33

8.1K 770 9
                                    


        Shafi na talatin da uku

................Duk wanda ya sanni zaisan inada damuwa tun dawowata gida, a kwana na uku da dawowata mukai ɗaya a cikin jarabawar data rage mana, ranar ƴan uwana suka nunamin ɓacin rai sosai akan abinda nake ɓoye musu, dan badan taimakon Nazifa dake kusa daniba da babu abinda zan rubuta sai shirme a takardata.
      Ba komai zai jawo hakanba kuma sai halin da nake ciki na ɗunbin tausayin Amina da fargabar tawa rayuwar idan na koma zaman gidan yanzu.
         Ganin sunyi fushi na basu haƙuri, sannan na ɗora da faɗin,
         “Ƴan uwana kuyi haƙuri, zan aikata muku babban laifi na canja burinmu nason zamowa ƴan jarida, yanzu na gane ba wan nan bane abinda nake buƙata, martaba da kare sauran ta ƴan uwana itace abar buƙatata”.
       “Wace magana kikeyi haka bily, mu bamu fahimceki ba” Rebecca ce mai maganar.
       Zama nai da ƙyau na shiga zayyano musu abinda na gani a gida, wanda inaji a raina cewa na manto abinda na koma ɗaukane dan na iske wannan iftila'in, dan ƙila daban ganiba babu mai bani gamsashen labari.
           A take naga duk sunyi murmushi mai ciwo, Nazifa ta miƙe tabar wajen tana kuka.
     Da kallo mamaki na bita, dan bansan manufar kukan nata ba, “Nazifa!”
      Na ambaci sunanta, hakanne ya sakata tsayawa cak sai dai bata juyo garemu ba.
     Miƙewa nai tsaye na taka zuwa gareta na dafa kafaɗarta, “Nazifa miya sakaki kuka a wannan maganar?”.
         Sai da taja wasu sakanni kafin ta juyo gareni, sosai take hawaye wasu nabin wasu, ta dafa tawa kafaɗar tana sake fashewa da kuka mai ciwo. Ban hanata ba, hakama sauran ƴan uwana babu wanda yay mata magana.
       Rebecca dake bayanmu tsaye tace, “Bilkisu, kukan da Nazifa keyi kukane namu mu duka, duk da dai ke mun ɓoye miki dalilin kukan tuni, sai dai maganarki ta yanzu ta sosa mana inda ke mana ƙaiƙayi harma da tuna mana abinda ya shuɗe”.
        Kallonta nayi sannan na maida gasu Ummie, kukan da Ummie take har yamafi na Nazifa, dan numfashinta har sama yake tamkar zai shiɗe ta fusgosa da ƙyar.
         Hankalina ya sake tashi mtuƙa fiyema da da, nace, “Ƴan uwana ku buɗemin abinda kuka rufemin ko zuciyata zata samu sukuni dan ALLAH”.
        Shiru sukai kusan na mintuna biyu, kafin Zuhrah tazo ta kama hannuna dana Nazifa zuwa inda muka taso.
        Duk zama mukai har Rebecca.
         Zuhrah tace, “Bilkisu kinsan dai mun taɓa baki labarin ƴar uwarmu data rasu sanadin sikila ko?”.
        Cikin ɗaga kai nace, “Tabbas anyi haka”.
       Zuhrah ta share hawayenta yana riƙo hannuna, “Bilkisu tabbas ƴar uwarmu nada sikila amma sanadin baƙin cikin fyaɗe ta rasu”.
     Cikin matuƙar razana na zabura, har taune harshe nake wajen ambaton “Fyaɗe fa kikace Zuhrah?”.
        “Tabbas fyaɗe Bilkisu, ni Nazifa nida ita akaima Fyaɗe a cikin gidanmu sunje mini weekend ita da Ummie, amma abin mamaki da al'ajab sai aka rasa wanda ya aikata mana wannan ta'asa, dan kuwa kamar yanda kika bamu labarin nan sai da aka bugar da Amina muma haka akai mana wlhy. Babu kalar binciken da ba'ayiba amma har yanzu babu wani bayani, kwannamu uku a asibiti ƴar uwarmu ta rasu saboda yanayin jikinta bayason wahala, da kuma dai ƙarar kwana. Bilkisu wlhy ba ɗiyan talakawa kawai akema fyaɗe ba, sannan ba mata kawai ba, harma da maza, ƙanin Rebecca an masa fyaɗe ta hanyar luwaɗi shima kuma ya rasu”.
       Kasa magana nai saboda kuka, jikina sai tsuma yake, hakan yasa na miƙe a fusace ina nunasu, “Amma duk da wannan abubuwan da suka faru da rayuwarku kuka ɓata lokacinku wajen tsara burinku akan business kawai? Rayuwa a hannun ALLAH take, amma baka yanke ƙauna daga rahamarsa, shiyyasa a kullum muke zama masu buri, kuyi haƙuri duk da ni ɗiyan talakawace, ban tashi gidanmu naga kuɗiba hakan bazaisa na cigaba da zama a cikin burinku ba gaskiya”.
     Dukansu kallona sukai, bance musu komaiba naja takarda da biro nai rubutu na tura a tsakkiyarsu.
       Dukansu kallon takardar sukayi, kafin su maido kallonsu gareni.
          “Wannan daga yau ni Bilkisu Adam makaho shine burina, ban isa canjawa gaba ɗaya ba, amma ko alwashin dana ɗauka akan Amina da Nazifa da ƙanin Rebecca da ƴar uwarmu data rasu suka cika naci riba”.
         Rebecca ta kamo hannuna ta ɗora nata, itama tace, “Daya yau nima Rebecca ina tare fake Bilkisu”.
       “Nima ina tare daku” cewar Nazifa tana aza hannunta akan na Rebecca, Ummie da Zuhrah ma duk suka ɗora tare da bamu goyon baya.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now