Page 31
...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan... zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa.
Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani ainun, mutum mai fara'a dason mutane.
Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki yazo ya sake hayewa sama.Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai. Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna a bakin gadon yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da bansan ko waneneba haka nai sallama, muryar Ummah naji ta amsamin, hakan yasa na gaisheta cike da girmamawa, itama daga can da kulawa ta amsamin tare da min ta'aziyya. Nai mata godiya Nabeelah ma ta amsa muka gaisa, sai aunty Batool itama, daga nan mukai sallama. Wayar na ajiye masa bakin gado na fita falo, Zama nai a kujera ina jiran ya fito naji hanlin da nake ciki, harga ALLAH bana fatan kwana a gidannan. Nai zurfi a tunani da jiran fitowarsa kira ya shigo wayata, gyara zama nai na cirota a aljihu, Amaturrahman ce, dan haka na ɗaga muka gaisa, daga can tace, “Mun jiki shirune, ca muke tun biyar zaki dawo?”. Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, kafin nai mata bayanin yanda zata iya fahimta, nakuma nuna mata cewar bamu dawoba muna ƙauyen su gimban sai dai gamu nan a hanyar dawowa” addu'ar isowa lafiya tai mana kafin mu yanke wayar. Na faɗama Amaturrahman hakane da tunanin idan boss ya fito zaiji tausayina ya maidani can a daren nan.

ŞİMDİ OKUDUĞUN
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AksiyonTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...