25

12.5K 1.2K 441
                                        

Page 25

.............Na daɗe banji irin wannan matsanancin bugun zuciyarba idan na samu kusanci dashi.
     Tunda Nabeelah ta sanar da shigowarsa duk sai na nema nutsuwata na rasa, farfesun da Ummah ma ta tsareni naci sai naji ya fitarmin a rai, ƙasa-ƙasa nake kallon ƙofar ta gefen ido harya shigo da sallama, Sanye yake cikin ƙananun kayan nasa na fama, sai dai sun masa ƙyau kamar ko yaushe. Da hannu yake amsama kowa sannun da yake masa saboda waya yakeyi. Ummah ta tura masa kujerar da take zaune a kai ita kuma ta koma kusa dani a bakin gado.
            Gaba ɗaya na kasa cigaba da shan farfesun har sai da Ummah taimin magana, “Saifa kin cinye abincin nan tas dota, garama ki dage kafin nasa a riƙeminke namiki ɗura”. Murmushi nai ina satar kallon boss da ƙamshin turarensa ya addabi hancinanmu, kasancewar turaren maza yafi na mata ƙarfi duk sai ya danne namu. A bazata muka haɗa ido, saurin janye nawa nayi dan banyi tunanin kallona yakeba. Farfesun na cigaba da tsakura kaɗan-kaɗan, har yanzu inajin idanunsa na yawo a kaina ko kunyar su Ummah bayaji.
     Kusan mintuna biyar ya ɗauka kafin ya ajiye wayar yana faɗin, “Am sorry Ummana nazo ina waya”. Murmushi Ummah tai masa, tace, “Babu komai Son”. Guntun murmushi yayi yana mai risinar da kansa ya gaisheta ita da Mama, kafin ya ɗorama mama da godiya. Mama tace, “Babu komai Jawaad, ai yima kaine, Bilkisu ta cancanci ai mata abindama yafi haka dan yarinyar kirkice mai tarbiyya, mu saidai muce ALLAH ya sanya alkairi a wannan al'amari ya kuma baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba”.
     Gaba ɗaya ban fahimci kalaman mamaba, dan dama Nabeelah ta shigo ɗazu tana cemin amaryar yayansu, kallonsa naɗan sata sai naga ya amsa da “Amin” akan laɓɓansa. Tunanin ko da aunty Shahudah aka ɗaura masa aurene yasa naɗanji nutsuwa. Ganin ya gama gaisawa da aunty Batool nima nace, “Ina kwana sir”.
         Amsamin yay da “Lafiya, ya jikin naki?”. “Alhmdllh naji sauƙi”. Bai sake cemin komaiba ya juya sukai magana da Ummah, sai naga sun miƙe sun fita. Numfashi na sauke a hankali ina rumtse idona, dan fitar tasa yasa naji kamar an saukemin kaya. Babu abinda nake buƙata a halin yanzu kamar ƙarin bayani akan abinda ya faru jiya tsakanina da ƴan gidanmu, banga kowa a cikinsu ba kuma yau tunda na farka, sannan kuma miya faru har aunty Shahudah ta nemi jimin ciwo su aunty Aamilah kuma sukaimin wannan bugun da gashi ya kaini da kwana a asibiti?........
         Ring ɗin wayatane da Ummie ta kawo ɗazun ya katsemin tunani, Nabeelah dake kusa da wayar ta miƙomin tana ƴar dariya, “Matar Yayanmu waye kuma masarauta?”. Wayar na amsa dan karta tsinke batare dana bata amsaba, bayan mun gaisa daga can Amaturrahman ke tambayata a ɗakin da nake?. Mamaki ne ya kamani sosai, ta yaya akai sukasan banda lafiya to? Kodai jiya sunzo ana wannan rikicin da bansan tshensa ba? Tunanin ƙila Ummie ce ta sanar musu ya sakani amsa mata da cewar bara na turo a shigo dasu. Da ga haka muka ajiye wayar, Nabeelah na kalla cikin marairaicewa nace, “Sorry dear, dan ALLAH ki shigo da baƙi wai suna waje”. Cikin dariya tace, “Karki damu matar yayanmu, girmankine ai”. Kasa haƙuri nayi nace mata, “Wai nikam wannan sunan daga ina haka?”. Sosai ta kwashe da dariya tana nufar hanyar fita da faɗin, “A wannan ba hurumina bane, yayanmu zai baki bayani”.
      Aunty Batool ce tace, “Fitsararriya ALLAH yasa ya jiki dai”. “Ba amin ba” ta faɗa tana ficewa fuska a kumbure.
      Murmushi mukai ni da mama, danni taɓarar Nabeelah dariya take bani, na lura gatane kawai yay mata yawa, ga uwa ga uba ga yayu ga dangi gata auta kuma. Mintuna baifi goma ba sai ga Nabeelah ta shigo dasu Amaturrahman bakinta fal magana da ganin jama'ar kamar jinin sarauta, dan tare suke da hadimai mata uku tare da wani dattijo, sai hadimai maza suma guda biyu.
    Tun a waje Jawaad da Ummah dake zaune suna magana akan yanda za'ai da bilkisu kafin lokacin tarewar sukaga Nabeelah dasu Amaturrahman, cike da mamaki suka bisu da kallo, ganin da gaske ɗakin da bily take suka shiga yasasu tasowa suka biyo bayansu.
      A waje suka iske hadiman su duka biyar, basuce dasu komaiba suka shiga.
       Amaturrahman na zaune a bakin gadon da babu kowa a kai tare da aunty Batool, Marwah tsaye kusa da mama dake a ɗayar farar kujerar ta wancan gadon. sai dattijon kuma a  kujerar da Jawaad ya tashi, , sai Safah data ɗane gadon kusa da bily tana taɓa kumburin fuskarta kamar zatai kuka, Bilkisu dai murmushi take mata, dan har cikin ranta takejin ƙaunar yarinyar da wannan shine haɗuwarsu ta biyu.
     Jawaad ya ƙaraso suka gaisa da dattijon cikin mutuntawa, fuskar dattijo da murmushi yace, “Ina fatan kaine mijin nata?”.
     Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi, babu shiri na zubama boss ido dan naji amsar da zai bada, saiko naji yace, “Eh nine ranka ya daɗe”. Idanun mamaki na zaro dan nama manta akwai mutane a ɗakin, wata ƴar harara naga ya zubamin ya ɗauke kansa, yayinda shi kuma dattijon ke faɗin yazo zasuyi magana a waje. Binsa yay suka fita. Cikin dawo dani hankalina Safah tace, “Aunty B mijinki mai ƙyau, zaki yarda na zauna gidanku?”. Dariya duk ƴan ɗakin sukayi, bandani dana kasa koda motsi, sai ɗan kaɗama Safah kai nayi kaɗan dan nikaɗai nasan a kalar ruɗanin da nake ciki. Buɗe ƙofar da aka sakeyine yasa duk muka kalli can, shine ya leƙo yay kiran mama da Ummah.
      Suna fita naji hawaye sun silalomin, da sauri nai ƙoƙarin gogewa dan banason kowa ya gani, sai dai na makaro dan Safah tarigada ta gani, da sauri tace, “Aunty B miyasaki kuka?”. “Ba kuka nakeba Safah, abune ya shigarmin ido” nai maganar da sauri. Tace, “Aunty B wai kema kina ɗaukata ƴar yarinyane? Nafasan kuka”. Tsawa Amaturrahman ta daka mata da faɗin, “Safah wai miye haka? Ke duk inda kika zauna saikin takurama mutane ne?........” Aunty Batool ce tai saurin katse Amaturrahman ɗin da faɗin, “Minene abin takura anan ɗin? Ai kulawama take bata”. 
        Marwah datun ɗazun bayan gaisuwa bata sake maganaba ta harari Safah ɗin da faɗin, “Aunty bakin yarinyarnan ne kamar bai gasuba”. Itama Safah ɗin harar Marwah tayi, tace, “Halan tarene ba'a gasa manaba, manya na magana kina wani tsoma musu baki mtsoww!”. Ƙwafa Marwah tai ta ɗauke kanta bata sake maganaba. Nai murmushi da riƙo hanun Safah nace, “A'a banda faɗa to, Marwah kema zo”. Babu musu ta bufoni, na kamo hanunta na zauna da ita ɗayan ɓangaren itama suka sakani tsakkiya.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora