Shafi na shirin da bakwai
............Koda motar Jawaad da ta Security's nashi suka iso ƙofar gidan nasu Shahudah basu shigaba, cayay suyi fakin a ƙofar gida.
Zamansa yay a mota bai fitaba, hakan yasa securitys nashi fitowa su zagaye motar da yake a ciki.
Yanata danne-dannensa a waya kai kace bashi bane ya fito Office ɗazun a fusace, sai dai shi yanajin zafinne a cikin zuciyarsa, yayinda fuskarsa ta shanye komai tamkar babu komai.
Har aka kira sallar isha'i suna wajen, da kansa ya buɗe ya fito daga motar dan son gabatar da salla.
Masallacin anguwar dake jikin gidan maƙwaftan su Shahudah suka shiga, tare dasu akai jam'i, suka bar waɗanda basayi a wajen.Bayan fitowarsu daga salla ne sai ga su Hafiz sun iso tare da Zaitun da Dr Jeo, sake shiga mamaki Zaitun tayi ganin ɗan uwanta Jawaad da take mutuwar ƙauna.
Shiko kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tamkar bai santaba ma.
Shi da rose da Hafiz, kawai suka shiga gidan, aka bar Aliyu da Jabeer a waje tare da securitys da su Zaitun da aka zubo a mota.
Amina data fito tana shirin wucewa gida tai azamar matsawa ta basu hanya jikinta na rawa, ko kallonta basu yiba kuwa, sai knocking ƙofar falon da Rose ta shigayi.
Amina da ta samu waje ta laƙe inda zata kalli komai, tace, “Ai dama tunda naji dambarwar da akeyi ɗazun a gidan nasan yau akwai kura”, dan haka tai azamar komawa ta ƙofar kicin ta baya, dan tayi alƙawarin sai taga komai kodan ta bama Bilkisu labari idan ta dawo.Tunda labarin zuwan Dr Tayyeb wajen Jawaad yazoma su Shahudah kowa ya kasa zaune ya kasa tsaye, ga Dad baya nan yayi tafiya jiya da yamma.
Aamilah tafi kowa shiga ruɗani dan dama can ita a kwai tsoron masifa, Shahudah kam dama tanada taurin kai tun fil azal, dukda tana a tsorace da sakamakon abinda zai biyo baya wani gefen zuciyarta na nuna mata Jawaad zaiyi buyaginsa naɗan lokacine ya sakko.
Wannan gurgun tunanin natane yasa bayan ta farfaɗo daga sumar da tayi saita ragema kanta fargabar.
Sunata ƙulla mafitar da zasu kare kansu ne a wajen Jay tun bayan farfadowar Shahudah, a wannan yanayin ne motar Jawaad data security's ɗinsa suka iso gidan.
Takun takalmansu Jawaad ya sakasu Mummy zubama ƙofar falon ido, dama Shahudah da Aamilah da Mummy ne kawai a falon, duk da kiran sallar magriba da akayi Mummy ce kawai taje tayi, maimakon taima Aamilah magana tunda ita Shahudah batayi saboda jinin ɓari sai batai ba, itako Aamilah dayake bata da man kai batai ko niyyar tashinba balle tunanin yi, idanma zaka bibiya ƙila yau daga sallar asubahi bata sake wata sallaba.
Kamar yanda Qaseem ya ɗorasu a kan keken ɓera koda Jawaad yazo kar wanda ya nuna razana hakan duk suka shirya, sai dai da yake a yanzu basuyi tunanin shi bane sai Aamilah ta miƙe domin duba mai knocking ɗin ƙofar.
Sun san dai idan Jawaad ne kansa tsaye zai shigo ciki.
Cike da barbaɗa ta buɗe ƙofar tana wani yatsine-yashine, taima Rose kallon sama da ƙasa tana faɗin, “Madam ke kuma fa?”.
Rose ta nunama Aamilah ID card ɗinta tana faɗa mata suna “Sunana Rose Ayo, ƴar sandar farin kaya”.
Karaf a kunnen Mummy da Shahudah, dan haka duk suka miƙe suma suna nufo ƙofar.
Aamilah data ɗansha jinin jikinta tace, “To lafiya?”.
“Ai mu dakin gammu kinga lafiya hajiya”. ‘cewar Rose tana wani annaminin murmushi.
Ƙoƙarin fita Shahudah da Mummy sukeyi, hakanne ya saka Rose basu hanya, itama Aamilah saita take musu baya.
Dukansu idanunsu akan Jawaad dake jingine da ƙarfen da akai kwalliyar barandar suka sauka, ya harɗe ƙafafu waje guda yana danna waya tamkarma baisan mi akeba.
Mummy da jikinta ke tsumar tsoron ganin yanayin Jawaad tace, “My son lafiya kuwa....?”
Kansa ya ɗago yana wani kaɗa hannunsa ya matse wayarsa tare da miƙewa tsaye sosai, a kausashe yace, “Ba ɗaba, Jami'in tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya *_JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSUF_* ne wannan, munzo ne domin gayyatar mutane uku na gidannan zasu amsa mana wasu ƴan tambayoyi a office Hajiya”.
Idanu sosai Mummy ta zaro, Shahudah kam ai neman faɗuwa ƙasa tayi, Rose kuwa dake mata kallon tsana ta tarota tana fadin, “Madam kulafa”.
Shiko Jawaad ko kallon inda Shahudah take baimayiba dama.
Aamilah cikinta kam ya ɗuru ruwa, harta fara ƙaramin fitsari a pant ɗinta😝.
Dai-dai nan Jack da Salman suka shigo, dan yajene ya gama shirin jirgin da zai tashi a safiyar gobe dashi zuwa ƙasarsa kamar yanda Qaseem ya bashi shawara, sam basuyi zaton zuwan Jawaad gidan a daren yau ba, ko a ƙofar gida da sukaga motoci basu kawoma ransu shineba tunda shi dai Salman yasan Jawaad baida Securitys.
Mummy zata sake magana Jawaad ya daka mata tsawa yana faɗin, “Hajiya nace wannan ba ɗanki bane, jami'in tsarone a gabanki ki kama kanki”.
Ba Mummy ba hatta dasu Hafislz kansu tsawarsa ta firgitasu, dama tunda suka iso gidan mamaki ya kamasu, dan dai a saninsu wannan gidan Gwaggonsa ce, kuma gidan surukansa. Furicinsa sosai ya sakasu a ruɗani, ya kuma basu umarnin tafiya da Shahudah da jack da Aamilah.
Yana gama lissafa da waɗanda za'a tafi ya doshi hanyar barin gidan cikin takun bajinta mai ɗauke da izzar fushi.
Gaba ɗaya ji da ganin Mummy sai ya toshe ɗaf, bibiyu ma takoma ganin mutane saboda ruɗani da mamakin Jawaad.
Kukan da Aamilah ke yine saboda tafiya da za'ai dasu ya maido Mummy a hayyacinta, duk roƙo da magiyar da takema su Hafiz babu wanda ya saurareta, umarnin boss ɗinsu kawai suke ƙokarin cikawa, duk da zukatansu a ƙulle suke da wannan aiki sukam yau.
Lokacinma da suka fito dasu Shahudah tuni Jawaad ya shige mota abinsa, ya lumshe idanunsa da sukai masa nauyi, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa bisa kansa, duk yanda yaso kiyaye irin wannan ranar sai da Shahudah tai ƙoƙarin zuwanta, to lallai kam zai tabbatar musu shi *_ƘWAI cikin ƘAYA_* ne, gashi dai abinso ga kowa, sannan kuma abin haɗari ga kowa, da kayi kuskuren ɗaukarsa kasha sukar ƙaya, ƙilama kana taɓashi ya iya fashe maka.
Tsabar ya manna musu hauka cayay a kaisu a ajiye, shiko yace a wuce gida dashi yana buƙatar hutawa.
YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...