34

8.3K 1.1K 25
                                        

Shafi na talatin da huɗu

...............Murmushi na sakeyi saboda yanda yaymin tambayar cikin zumuɗi, duk yanda zaiyi ka sake dashi dad ya sani, shiyyasa akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninsa da yaransa, kawai sakacine dai dashi wanda yake kallon hakan matsayin ƴancin kai.
      “Dad bansan yaya zaka ɗauki zancenba, dan mutanenmu da yawa sukan ɗauki aikin matsayin bai dace da mace ba, sai dai ƙabilun nan suna shigasu, mune dai gaskiya akan daɗe babu ɗiyan bahaushe a ciki....”
        “Kinga faɗamin kawai kanki tsaye, wane aikine?”.
      “Dad aikin ƴan sanda, sonake na zama ƴar sanda inhar kana ganin ya dace nayi?”.
       Kansa yaketa kaɗawa cikin murmushi, ya dafa kaina yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka Bilkisu, wannan tunanine mai ƙyau kuwa, wanda ya kamata ace yaranmu mata suna irinsa koda cigabanmu, ina goyon bayanki ɗari bisa ɗari, sai dai kibari zan zaɓa miki wanda zaifi dacewa dake kinji ko?”.
         Kaina na ɗaga masa ina jero masa godiya ta musamman,  dan ina ganin fatana na zama ƴar sanda maisa kaki zai cika.
        Ƴan sanda masu saka kaki yafi birgeni, aikin su Yah Qaseem bai cika birgeniba, dukda su ƴan sandane sunfi yin manyan ayyuka ba irin na ƴan sandan dana saniba masu fuskantar kowacce matsala musamman ma irin tamu ta cikin gidaje, to amma babu yanda zanyi, dan kimar Dad ta wuce nai masa musu koda a mafarkine, bazan dai taɓa masa biyayya akan abinda ya kauce shari'a ba, amma duk wanda ya zaɓamin zan amshesa matsayin zaɓin UBANGIJI na.

       Ina dawowa ɗaki Number Ummie na kira na sanar mata yanda mukai da Dad, taji daɗi sosai, dan haka tace zata sanarma Dadyn ta dan yazo ya samu Dad akan batun, dan suma duk sun sanar a gida kuma an barsu, Zuhrah ce kawai aka hana itama tana kan lallaɓawa.

*_KANA NAKA ALLAH NA NASHI_*

       
          Tabbas haka wannan batu yake, sanda kake tsara wancan sai kaga ba shine a kundin ƙaddararka ba, tunda tun farko bakai ka rubuta littafinba balle kai tunanin bin tsarin daka shirya ko zuciyarka tafi so.
    Kwanaki uku dayin wannan magana da Dad sai ga Dadyn Ummie yazo gidan, wanda na lura dai yaron Dad ne, dan abubuwa da dama daya shafi karatun yaran gidan shine tsaye a kansa, hatta da aiki ko wani abu shi dad ke ɗorawa akan nemawa wanda duk yaso.
      Bansan mi suka tattaunaba, na dai je mun gaisa, inda kamar yanda ya saba ya sakemin nasiha akan na kula da komai karna bari nai zirmawar da zanyi dana sani anan gaba.
     Na riga na gahimci hannunka mai sandarsa, dan yasha faɗamin karna yarda nai koyi da tarbiyyar gidanmu, ba ƙaramin daɗi nakejiba kuwa da wannan kulawar tasa, shiyyasa a kullum nake sake ganin kimarsa da mutunci.

     Nayi zaton ko Yah Qaseem zaice shi aure yakeso muyi baison na tafi wannan aikin, amma sai naji tsitt baice komaiba, sai dama akai kusan sati sannan yakemin tambaya akan maganar.
       Koda na bashi amsa murna kawai ya tayani muka cigaba da wata hirar kuma.
      Hakan sai ya bani mamaki, a shekarun Yah Qaseem ya cancanci buƙatar mace a kusa da shi, kumani ban taɓa kamashi da wata maceba ko ganin wani abu daya danganci mace a ɗakinsa balle nace yana neman mata, to minene matsalarsa? Dan a yanda yake nunamin dai ai yana buƙatar jin ɗumin macen.
     Na kauda wannan tunanin a raina dan bashi da wani muhimmin amfanin da zai mini.

     Su Aamilah kam dariya sukaita min, inajinta har aunty Shahudah ta kira ta sanarmawa itama tana tayasu.
      Mummy dai batace komai akan batunba, amma naji wani furuci nata daya tsayamin a ƙahon zuciya, wanda na lura ita gani take kamar dan neman kusanci da yah Qaseem ne ya sakani son aikin.
      Ni dai na tattara dukkan lamarina a hannun mahaliccina, domin yafi kowa sanin mike raina .
      Nakuma cigaba da miƙa kukana a garesa da fatan dacewa idan har aikin alkairine a garemu, idan ba alkairi bane ALLAH ya canjamana da wanda zai zama alkairi.
         kusan wata guda babu wani bayani daga Dad ko dadyn Ummie, dan dad ma har yayi tafiyar sati uku yaje ya dawo.
     Sai ranar kwatsam na dawo islamiyya na iske Dadyn Ummie da Ummien kanta a gidanmu. Muka rungume juna muna farin ciki, sannan naja hannunta muka shige ɗakina.
        Itace ta fara gumtsamin abinda ya kawosu gidan, tuni farin ciki ya mamaye min zuciya, muka sake rungume juna, kiran Dad ya sakani sakinta muka tafi falonsa tare.
      Na gaida Dadyn Ummie bayan mun zauna, Dad ya miƙomin takardun hannunsa dake tabbatar da an ɗaukemu zamuje training, harda ƴar ƙwallata ta murna tamkarma ance mun zama ƴan sandan.
       Su dad nata min dariya, duk da dai ba ɗan sandan danai fatar zama bane wannan ma nayi farin ciki dashi, naji a jikina shine alkairi a gareni shiyyasa ALLAH yay min canji dashi.
      Mun taso zamu fita naji Dadyn Ummie na faɗin, “Wlhy nayi mamakin hakan Alhaji, dan ban taɓa zaton Jawaad zai iya aikatawaba, kamar yanda na faɗa maka shine yayta ƙoƙarin ganin takardun yarannan sun shiga duka wlhy, musamman dayaji nace saƙon nakane.....”
     Banji amsar da Dad ya bashiba muka ida ficewa, ina mamakin wanene wannan Jawaad da ake yawan faɗar sunansa a gidannan? Sai kuma labarin da Amina ta bani akan Aunty Shahudah da mijinta ya faɗomin a rai, to kodai mijin aunty Shahudah ne? To amma miyasa Yah Qaseem ya tsanesa matuƙa? Bani da mai bani amsa dan haka na kauda zancen a raina kawai muka cigaba da hirarmu da Ummie.


*_INDA RAI! DA RABO_*

         Lallaikam inda rai da rabo inji masu iya magana, to nima dai Bilkisu yanzu na shaida hakan, dan kuwa yau gani cikin jerin waɗanda ake horaswa na hukumar ƴan sandan farin kaya a cikin (Training center) ɗinsu, tare da ƙawayena huɗu a karo na  uku.
         Duk yanda zan fasalta abun ba lallai ku fahimta ba, amma al'amarin ɗanba sauƙine, anji jiki kafin ƙashi da tsoka su saba, yayin da ƙarfin jini da karsashin zuciya ke ƙara yawaita, babu babban maicin ribar abu irin maiyinsa da yaƙini ko fushin son maida murtani.
     Nayi imani da hakan ya taimakama ƙwazonmu sosai ni da ƴan uwana, dan kuwa matakin farko na nasara damu aka shallakesa, kamar wasa sai gamu a mataki na biyu, inda mataki na uku ya kasance na masu babbar nasara, dan kuwa a cikin waɗanda muka shigo wajen mu sama da dubu biyu bamu wuce mutum dubu ɗaya da ɗari uku muka shallakeba, a kuma cikin dubun muka kasance mafiya ƙwazo mu ɗari uku da ashirin, cikin 300 ɗinan aka kuma rairayemu mu saba'in, mu goma sha uku ne kawai mata a cikin saba'in ɗinan, sauran duk sun kasance mazane, cikin amincin ALLAH kuma ko ina ina tare da ƙawayena.
         Mu 70 ɗinnan an waremu domin samun horo na musamman fiye da sauran ƴan uwanmu, ƙwazon da muke nunawa da juriya ya samu fita cikin ƴan rukunin farko kenan.
      
