ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce👌🏼
Shafi na goma sha uku
.............“Alhaji akwai matsala fa”.
Jikin Alhaji lado na ɓari yace, “Yallaɓai matsala kuma? Akan mi? Yarinyarce ta gagareku samune ko yaya?”.
“Alhaji ba wannan bane, yarinya kam muna kan nemanta, insha ALLAHU kuma zamu sameta, matsalar danake faɗa akan ɗanka take, harbine a damtsen hannunsa, binciken likita ya tabbatar mana kuma jami'an tsarone suka harbesa a wajen, kuma da alama harbin anyisane bayan awa goma sha ɗaya kafin faruwar rigimarsa da yarinyar, lallai idan labarin nan yaje kunnen manyanmu reshe ne zai juye da mujiya, komai kuma zai iya ɓaci”.
Zufar data jiƙa alhaji lado yasa hannu ya sharce, harshensa har sarƙewa yake yace, “Yanzu miye mafita?”.
“Shine nima abinda na kasa haɗawa a raina gaskiya”.
Alhaji Lado yay shiru yana kallon ɗan sandan, sai buga hannunsa daya dunƙule yake cikin ɗayan, cikin taune leɓe yace, “Ni ga tawa shawaran”.
“Ina saurarenka Alhaji”. ‘Cewar ɗa sandan yana kallonsa’.
“Mizai hana shi likitan mu ƙara masa kuɗi ya rufe zancen da dabarunsa, dan gaskiya inason a kamo wannan yarinyan, cikin abokansa sun tabbatar min akwai abinda yarinyar tagani a ɗakin my son kwana bakwai da suka shuɗe, kwana biyar kafin faruwar wannan abun kenan, sannan rashin kamata barazanane a garemu baki ɗaya”.
“To Alhaji ka kawo shawara mai ƙyau, sai dai matsalar da nake hasashe kar yazam waɗanda suka harbi yaronka sun san fuskarsa ko wani abu dangane dashi, hakanne kawai zai kawoma shirinmu rashin tasiri”.
Nanma shiru Alhaji Lado yayi, zuwa wani lokaci ya saki wani nishi da ƙarfi, gaba ɗaya ya rasa wane irin tunani kuma zaiyi, yana ƙaunar Jazuli, sam baya buƙatar rasashi, gashi dama har yanzu baima farfaɗoba cikin hankalinsa, dan sosai bugun da Bilkisu tai masa akai ya shigesa har can cikin kansa.
Basu samo mafitaba a wannan zaman, hakan yasa Alhaji lado yace ɗan sandan ya bashi lokaci zuwa safiya zaiyi tunani akai._________________________
JAWAAD
_________________________............Da sallama ya shigo falon, Shahudah da mama Atika dake zaune duk suka zuba masa idanu, yana sanyene da ƙananun kaya farare tas gaba ɗaya, duk da bana kwalliya bane yayi ƙyau abinsa, ga wani annuri da cikar haibar kwarjininsa na fitowa a fuskarsa.
Babu walwala a kan fuskar tasa, ya risina yana gaida Mama Atika.
Cikin fara'a ta amsa masa tana tambayarsa ya aikin nasa, ta kuma ɗora da ƙorafin rashin zuwansa gaidasu a koda yaushe.
Haƙuri kawai ya bata yaja bakinsa yay shiru, bai ko kalli inda Shahudah takeba, ita kuma ALLAH bai bata tunanin tako gaidashiba.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna da basu gaza uku ba, kafin sallamar Uncle Uwaisu ta katse musu tunani.
Yana zama Uncle Bashir shima ya shigo, dan haka Jawaad yay musu gaisuwa a tare cikin girmamawa.
Sai da suka kammala gaishe-gaishen nasu, suma sukai masa ƙorafi akan rashin ganinsa akai-akai, kamar yanda ya saba dai haƙurin ya basu suma da tabbatar musu da yanayin aikinsane ya kawo hakan.
Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shiyyasa suka saki wancan zancen suka tsunduma maganar data tarasu game da ƙararsa da Shahudah ta kawo.
Hakan ba sabon abu bane a wajensa, shiyyasa baice uffanba har suka kammala, itama Shahudah aka sata ta maimaita komai daya faru.
“Jawaad kaji abinda matarka tace, shin hakane? kokuwa akwai kuskuren fahimtarta a ciki?”.
Guntun murmushi Jawaad yayi, cikin nutsuwarsa yace, “Uncle ni dai gareni babu komai, amma tunda ita na mata ba dai-daiba tayi haƙuri, akan rashin sanine”.
Dukansu sagade sukai suna kallonsa, duk da dama a koda yaushe irin wannan zaman ya haɗa amsar da yake basu kenan sai ta yau tafi ƙona ransu, a ɗan fusace Uncle Uwaisu yace, “Jawaad ka daina mana wani ɓoye-ɓoye akan abinda ke faruwa tsakaninka da matarka, mu dai iyayenkune ku duka, bamajin daɗin yawan matsalolin dake kunnowa a cikin aurenku, gashi kai kullum akazo irin wannan zaman sai kace batai maka komaiba, anya kuwa gaskiya kake faɗa?”.
“Uncle gaskiya nake faɗa, da tamin wani abu dana faɗa ɗin......”
“Wlhy ƙarya kake bb, ban maka wani abuba kake cewa kayi nadamar aurena, wai harma bazaka taɓa yafema kanka hakanba”.
