Page 35
.................Rintse idanuna nai da azabar ƙarfi, a duk lokacin da jikinsa ya taɓa nawa nakanji tamkar na taɓa wuta, daga randa mukaje ɗakko gawar Gimba kuma sai na rage jin hakan, sai dai sam banason yace zai taɓani, amma a mamakina yau sai naji tamkar an azani bisa wutar. A take jikina ya fara karkarwa saboda azabar da nakeji, cikin gangarowar hawaye bisa idanuna nace, “Boss dan ALLAH ka matsa, wlhy jikinka tamkar wuta nake jinsa”.
Yanda ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana neman silalewa ƙasa yasaka Jay ja baya cikin ɓacin rai, dan shi kalamanta zafi sukai masa a zuciya, cikin kaushin murya yace, “Qaseem ne kawai idan ya taɓaki baƙyajin zafi tunda shi kikeso?”. Idanuna na shiga lumshewa ga zufa sai karyomin take a jiki saboda azabar da nakeji, na shiga girgiza masa kawai, “Kaimin addu'a, fatar jikina jinake tamkar ana ɗayemin itane”. Yanzu kam da mamaki yake kallonta, dan yanda jikinta ke wani irin karkarwa da zufar da takeyi ta cancanci a fahimceta, kalaman baba ƙaurane suka faɗo masa cikin rai, addu'ar ya shiga karantowa yana tofa mata, idanunsa harsun ƙaɗa sunyi jazur saboda yanda yakeji a cikin ransa, gaba ɗaya yakan rasa wane tunani zaiyi akan lamarinnan, idan ya zurfafa tunaninma sai kiji kansa ya fara matsanancin ciwo, dole yake ajiye batun ya shiga wata sabgar badan kuma al'amarin baya cikin ransa baneba. Ahankali Bilkisu ta shiga sauke numfashi, zufar na tsafewa sanyin ac na ratsata, kusan mintuna goma suna a haka.Rose da tunɗazun tai sumar tsaye tai Luuuu zata faɗi saboda wata hajijiya data rufe ganinta. Da sauri Hafiz da isowarsa kenan dasu Jabeer ya tarota. tai ƙoƙarin ƙwacewa jikinta na rawa zata sake danna kai cikin office ɗin idanunta na zubar hawaye Hafiz yay saurin sake fusgota, cikin tsawa-tsawa yace, “Rose! Minene kikeyi hakane?”. Wasu irin zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sake gangaro mata saman kumatu, ta tsare Hafiz da kallo, hannu na rawa ta nuna ƙofar office ɗin Jay, “Boss fa rungume da yarinyar nan”. Cikin takaici Hafiz yace, “Idan ya rungumeta sai akai me? Ba matarsa bace! matarsa ce ita halalinsa, ke kanki shedace akansa, inda Jay yana harkar mata ke zai fara lalatawa ai” ya ƙare maganar da balla mata harara yaja tsaki ya juya yabar wajen.
Da sauri Rose ta maida kallonta ga Jabeer da Aliyu. Tace, “Kunajinfa miyace, miyasa Hafiz baya ƙaunata?”. Ɗan murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa, “Hafiz ba ƙaunarkine bayayi ba, gaskiya ya faɗa miki, Mami matar Jay ce yanzun”. Daɓar Rose ta zauna ƙasa tana faɗin, “Jesus, shikenan na mutu Jabeer, yaushe akai musu auren?”. Duƙawa Aliyu yay gabanta cikin taushin murya yace, “Baki mutuba Rose, kisama ranki haƙuri dan ALLAH karki tada hankalinki kinji, ALLAH ya rubuta itace matarsa, kema naki mijin nanan zuw.......” “Aliy daina faɗamin maganar banza kaji, ni boss zai yaudara, dama tunda naga yarinyarnan na shige masa nasan zatai abinda yafi haka, nasan asiri tai masa kawai”. Ƴar Dariya Jabeer yay shima ya duƙa gabansu, “Rose na faɗa miki gaskiyar magana? Boss shike bin Mami ba ita ke binsa ba, tunda muke da ita bata taɓa nuna wanima a cikinmu ya taɓa koda birgetaba, shi kansa farautar soyayyarta yake amma sam taƙi bada ƙofar hakan, kullum ma nunawa take ita batama taɓa fahimtarsa ba, itaɗin mace ce mai AJI!, shine babban maganin asirinta akan zuciyar Boss, yakamata ki fahimci yana son mace mai suna mace, ma'ana mai Ajiiii!!”. ya ƙare maganar cike da salon iskanci yana salute ɗinta, miƙewa yay tare da mata nuni ta miƙe dan tayi sagafene tana kallonsa da fassara maganganunsa sala-sala.Sam Jay baiga Rose ba, Bily kanta data ganta halin data shiga yasa tama manta da ganin nata, ruwa ya ɗakko ya bata, babu musu ta amsa, yanda tasha ruwan sosai har mamaki ta bashi, ta miƙa masa kofin tana godiya, baice mata komaiba sai nuni da yay mata data tashi takoma kan kujera.
Nima ina buƙatar hutawar, dan haka na tashi na koma saman kujerar na zauna tare da lumshe idanuna.
Sosai nakeji a jikina kallona ake, ina buɗe idanu muka haɗa ido dashi, ɗauke kansa yay tamkar baniɗin yake kallonba, nima na janye nawa a raina ina jinjina yanda ya ƙware a iya kallon mutum.
Babu wanda ya sake shigowa office ɗin har aka kira sallar la'asar, shine ya fara shiga ya ɗaura alwala sannan yace naje nayi nima, lokacin dana fito tsaye na gansa, bance komaiba na nufi hanyar fita yana biye dani.

BẠN ĐANG ĐỌC
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Hành độngTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...