        A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har suka rikiɗe zuwa watanni, inda cikin amincin UBANGIJI muka cika dikkan shariɗɗan zamowa cikakkun ma'aikata abin alfahari.
      Tabbas wannan nasara da muka samu munyi matuƙar farin ciki da ita, ranar kuma nasha kuka saboda tunowa da iyayena da siraɗin rayuwa dana tsallake batare da hasashen kaiwa wannan matsayinba na yanzu.
      Shiyyasa akace babu maraya sai rago, wannan magana tabbas haka take.

★★★★★★

         Ranar data kasance ranar yayemu ta zamto rana mai daraja da zuciya bazata iya mantawaba, dukanmu muna cikin Uniform da suka ƙara mana kwarjini da cikar kamala, inda manyan baƙi da manyan wannan hukuma sukai jawabai masu nuna ƙwarin gwiwa a garemu da fatan alkairi, sai ƙyaututtukan karramawa da suka biyo baya na ɗalibai mafiya ƙwazo a cikinmu inda sunana ya fito a bazata.
       Wannan abu ya sakani ɗunbin mamaki da al'ajabi, dan ban taɓa kawo hakan a rainaba koda a mafarkina, dan ni kaɗaice mace a cikin waɗanda suka samu wannan karramawa.
          Dad yaji daɗi sosai, hakama Yah Qaseem, su Mummy ma dai dayake duk hardasu akazo sun tayani murna koda bata kai har cikin zukatansuba.
         Daga ƙarshe kowannenmu ya samu takardar tabbatuwarsa ma'aikaci tare da inda aka turaka, matakin karatu ya matuƙar taimaka mana wajen tsintar kai ba'a matsayi mafi ƙaranci ba, dan kuwa bamu kasance matakin ƙarsheba.
      Mun rungume juna mu dasu Zuhrah muna kuka, dan kuwa dai an samu matsala wajen rarrabamu bazamu kasance a waje ɗayaba, kowanne da inda aka cillashi, ni da Ummie ne kawai a waje ɗaya.
      Sosai hakan ya taɓa zukatanmu, har sai da iyayenmu suka koma lallashi da nuna mana ai dama aikin kenan, wannan ba makaranta bace balle muce tilas mu kasance a zaɓinmu.

★★★★★★★

         Sati guda cif da gudanar da bikin yayemu muka shiga filin daga, yau sai ga Bilkisu Adam makaho matsayin ƴar sanda ta hukumar DSS, Yah Qaseem shine ya zamemana fitila a komanmu ni da Ummie, duk da kasancewarsa babba a wannan hukuma.
      Aikin farko da muka fita Ummie tayisa cike da tsoro, ni naita ƙarfafa mata Gwiwa har itama ta samu ƙarfin zuciya, a cikin kwanakin da basu gaza sittin ba, waɗanda a jimlace zasu baka wata biyu mun gama gogewa, muma munaji a ranmu mun isa karanmu yakai tsaiko.............✍🏻

Akwai sauran pages 6 a ƙasa, nima sai naga ana zabga mana ruwan subscribing sannan zan sakesu🙄😂, waɗanda sukai mana sub... Muna godiya, ALLAH yabar zuminci, kuma nayi farin ciki dan duk wanda yayi na gashi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now