Banza Jawaad yay mata bai tankaba, yayinda su Mama Atika suka zuba masa ido suga idan zaice wani abu, amma sai sukaji yaƙi cewa komai.
“To kaji abinda tace Jawaad”.
Uncle Bashir ya faɗa yana kafesa da idanu.
Kamar Jawaad bazai amsaba sai kuma ya gyara zamansa yana kallon Uncle Bashir ɗin, “Uncle wannan zancentane kawai, ita tasan a inda ta samoshi”.
Gaba ɗaya ba ƙaramin haushine ya turnuƙe zukatansu ba, musamman ma Shahudah da kamar zuciyarta zata babbake dan baƙin cikin murɗaɗɗen halin Mijin nata......
Mama Atika tai ƙarfin halin haɗiye nata ƙududun tana ƙaƙalo murmushin yaƙe, “To shikenan yanzu duk abar wannan maganar tunda yace shi babu komai, sai kuyi musu nasiha suyi haƙurin zama da juna kamar yanda kowa ke zaune a nasa gidan, ni dai zan faɗi maka albishir mai gidana Jawaad”.
Ɗago manyan idanunsa da suka sake girma saboda ɓacin rai yay ya kalli kakar tasu, sai dai baice komaiba.
Ta faɗaɗa fara'ar ta tana cewa, “Matarkace ke ɗauke da cikin wata ɗaya da wasu kwanaki”.
Kafeta da ido Jawaad yayi, sai kuma ya janye ya maida kan Shahudah, baka isa fahimtar farin ciki yayi ba kokuwa baƙin ciki.......
Shahudah ta katse masa tunani da faɗin, “Nifa kuma bar lasa masa zuma a baki Hajiya, dan wannan cikin zan zubdashine, dan yazo ne akan kuskure, sainan da shekaru tara zan sake amsar waninsa, lokacin mun cika shekara goma da aure.......”
Cikin Hanzari Uncle Uwaisu dake kusa da ita ya kai mata duka, kaucewa tai tana kumbura baki.
“Wai miyasa baki da hankaline shin Sabira?, mike damun tunaninki ne?......”
Murmushi Jawaad ya saki yana katse Uncle Uwaisu da faɗin, “Uncle barta, tanada gaskiyarta itama, haka muka tsara ba yanzune zamu haihuba saboda gudin karmu tsufa da wuri, “Hudah nawa kike buƙata dazai isheki ganin likitan da zai zubda cikin?”.
A matuƙar razani duk suka kalleshi, banda Shahudah da daɗi ya lulluɓe, babu kunya ta taso daga wajen zamanta ta faɗa masa ajiki tana ƙanƙamesa, dukda yaji kunyar hakan saiya basar shima yaɗan rungumota yana bubbuga bayanta, ɗago kanta tai ta sumbaci goshinsa da laɓɓansa, tana niyyar kissing ɗinsa ya kauda fuskarsa da ɗan tureta kaɗan a jikinsa.
Wannan abu yabama su Mama Atika matuƙar kunya, dan haka duk suka kauda kansu garesu, Shahudah kuwa ko a jikinta, neman ma ɗare cinyarsa take zata zauna yay mata gargaɗi da idanu.
Matsawa tai tana wata siririyar dariya da faɗin, “Bb har yanzu baka wayeba, ai dai matarkace ni balle ace munyi abu mara ƙyau, tunda komai ku hausawa a wajenku baida ƙyau.......”.
“Kinci gidanku Sabira”. ‘Uncle Bashir ya katse Shahudah cikin mata daƙƙuwa’ yaci gaba da faɗin, “Ke yanzu da ƙaniyarki a gabanmu kike faɗar wannan maganar?”.
A hannun kujerar da Jawaad yake ta zauna tana dariya, ta maƙale damtsen hannunsa tana ɗora kanta ta kwantar jikin hannun.
Ko motsi Jawaad baiyiba, ya kuma fuske abinsa kamar ba shi ta kwantama a jikiba.
Rashin mutuncin Shahudah ya wuce dukkan tunanin su mama Atika, dan haka suka ɗauke kansu akanta.
Mama Atika tace, “Kai yanzu nan Jawaad da hankalinka zaka biye mata ku zubda ƙyautar da ALLAH ya baku? Wane irin banzan aƙidane wannan? Ku ba'a haihuwa aka haifeku ne?”.
“Kiyi haƙuri hajiya, ni karkuga laifina, Hudah itace mai ɗauke da cikinnan, sannan itace zata haifesa, ta rainesa, ta bashi tarbiya, to taga bazata iyaba ni mizaisa na takurata, bayan kuma ƴancintane zaɓama kanta duk abinda taga ya dace da ita, inhar batason ta haihu yanzu zan goya mata baya ta zubda cikin, idan kuma zata haifesa zanfi kowa jin daɗin hakan,duk shawarar data tsaida ta sanarmin”. Ya ƙare maganarsa da ƙokarin cireta a jikinsa ya miƙe, “Kuyi haƙuri bara naje, dan nanda awa biyu zan sake fita, inason naɗan huta kafin lokacin”.
Babu wanda ya iya cewa komai sai Shahudah da tai tsigil tana faɗin, “Bb jirani mu wuce”.
Tsayatan kuwa yayi, ta shiga ɗakin Mama Atika ta ɗakko wayarta ta fito, a gabansu Uncle Uwaisu Jawaad ya kama hannun Shahudah suka fice abinsu”.

STAI LEGGENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AzioneTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...