26

13.6K 1.1K 515
                                    

Page 26

BARKA DA JUMA'A

..............Jawaad da yay ɗan jim fuskarsa ɗauke da murmushi yana juya maganar gimbiya ta ƙarshe a ransa, koba komai ya sakejin kimarta, domin ta nuna tanada ƙyaƙyƙyawan tsari da tausayi akan talakawa. yace, “Shikenan ranki ya daɗe, ke uwace, kinada damar yanke duk hukunci daya dace a kanmu koda babu saninmu, sai dai ina neman alfarmar zuwa na sanarma kakana da kuma ƙannen mahaifiyata, zuwa gobe insha ALLAH zan dawo na sanar miki yanda mukayi”.
            “Wannan tunanin naka shine ƙyaƙyƙyawan tunani da yakamata ya fito daga bakin jajirtaccen ɗa mai riƙo da tarbiyyar magabatansa, kaje ka sanar musu ɗin babu damuwa, sai dai zan baka shawarar koda likita yace zai sallami bilkisu kace ya jinkirta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan nafison da an sallameta kawai nan za'a wuto da ita”.
        Kansa ya jinjina mata. Ta ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinta masu azabar ƙyau ta miƙa masa, “Kasaka Number ka anan, saika ɗauki tawa yanda idan sun amince ɗin zakai kirana ka sanarmin basai kayi wahalar zuwa ka koma kawomin bilkisu ba kuma”.
     Tasowa jay yay ya amshi wayar, Number sa ta musamman da wanda ya yarda kawai kuma yakeda kusanci dashi matuƙa kawaine ke da ita ya saka mata, sanan yay kira yaga tata, saving yay mata da Jawaad A yusif ya maida mata yana godiya.

___________________________________

          Tare Jawaad suka dawo da dattijon nan dan zai juya dasu Amaturrahman masarauta.
         Shi kaɗai ya shigo ɗakin da sallama ciki-ciki kamar yanda ɗabi'arsa take ta rashin son hayaniya, babu kowa a ɗakin, Safah kaɗaice kwance tana barci a gadon da Bilkisu ke jiyya, mamaki ya kamashi da tunanin ina suke har ita Bilyn?. kafin yay yunƙurin yin wani abu aka buɗe ƙofar toilet, Bilkisu ce ta fito ɗaure da zani, ta yafa ƙaramin towel a kafaɗarta da alama wanka tayo saboda yanda ruwa ke jiƙe da fuskarta, duk tsefaffen gashinta ya kwanto goshinta da gefen kumatu.
       Wani faɗuwa gabana yayi dan banyi tunanin iske kowaba tunda su Nabeelah sunce zasuje sallah, Mama kuma tunda ta gasamin jiki ta fita akan zata ɗauraye kwankikan da akaci abinci, bawani ƙwarin jikin nakejiba dama, dan dukan da sukaimin yasa jikina yin tsami ko ina ciwo yakemin, wai danma Doctor ya bani maganin ciwon jiki nasha. Nakasa koda ɗaga ƙafata da sunan juyawa baya, sai kawai na duƙe a wajen inaji tamkar ƙasa ta tsage na shiga ciki dan matsananciyar kunyar data riskeni, nice yau tsaye gaban boss babu riga? Dagani sai zani da ƙaramin towel ɗin dana yafo a kafaɗa, kaina sanye da hular wanka, dukda nasan fuskata kawai zai iya gani da hannayena zuwa gwiwa, sai ƙafafuna suma iya rabin ƙwairi dan zanin ya sauka min ƙasa sosai duk da ɗaurin ƙirji nai dashi, hakan ba ƙaramin abun kunya bane a gareni.
          Ɗauke kai Jawaad yay daga kallon daya kafeta dashi yana mai lumshe idanu a hankali da furzar da sassanyar iska daga bakinsa, baice da ita komaiba ya juya ya fita zuciyarsa na gudu da sauri-sauri.
          Hawaye nake kashirɓan da bansan dalilinsuba sam, dukda naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fita na kasa miƙewa tsaye bare na tashi. “Bilkisu lafiya kuwa? Ko jiri kike ganine?”. Muryar mama ta dawo dani hankalina. Saurin ɗago kaina nai ina share hawayen da suka jiƙen fuska, ganin dagani sai ita a ɗakin yasani sauke numfashi ina mai ɗaga mata kai alamar juwarce. Kwanikan hannunta ta ajiye tazo ta taimakamin na tashi tsaye, da taimakonta muka ƙarisa bakin hadon dan a gaske yanzun saima nakejin tamkar juwarce tazomin, ita ta taimakamin na shirya, ina kammala shiryawa su Nabeelah da Amaturrahman da Marwah na shigowa. Sannu suka yimin kafin Amaturrahman ta shiga tada Safah tana faɗin Su zasu wuce gida, jinai kamar nace su zauna, amma banda wannan ikon, ga Safah ta sanya kukan shagwaɓa akan itafa anan zata zauna tare dani. Ina mamakin wannan irin ƙauna da Safah ke nunamin.
      Kafin kowa yace wani Abu boss ya shigo ɗakin da sallama. Nidai ƙasa nai da kaina ban yarda nako saci kallonsaba, tambayar da yakema Safah akan mitakema kuka kawai naji, Nabeelah ce ta bashi amsa da cewar tace bazata tafiba anan zata zauna wajena. Banji ya bata amsaba, sai saukar hannunsa naji akan nawa dake riƙe dana Safah, a take tsigar jikina ta tashi, gashi har yanzu akwai damshin ruwa jikina dama, ya cire hannunta batare da yace uffan ba, binsu da kallo nai ta ƙasan ido har sukaje gab da ƙofa. Ranƙwafawa yay yaymata maganar da duk bamujiba a cikin kunne, ta ƙyalƙyale da dariya tana tsalle, shima wani shegen murmushi ya saki maiban mamaki, Safah tace, “Amma Yayanmu (Yanda taji Nabeelah na faɗa) kafin goben zaka rama mata dukanta ko? Inba hakaba saina saka Abbu ya turo sarkin tsabga na masarauta ya musu dukan mutuwa da dorinarsa”.
      Janyeta yay daga jikinsa da take neman shigewa yana lumshe idanu, a hankali yace, “Karki damu zan rama mata da kaina”. Sosai ta shiga daka tsallen murna Nabeelah da Mama na dariya harma da Amaturrahman, Marwah ce dai tai murmushi kawai tana rakuɓewa a jikina, juyowa yay muka haɗa ido nai saurin janye nawa, da hannu ya yafito Marwah alamar taje itama. Da sauri kam ta nufesa cike da ɗoki harda murmushin daya bama kowa mamaki, dan tunda tazo taƙi sakin jiki da kowa. Hannunsu ya kam suka fita, Amaturrahman taimin sallama tabi bayansu tare da Nabeelah da zatai musu rakkiya, mama kuma ta bisu da kalaman godiya dana addu'a. Nima haka godiyar nake musu har suka fice.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora