ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce
Shafi na goma sha biyar
...........Washe gari ma dai naga gata wajen Uwargida, yanda na saki jikina da ita sai itama ta sake yarda dani ɗari bisa ɗari, dan har barina tai naje wajensu ƴar daɓas.
Yanda suketa sinne kai basason mu haɗa ido sai suka bani mamaki, amma sai ban nunaba, dan na lura kunyata sukeji.
Nima dai a kunyacen nake dasu, amma sai na dake tamkar baniba, nanko ƙasan zuciyata a matuƙar tsorace nake da kowa na gidan, nakan danne zuciyata bana kukan zahiri sai na zuci, tunanin iyayena dasu Firdausi yana sake gallabar zuciyata.
Tun a yammacin ranar naga anata shigowa da drinks da wasu kayayyaki a kwalaye, tsoro ya sake kamani, danfa tabbas da gaske wannan sheɗaniyar takeyi, cigaba nai da neman tsarin ALLAH da sharrin kowannensu a zuciyata.★★★★★★
Washe gari aka tashi da shirin baiko kamar yanda Uwargida ta faɗa, tun da rana manyan hajiyoyi suka fara isowa gidan, abin idan ka gani zat tashin hankali, sam banyi tunanin wannan ƙazantar tayi girma da yaɗuwar haka a cikin al'ummar musulmai jinin hausa fulani ba, wanda ma baka taɓa zato ko tsammani ba saika ganshi a wajen.
Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai.
Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa.
Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi.
Kai jama'a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar.
Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha'i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu.
An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan.
Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha'i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida.
Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba.
Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya.
Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni.
Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, “Karki damu nine”.
Bansan inda muke jefa ƙafa ba, kasancewar gidan babban gidane, maido wutar da akayine ya saka gabana faɗuwa, ni dashi duk mukaja birki ba tare da mun shirya ma hakanba.
Surutai muka fara jiyowa wanda da alama ni suke nema, wasu na faɗin ta gudu, wasu na cewa ai da alama wata baƙuwace data shigo ta saceta kota kuɓutar da ita, dama su basu yarda da baƙuwar fuskarba.
Cikin hanzari yaja hannuna muka faɗa ɗakin mai gadi dake a bakin gate, hawaye kawai nake jikina na rawa.
Duk bidirin nemana da sukeyi muna jiyosu, wata naji tana tambayar Uwargida ko ina Sani?.
Uwargida tace tun da rana ta turashi can wani ƙauye danya bar gidan ma tace ya kwana acan da safe ya dawo.
Kallonsa nayi, dan da alama na lura shi ake nufi, kenan wasu sun fara zargin akwai saka hannunsa.
Tun suna ɗaukar neman nawa wasa har abun ya fara caja musu kai, dan haka suka rabu, akabar ƙalilan a cikin gidan, ɗaukar kowa na fice, saboda sun iske gate buɗe.
Saurayin ya ɗan leƙa ta Window, sai da ya tabbatar babu kowa kusa yay min nuni muje, hijjab ya bani na saka, ta bayan ɗakin mai gadin muka iske tsani, duk da tsahon katangar nan haka na hau tsanin nan ga tsoro na cina ga hawaye, da taimakonsa muka dira can baya, dayake ta canma ya saka tsani, kuma akwai abokinsa dake tsaye yana jiranmu.
Duk naji ciwo a jikina, amma sam tashin hankalin da nake ciki baisa na damu da ciwukanba.
Babu ɓata lokaci muka bar wajen, muna matsawa muka jiyo hayaniyar su Uwargida suna faɗin “tanan ta biyo” kugafa harda tsani, aiko tabbas akwai waɗanda suka taimaka mata ta gudu kenan. Buɗar bakin wata sai naji tace “kodai su ƴar daɓas ne”.
Bamu jiyo amsar da Uwargida ta bata ba mai adaidaitar da suka sakani ciki yaja yay gaba.
Na damƙe jakkar da saurayin ya bani a jikina sosai ina cigaba da yin hawaye, yanzu kuma ko ina zan dosa kenan?.
Wata zuciya ce tace, “Bilkisu duk kibar wannan guje-gujen, kibi shawarar zaɓi biyu, kodai ki miƙa kanki ga ƴan sanda, kokuma ki nema gidan ƴan uwan mahaifinki ko mahaifiya kije ga wani, idan sun riƙeki shikenan, idan sun nuna bazasu iyaba sai kisan mafita”.
Wannan shawara itace tai tasiri a raina, koda mai napep ya tambayeni batare da na shiryaba na faɗa masa anguwar da zai kaini.
Ganinai ya tsaya da napep ɗin yana kallona, “Hajiya kinsan kuwa mi kike faɗane? Anguwar nan gaskiya tana da nisa, nikuma wanda ya bani ke ya cemin tashar mota zan kaiki”.
Hawayen fuskata na share, murya na rawa nace ka taimakeni bawan ALLAH, kaga ni mace ce, tashar mota kuwa wajene mai haɗari musamman da daddare, amma anguwar da zaka kaini yanzu akwai wanda na sani, wajenta zanje kafin safiya idan ALLAH ya kaimu”.
“Gaskiya Hajiya bazan ɓoye mikiba, a darennan bazan iya zuwa har canba, yanzu idan mun tafi sai mukai goma na dare bamu isaba, to yaushene na ajiyeki harna juyo nikuma na dawo gida. Ki dai faɗi wani wajen bayan wannan ɗin”.
“Shikenan na gode” nai maganar cikin jan majina ina sharce hawaye, zuwa can wani tunanin ya sake faɗomin, bara naje gidan Inna zainaba, ko arziƙin kwana ɗaya tamin, da safe saina doshi gidan baba manu ɗin da nai niyyar zuwa, duk da dai bana zaton samun alfarma daga ko ɗayansu, amma zan gwada, karya zam na yanke hukunci akan gaibu.
Sake faɗa masa anguwar da zamuje nayi, dan haka ya tada napep muka cigaba da tafiya, sai yake cemin to ai shima cannema anguwarsu.
Wani daɗine ya kamani, dan dama dai bawani iya gane gidan inna zainaba ɗin zanyiba sai na haɗa da tambaya.
Shiru mukai na wasu mintuna, lokacu-lokaci ina cigaba da sharar hawayena.
Muryarsa na tsinkayo yana cewa, “Baiwar ALLAH kibar kukannan, ita rayuwa duk jarabawace, haƙuri kawai kesa a cimma buri, da alama dai wanda ya sakaki a keken nan mijinkine ko?”.
Shiru na masa ban tankaba, jin haka shima sai ya tsuke bakinsa, mun ɗan ƙara tafiya na sake jiyoshi yana faɗin, “Dai-dai ina zan ajiyeki baiwar ALLAH?”.
Muryata a dasashe saboda kukan dana sha nace, “Kace nan anguwar kake ai kaima? Dan ALLAH ko kasan gidan dogo kafinta?”.
Da sauri ya juyo ya kalleni, bakinsa har harɗewa yake wajen faɗin, “Can gidan zakije?”.
“Eh” na faɗa cikin mamakin razanar danaga yayi.
Yace, “Kai, to ai babanane dogo kafintan hajiya? Dan ALLAH kozan iya sanin ke wacece?”.
“Gidankune? To ko dai Yaya Shu'aibu ne?”.
“Ikon ALLAH, tabbas kuwa kin canka dai-dai, Shu'aibu ne kuwa, wacece ke dan ALLAH? daga ina kuma?”.
Murmushin yaƙe mai haɗe da takaici nayi, ganin yanda taɓarbarewar zuminci tasa ko juna bamu saniba dukda kusanci mai ƙarfi da muke dashi, shi kansa sunansa kawai nakeji a bakin Innata, amma ban taɓa ganinsa ba a ido, “Da wahala ka sanni, sai dai bansan ko kasan Asiya gurguwa data rasu kusan shekara ɗaya kenan?”.
“Tabbas na santa, dan gwaggona ce ma ai, tunda ƙanuwar innatace”.
Murmushi nayi mai ciwo, na maida kallona ga wata tukubar mai nama da muka tsaya dai-dai satinsa, mazane cike da wajen saboda mai shayi dake gefe, daga can kuma gabansu kaɗan mai doya da ƙwai, zaman masu wannan sana'a ne ya maida wajen dandali, harda masu suyar awara, gaddamar siyasa kawai kake jiyowa a wajen kamar zasu fara danbe, cikin share hawaye nace, “To ita mahaifiyata ce, ni kaɗaice kuma ƴarta tilo data bari a duniya”.
Jinai kawai yanata jero salati da sallalami, na maida hankalina sosai a garesa, cike da tsagwaron mamaki yace, “Yanzu nan dama Gwaggo Asiya nada ƴa amma ban saniba? Har tambaya nayi wlhy a randa mukaje zana idarta sai akace ai bata haihuba, to kodai dama baƙya tare da ita?”.
“Muna tare” kawai na iya cemasa saboda abinda ya tokaremin maƙoshi.
Saurin tada Napep ɗin yayi yana faɗin, “Kinga yi haƙuri na tsareki da tambayoyi a titi, muje gida duk a yisu............

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...