56

13.2K 1K 98
                                        

Page 56

................A yanda Dad ya faɗo mana ya sakani zabura nai baya zan faɗi, Cikin sa'a boss ya taroni jikinsa, nannauyan ajiyar zuciya na sauke wadda tai dai-dai da wadda shima Dad ɗin ya sauke yana dafe kansa. Sai kuma ya juya ya kalli bayansa da faɗin, “Kai Humaira kedai lamarinki sai ke, wlhy na zata wani abunne ya faru da yaran nan kikaimin wannan irin kira na ujila haka”.
         Cikin tsananin ɓacin tai Mom dake kallon Dad tace, “Hakama zakace Alhaji? Yanzu tsabar wulaƙanci yaran su shigo babu neman izini cikin gidannan har su wuto nan kai tsaye tsabar raini amma kace hakan ba zama wani abuba?”.
         “Haba Humaira, yanzu nan wanene baƙonki a cikinsu? Jawaad dai ɗanki ne, tun bai kai hakaba yake shiga har ɗakin barcinki ma balle cikin gidanki, hakama itama Bilkisun ɗiyarki ce, dan aure ya ɗauketa daga gidan sai kuma ya zama laifi dan ta shigo, mtsoww, dan ALLAH kisan kin girma”. Dad ya ƙare maganar da raɓata ya fice cikin ɓacin rai. Da kallo Mom ta bisa ranta na matuƙar suya, sai da ya ɓacema idonta sannan ta juyo garemu. “K yanzu bakiji kunyar zuwa gidan nan ba butulu? Wlhy nayi nadamar saninki a rayuwata, da nasan zaki zamarwa rayuwar zuri'ata tauraruwa mai wutsiya da namiki addu'ar ƙare rayuwarki cikin masifa har abada, dan da bazan taɓa amincewa kin raɓemu ba, amma ni da kaina zanyi maganinki. Kai kuma lusari shasha, yarinya ƙarama ta gama tawaiwaye rayuwarka da tsafi ka kasa ganin kowa da gashin arziƙi, inda Abdul-aziz ne ke raye ai da bakai masa hakanba, kaje ai duniyace, wanda bai zoba ma jiransa take wlh Jawaad”. Tana gama faɗa ta fice abinta tana huci tamkar wata kumurcin maciji.
         Juyawa nai na kalli boss hawaye na zirara bisa kumatuna. Fuskarsa babu wani alamar damuwa. Yama fiske abinsa tamkar ba'ai komai ba, ƙasa na sulale zan durƙushe ya taroni jikinsa, rungumeni yay cikin ƙirjinsa yana ɗan bubbuga bayana, kusan mintuna uku muna a haka, baice komaiba ni kuma inata zubar da hawaye masu zafi da ƙunar zuciya saboda kalaman Mom. “Boss dan ALLAH ka faɗamin yanda akai aurenmu ko nima zan daina tuhumar kaina da cin amana, ta yaya za'ai mijin yayata ya koma mijina rana tsaka? Bana ganin laifin Mom dan kalamanta gaskiyane a gareni, ni.......” Shiiiiii!!!!” ya faɗa yana ɗagoni da ɗan ranƙwafowa dan ya fini tsaho, ya ɗaura hannunsa saman bakinsa. Ruf kuwa na rufe bakin nawa ina cigaba da kallonsa tamkar idanuna zasu zubo ƙasa dan tashin hankali. Sassanyan Murmushi yay min da kanne min ido ɗaya, yay zipping bakinsa alamar karna sake magana. Kaina na girgiza masa hawaye na sake gangaro min saman kumatu, baki na buɗe zanyi magana ruf ya rufemin shi da nashi batare da ya bari na ƙarasa faɗaba, wata irin sumbata mai cike da sirrika masu wahalar fassara yake aikamin, tun muna tsaye bisa ƙafafunmu har hakan ya nema gagararmu mukai baya zamu faɗi, saurin riƙe bango yay muka jingina jikinsa. Ganin yana neman wuce gona da iri nai ƙoƙarin ƙwatar kaina dan na fahimci yama manta nanɗin ba gidanmu bane. Da ƙyar na samu ya barni, muka ƙurama juna idanu, tunda nake ban taɓa juriyar kallon tsakkiyar idanunsa a tsahon lokaci kamar haka ba. Ya matso da fuskarsa dab da tawa har muna shaƙar numfashin juna, wani munafukin murmushi da bai wuce laɓɓansa ba ya sakarmin, sai dai hakan bai hana dimples ɗinsa da nake tsananin burgeni loɓawa ba, ya lumshe idanu a hankali sannan ya buɗe yana ɗaura ɗan yatsansa saman laɓɓana da suka gama shan wajala a hannunsa yanzu. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “A wasu lokutan baki yana ƙarya, yana yaudara, yana ha'inci. itako ZUCIYA abinda ke cikinta kawai take kuwwa a kansa, agaban kowa, a kuma ko ina. k wacece a gareni bakina yayi ƙanƙantar lissafa miki, wani jinin sai an tsaga ake ganesa a jini, karki zama mai gaggawa, karki zama mai wasiwasi, karki zama mai sakaci, dan bakowa bane mai ZINARIYAR ZUCIYA irin taki”. Ya ƙare maganar da ɗaura ɗan yatsansa saitin zuciyata. Kallon inda ya nuna ɗin nayi kafin na ɗago shima na kallesa, ya ɗagamin gira ɗaya da ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa da suka koma sirkin jaa, “Ke ɗin ta dabance, idan nace tadaban ina nufin tadaban a kowanne daƙiƙa na bugun zuciya da numfashina Bilkisu”.
      Kamar wata sakarai haka na bisa da kallo harya fice a ɗakin. Gaba ɗaya ya birkicemin tunanina, kalamansa suna dai-dai da tambayoyin jarabawa masu wahalar gaske da ruɗani ga ɗaliban dake zana jarabawar ƙarshe ta barin makaranta. ‘Mike nan?’ na faɗa a fili batare da tunanin mai bani amsarba........
      Sanin hakan da nai ya sakani bin ɗakin da kallo tamkar baƙona, sai kuma na juya jiki a sanyaye na fice daga cikinsa. Idanuna akan boss da ke zaune bisa kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya suka fara sauka, sai Dad da Mom dake zaune suma kusa da juna, Yah Salman na daga can Dining zaune da waya a hannu, sai Aunty Aamilah dake jikin ƙarfen bene ita kuma a tsaye. Takawa nai a hankali gaban Dad na durƙusa, hawayene ke zarya a kumatuna masu zafi da saka ƙunar zuciya, “Dad ina kwana” ta faɗa muryarta a ɗarare. Murmushi yayi yana gyara zamansa, “Ɗiyata yau da kanki a gidan nan? Ko dai ɓatan kai kikayi?”. Hawayen da suka cikamin ido suka gangaro akan kumatunna, na ɗago kaina ina kallon Mom da girgiza ma Dad kaina. “Kayi haƙuri Dad, nasan ni ɗin mai tarin laifukace a gareku waɗanda a kullum nike cike da damuwa da kunya a kansu, Dad wlhy banci amanarku ba, har yanzu bansan dalilin da yasa kuka auramin shi ba a maimakon Yah Qaseem, Dad  inajinka a rainane tamkar mahaifina, banason nazama silar ɓacin ranka kona minti guda kai da Mom, banason ka ringa kallona matsayin tauraruwa mai wutsiya, dan ALLAH kace ka yafemin, ka samin albarka kuma, ka roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu harta birgeshi kaine silar komai..........”
        Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.
        Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.
         Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa. Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.
          Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.
      Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta miƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace, “Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.
       Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.
        Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na kalli inda Aunty Aamilah take zanyi magana, wata muguwar harara ta watsomin tana jan tsaki da ɗauke kanta ta nufi ɗakinta. Duk da naji babu daɗi sai nai ɗan murmushi kawai najuya ga Yah Salman. Shima koda nai masa magana bai amsamin ba, haka na baro inda yake jiki a sanyaye naima Dad da duk abinda ke faruwa yana kallonmu sallama na fice.
            Fa kallo Dad yabi Bilkisu harta fice daga falon, ya sauke nannauyan numfashi yana gyara babbar rigarsa, kallon Aamilah da keta cika da batsewa yay ya ɗauke kansa, batare da yace mata komaiba ya haye sama abinsa. Ɗakinsa ya wuce, sai da ya rufe ƙofar sannan ya ciro wayarsa daga aljihu yay kiran Qaseem. Bugu biyu Qaseem ya ɗaga kuwa. Dad ya sauke numfashi yana cire hularsa ya zauna a bakin gadonsa, “Qaseem gasu nan sun fito, dan ALLAH ka danne ranka karka bari rigimar da kuka saba da yaron nan ta shiga tsakaninku, mu lallaɓasa musan inda Mamana take dan nasan wlhy shi kaɗaine keda masaniyar hakan”. “Karka damu Dad, namaka alƙawarin a daren yau sau Shahudah ta kwana gida, yanzun nan zan kirashi a waya nace masa yazo ya sameni muyu magana”. Qaseem ya faɗa yana danne ɓacin ransa da mugun tsanar Jay dake cimasa zuciya. Sallama sukai, Dad ya ajiye wayar yana sauke numfashi da haɗiye tsantsar damuwarsa akan rashin abar ƙaunarsa mafi soyuwa acikin ƴaƴansa. Qaseem kuwa daga can kiran Jay yayi duk da yana tunani da wahala ya ɗauka tunda bayin wayar sukeba, a yanzunma sai da Dad ya turo masa number Jay ɗin dan bashi da ita da.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt