. “Ai dama nasan zata ɗakkosu, yanda yarinyar nan ta mutu a kaina ko Alhaji kokinon nace ta sato ai zata sato min”. “Uban nata?”. “Sa wasa yarinya, nifa nan farin jinine dani garama ki ringa lallaɓani”. Yay maganar yana miƙewa, sai da yaje dining sannan ya juyi ya kalleni, “ƴammata ko dai kina jealous ne?”. Baki na taɓe ina miƙewa nima bayan na maida wayoyin a jikkar. Ganin na basar shima sai ya basar da zancen.

ŞİMDİ OKUDUĞUN
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AksiyonTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...