14

14.3K 1K 103
                                        

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce

Shafi na goma sha huɗu

..............Kusan a tare suka farka da ga barcin da ya kwashesu, sai dai yanda Shahudah taci karo da fuskar Jawaad sai zuciyarta ta shiga yimata wasuwasi.
      Ya sauka a kan gadon ba tare da yace da ita uffanba, bayi ya shiga, ta miƙe da sauri tabi bayansa, sai dai a mamakinta ya rufe ƙofar bayin.
     Ɗan bugawa tai kusan sau uku, yanajinta lokacin yana ƙoƙarin haɗa ruwan wanka amma sai ya shareta kawai tamkar bai jiba.
       Dole ta haƙura saboda motsin fara wankanta da tajiyo.
      “Mike damunsa kuma?” ta faɗa a fili cike da mamaki, kujerar gaban mirror ɗinta taja ta  zauna, bayan wasu mintuna kusan ashirin sai gashi ya fito yana tsane jikinsa da towel.
        Yanzun ma dai fuskar babu walwala, bai kuma kalli sashen da Shahudah takeba ya wuce wajen kayansa, jallabiya ya ciro a drawer, ya juyo zai saka suka haɗa idanu da Shahudah data kafesa da idanu.
        Janye nasa idon yayi  kamar bai ganta ba, saida ya saka jallabiyar a jikinsane ya ƙaraso gaban mirror ɗin yana ɗaukar turare zai fesa.
     “K bazaki tashi ki wanka ba kizo kiyi salla?”.
       Shiru kamar bazata tankaba, sai kuma ta sauke numfashi tana miƙewa, gabansa ta matso kamar zata shige jikinsa, ya ɗan matsa baya kaɗan yanda zasu sami tazarar data matse.
     “Humm” ta faɗa cikin kafesa da ido, muryarta a raunane tace, “Bb yanaga ka canja daga tashinmu? Naga cikin farin ciki muka shigo gidannan”.
      Turaren hannunsa ya ajiye, ya juya zai tafi ba tare da ya bata amsaba, saurin riƙo hannunsa tayi, bai juyoba, sai dai a hankali ya furta, “Karki ɓatan lokaci salla zanje”.
     Dole ta sakar masa hannu saboda fisgar da yayi, harya fice tana binsa da kallo.

         A tsakkiyar falon ƙasa ya tsaya, ba tare da ya kalli ko inaba a cikinsa yace, “K fito, idan kuma kika bari na fito dake wlhy saikin raina kanki”.
       
    Mamaki ya kamani, dan ni dai bilynku banga alamar mutum a falonba, amma maganar Jawaad ta sakani waige-waige, a raina ina tunanin ko aljani ya gano.
        kamar da wasa kuwa saiga ɗaya daga ƴammatan gidan ta fito daga ƙasan bene jiki na rawa.
        Fitowarta yay dai-dai da sakkowar Shahudah da tai tunanin Jawaad ya fice.
      Jikin Amrah sai ɓari yakeyi, dan batasan ta yaya Jawaad ya ganta a falon ba, tunda ta rigasu shigowa shi da Shahudah.
         Juyowa yay ya kalleta da rinannun idanunsa masu firgitasu, yay mata kallon sakwan biyu ya janye yana kallon Shahudah dake tsaye jikinta sai tsuma yake dan tsoro, dan batai tunanin Jawaad zai ga Amrah ba.
       Murmushin takaici ya saki launin idonsa na sake yin duhu, ya nuna kansa cikin ɗacin da yakeji a zuciyarsa yana faɗin, “Ni kika kirama wata taga yanda zanyi kwanciyar aure da ke Hudah? Saboda kawai ki burgesu akan ina miki duk abinda kikeso ko? To gata nan, saiki zauna kafin na dawo massalaci ki ida sanar mata duk abinda ya faru a cikin ɗakin da bata ganiba”.
       Ya maida kallonsa ga Amrah itama, tana tsaye tamkar zatai fitsari a wajen dan firgita,  “K kuma yanzu nasan kin yarda inabin dukkan abinda takeso ko? Tunda na amince mata ta zubar da ciki, ta kuma gigitani da salonta a gabanki wanda yasa nake koma mata soko” yay murmushi irin mai nuna tsantsar takaici ɗinnan, kasa cigaba da musu magana yayi ya juya ya fita zuwa massalaci.

            Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a fuskar Amrah, lallai taji kunyar abinda ta aikata yau, takuma yi nadamarsa, bata san miyasa ta biyena Shahudah ba, yanzu da ace Yah Jawaad ɗin bai farga da itaba ya kuma biyema Shahudah a falo ɗin tamkar yanda taso da ta kasance azzaluma, dan dafa sai taga komai na sirrinsu.......
       Dafa kafaɗarta da Shahudah tayine ya katse mata tunani, ta kalleta cikin takaici tana janye hannunta.
     A zatonta zataga nadama a idanun Shahudah akan abinda sukaso aikatawa, amma sai taga saɓanin hakan.
     Cikin dariya Shahudah tace, “Wai wannan faɗan nasa kikema kuka? Tab amma baki da wayo, mutumin da a gabanki ya komamin ƙaramin yaro shine mazuransa yanzu zasu ɗaga hankalinki, wlhy naso ya biyemin kiga abin dariya, ashe shegen idonsa ya hangoki, ni........”
      A harzuƙe Amrah ta ɗagama Shahudah hannu, “Ya isheki haka malama, ni wlhy bamma san bakida wayoba sai yanzu dana dawo cikin hankalina, bansan miya lulluɓe ganina ba har na iya yarda naga abinda zan shekara dubu ina nadama, Shahudah wannan ba wayewa baceba, dan ALLAH ki dawo akan ƙyaƙyƙyawan tunani na mutanen ƙwarai masu riƙo da addinin ALLAH, yanzu dan kawaifa ki birgeni kika jawoni nazo na laɓe dan naga yanda kike maida Yaya Jawaad kamar ba shiba a shinfiɗa, sirrinku, innalillahi, na shiga uku ni Amrah, wlhy naso tafka kuskure kam yau a rayuwata” da gudu Amrah ta fice daga falon tana kuka.
          Shahudah da jikinta yaso yin sanyi, amma zuciyarta dake ɗorata a shawarar banza tai saurin bijiro mata shaiɗaniyar shawarar da take bata sai tayi dariya tana taɓe baki, a fili tace, “Sun wani damu mutane da maganar sirri-sirri, uwarmiye sirri anan? Waima shegiyarnan Amrah da BF yafi talatin a cikin wayartace take faɗar kallonmu ni da Bb zaisata na dama, Mtsoooww aikin banza kawai, ni wlhy dama nayi mamakin yanda ya biyemin cikin sauƙi, mutumin da idan ina bukatarsa sai ya gama yanƙwalani kafin ya bani haɗin kai, amma ɗazun dandanan sai gashi ya miƙa wuya kamar yau ya taɓa sanina, munafiki kawai”.
    Ta ƙare maganar da juyawa ta koma ɗakinta.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now