45

17.9K 1.3K 368
                                        

Page 45

..................Ganin ya nata juya spoon a abincin ya kasa kai ko lauma ɗaya yasa tausayinsa kamani. nasan yana cikin yanayin ruɗani da shikaɗai yasan yanda yakeji, sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye komai daga fuskarsa harma da kuzarinsa. naɗan rumtse idanuna ina tariyo kalamun Umm-Anum. ‘Anya zan iya kuwa?’ na ayyana a cikin raina, daga can gefen zuciyata tace zaki iya ki daure, ruɗanin da yake ciki yana buƙatar kulawarki, hakan zai bashi nutsuwa. Kaina naɗan jinjina ina danne fargabata da matsananciyar kunyar da nakeyi na ɗaura hannuna akan nasa dake riƙe da cokalin.
     Ɗago lumsassun idanunsa yay yana kallona batare da yace komaiba. daƙyar na iya danne zuciyata nabar idanuna cikin nashi daya tsareni dasu, na langaɓe kaina cikin tsananin nuna kulawa nace, “Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaci abincin karya huce, kagafa harka rame, kanaso Ummah tace bana kula mata da kai duk farfesun da take sawa kullum Nabeelah tana kawowa”.       
             Lallausan murmushi na musamman ya saki har dimples ɗinsa guda biyu na loɓawa, haƙwaransa suka fito kaɗan, yaɗan lumshe idanu ya buɗe a kaina yana faɗin, “Yarinyarnan na kula wayo kawai kikeson min dan karna fita”. Ya ƙare maganar a hankali yana wani kashemin ido ɗaya da ɗage gira sama.
           Hannu na saka na rufe fuskata ina murmushi, ba ƙaramin kasheni murmushinsa yayiba, dan nikam zan iya rantsewa ban taɓa ganin kalarsa daga garesaba sai yau, fuskata a rufe cikin tafukan hannuna nace, “Ni ƴar ƙaramarnan da nice zan maka wayo?”.
          “Ba gashi ba kinamin”. Yay maganar da kamo hannuna ya miƙar dani tare da zagayo dani inda yake ya ɗaurani saman cinyarsa, ya zagayo hanayensa duka biyu kan cikina, kansa kuma na bisa kafaɗata. Jinai kamar na nutse dan kunya amma na daure kaina a ƙasa nace, “karfa kasa wani yaji ya ɗauka da gaske ne, ina ni ina yima boss wayo, bayan kai ɗin wayon ne da kansa”.
       Kansa ya ɗaura saman wuyana yana huramin iskar numfashinsa, hakanne ya saka tsigar jikina tashi lokaci guda, naɗan ƙanƙame jikina ina haɗiye yawu daƙyar. Dai-dai saitin kunnena ya ɗora bakinsa yana magana a hankali kamar mai tsoron a jisa, “Ni ina naga wani wayo tunda gashi kinamin kuwa, a wajene Jay yake boss, amma a gaban Zinaran bawane, kece boss ɗin. buɗe idonki kiga wani abu”. Sosai maganarsa ta nema fasan kai, ashe mutumnan haka yake yana magana raɗam abinsa, amma yayta mana mazurai a office. Janye hanayen nawa nayi daga kan fuska a hankali harna kaisu ƙasa sannan na buɗe idanuna dake rufe. Ina buɗewa yana ɗaura laɓɓansa akan nawa. Na zaro idanu sosai dan ba haka na zataba. Shima idanun nasa dake cikin nawa yaɗan zaro yana cigaba da abinda yakeyi.
       Nasan banida ƙarfin dazan ƙwace, kuma ma nayi alƙawarin insha ALLAH bazan taɓa zama mai bijirewa a garesaba a komai da zaizo min dashi inhar bai taka dokar ALLAH ba. Ballantana a yanzu da nake hango tsagwaron damuwa akan fuskarsa, dannewa kawai yake dankar na fahimta. Mun kwashi tsahon mintuna biyar ahaka kafin ya barni, ya rungumeni muna sauke ajiyar zuciya a tare, ya sumbaci kuncina da wuyana, acan ƙasan maƙoshi yace, “Idan nace tadaban ina nufin keɗin tadabance har ƙasan ruhina Miemaa, a kwana biyu kacal da mukai dake na fahimci ƙyawawan abubuwa masu yawa daga gareki, inason mace mai juriya da biyayya akan abu koda bai mata ba, inason mace mai tsafta da ƙamshi, inason mace mai kawaici, kunyarki tana a farkon abinda ke ƙara miki daraja da girma, inason mace mai aji, mai addini, mai kamun kai, na tsani ballagazar mace mai rawar kai, da ace ƴammata da yawa zasu zama irinki da sun zama masu darajar daraja bisa daraja a wajen maza......” ya ɗagoni daga ƙirjinsa, muna haɗa idanun nai azamar maida kaina a ƙirjin nasa.
       “Ka daina huramin kai da yawa irin haka, yanda kake lissafin nan bankai haka ba, ni macece mai rauni, maison kulawa, waɗanan makaman suna saurin sakani bama mutum yarda, ada kallon bahagon mutum nima nake maka, wanda ba damu da damuwar kowaba sai abinda ya shafesa, amma a tsakanin jiya da yau na kula kai adaline mai sauƙi ga iyalanka, ka yafemin akan gurɓataccen tunanina, idan nace kai na dabanne ko a cikin mazan ina nufin nadaban a cikin miliyoyi, ba dan kafi sauran maza bane dan dukiya, ba dan kafi sauran maza bane dan ƙyau, ba dan kafi sauran maza bane dan darajar da ALLAH ya baka, kafi sauran mazan dan kai ɗin mai ƙyaƙyƙyawar ZUCIYA ne”. Na ƙare maganar da ɗora yatsana akan saitin zuciyarsa ina hawaye”.
        Bilkisu ko duniya zatace ƙarya nake saina faɗa, keɗin tadabance ko acikin nadaban ɗin kinzo da banbanci mai tazarar nisa.  
        “Karfa kasa mata sumin bugun kayan wanki”. Ɗagoni ya sakeyi yana murmushi, “Su sun isa ko kallon banza ga matar Jay ma”. Dariya muka ƙyalƙyale da ita a tare saboda yanda yay da fuska kicin-kicin kamar mai shirin shiga filin daga. Na yunƙura zan sauka daga jikinsa ya sake riƙeni. Naɗan marairaice masa batare da nabari mun haɗa idanu ba, “Yanzufa za'a kira sallar isha'i, ga abincin zai huce kuma”. Siririyar ajiyar zuciya ya sauke yana sakina, “Idan bakiso na fita akwai sharaɗi”. Kallonsa nai alamar ina sauratensa. tattausan hannunsa ya ɗaura akan haɓata ya matso da fuskata gab da tashi. “Idan har bakiso na fita sai dai ki ciyar dani da hannun nan naki, inba hakaba bazanci abincin nanba, kuma saina fita, kuma yunwa nakeji, kuma nagaji barci nakeji”. Ƙoƙarin juyar da fuskata nayi dan kunya da dariyar dake tahomin dan a narke yay maganar, amma ya hanani damar hakan, saima wani sake narke fuska da yayi irin na (Aji tausayina ɗinnan😔).
          Da sauri na jinjina masa kai danya barni na tashi nidai, zuciyata sai wani zallo take cikin ƙirjina tamkar zata fito, ga kunya kamar ƙasa ta buɗe na shige ciki, dan kusani ALLAH ba ƙaramar dauriya nakeyiba yasin.
      Ɗauke hannunsa yay ya gyara zamansa, hakan ya bani damar tashi tsaye, kujerar kusa da shi ya zaunar dani da juya kujerar yanda zanyi facing ɗinsa sosai. Ya zanyi, nina taroma kaina match ɗinan ai. Abincin na fara basa idanuna a ƙasa ban yarda na kallesa ba, amma shi inajin yanda idanunsa kemin yawo a zahiri da baɗini na, koda naɗan saci kallonsa sai muka haɗa idanu. Saurin maidasu nai ƙasa, daga haka ban sake ɗagowarba harna tabbatar ya ƙoshi. Ina murnar an gama zan tashi ya riƙe hannuna, kallonsa nai ya ɗagan gira, “Malama saura ke dan baza'amin ɗuraba ni kaɗai”. Dukda da gaske yunwar nakeji saina ɗan ɓata fuska nace, “Nifa na ƙoshi”. “Idan na yarda kenan”. Yay maganar yana ɗebo abincin ya kai bakina. Dole nima na haƙura na karɓa, yana bani yana addabata da kallo, hakan yasa duk naji na takura matuƙa. Sai da ya tabbatar na ƙoshi sannan ya barni.
          Naɗan kallesa ina tattare kayan ganin bai tashiba, kuma salla akeyi. Nace “Sallafa akeyi”. “Kin karyamin alwalata ai?”. Yanda yay maganarne ya sakani barin wajen da sauri na nufi kitchen. Bayan na kammala ɗauraye kayan na fito, ban iskesaba ya tashi, ɗakina na nufa nima domin gabatar da sallar isha'i.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Where stories live. Discover now