😂😂🤣😂🤣😆😆😆Kunsan miyasa nake dariyarnan? Akan yanda kuke ganin kamar bily tsoron Jay takeyi, dukfa halin da take shiga shiba fahimta yakeba, hasalima kallon miskila idan kun lura yake mata, akwai masu samun kansu a irin yanayin bily akan wani ko wata, sai daga baya suke fahimtar dalilin shigarsu irin wannan halin, itama bily lokaci zai warware mata komai har muma mu sami amsa, ina muku fatan alkairi aduk inda kuke, sosai Comments naku na sakani nishadi da sani typing kodama ban niyyaba.
I love you wujiga-wujiga irin trillions ɗinnan🤸🏼🤸🏼🤸🏼 😍😘😍😘😍😘🤗.Page 6
Ko kaɗan ban fahimci dani yakeba, musamman dana waiga naga rose data fito daga office ɗinsa a bayanna, wani kallo naga ta watsamin mai kama da takaicin tabi bayansa. Numfashi na sauke mai nauyi na shafa ƙirjinna dai-dai saitin zuciyarta dake harbawa da sauri-sauri, duk da na fahimci kallon da rose tai mani sai hakan bai dameni ba, dan bata ita nakeba. Nima fita nai daga wajen, na fito ainahin harabar station ɗin domin nufar sashenmu.
“Ɗi! Ɗi! Ɗi!!” gimba ya danna mata horn kamar yanda Jay ya bashi umarni.
Duk da naji horn ɗin hakan baisa na fahimci da ni akeba, saboda idan akai dubi da sauran jami'ai irina daketa kaikawo a harabar wajen, kowa da hidimarsa.
“K! Wace irin daƙiƙiyace da baƙya fahimtane? A haka kike tunanin zama jami'ar tsaron al'umma!!?”
Maganar Rose a tsawace ta shiga dodon kunnena ina gab da shiga lungu da zai sadani da office ɗinmu. Da sauri na juyo, idona ya sauka akan rose dake huci da jifana da kallon takaici mai nunin tsana. Duk da naji zafin kalaman datai amfani dasu a gareni sai na danne saboda tana sama da ni, a ladabce nace, “Kiyi haƙuri maa! Bansan dani kike ba”.
Tsaki rose ta buga, tare da juyawa tabarni a wajen, wani jami'i dake tsaye kusa damu ya kalleni da tausayawa, dan shi dai yarinyar tunda tazo station ɗin ɗabi'unta birgesa sukeyi, ganin ban fahimci manufar rose ba sai yay min fassara akan nabi bayanta maybe kirana akeyi.
Godiya nai masa, kafin nabi bayanta cikin nutsuwata, sam ban iya sauri ko rikita kaina a tafiya ba koda kuwa a tsorace nake, a yanzunma duk da zuciyata na cike da tunani da baƙin cikin abinda tamin ban rikita kainaba a yayin bin bayanta, can na hangota jikin wata farar mota mai ƙyau da ɗaukar hankali, na cigaba da takawa a nutse gareta, ina isa jikin motar ita kuma tana buɗe gaba ta shige, hakan sai ya sakani a duhu, dan bansan kuma wajenwa zanje ba. Saitin inda take na ƙarasa, na ɗan risina yanda zata ganni ina faɗin, “Gani maa!”.
Kafin ta bani amsa ƙofar murfin baya naga ta buɗe, ita da drivern naga duk sun kalli bayansu, hakanne ya sakani kallon murfin ta waje nima, muryar drivern ta katse min tunani, “Ki shiga” ya faɗa yana nunamin bayan.
Duk da na shiga ruɗani, ga harbawar da ƙirjina keyi hakan bai hanani bin umarninsaba, koda wasa ban kalli waye a bayanba, na shiga kamar yanda aka umarceni, sai da na zauna ne wani mayen ƙamshi ya samu cikakkiyar damar surɗaɗawa a ƙofofin hancina, da sauri nai ƙoƙarin kallon gefena, gabana ya faɗi dan ganin wanda banyi zatoba, fuskarsa babu alamar wasa kamar yanda na gansa yanzu da mukai karo.....
“Sai kin gama kallona zaki rufe ƙofar ne?” muryarsa ta daki dodon kunnena babu zato, kaina na girgiza da sauri ina tattaro busashen yawun bakina da ƙyar na haɗiye, tare da jawo murfin motar na rufe. Nama rasa yanda zan fassara wannan al'amarin sam, gashi yanayin dana tsinci kaina ya hana mani damar yin nazarin daya dace da hakan.Ɓangaren Rose da Gimba kuwa mamakine fal a rayukansu, gimba shaidane akan bai taɓa ganin rose ta shiga bayan motaba kusa da boss, baima taɓa bata wannan damarba koda a fuskane, idan har kaga wani ya zauna a kusa da shi to lallai sai dai cikin su Aliyu ne, amma yau abin mamaki sai gashi shi da kansa yasa hannu ya buɗema yarinya ƙarama murfin mota, ya kuma bata lasisin zama a gefensa, ‘Anya kuwa?’ ya ayyana akan laɓɓansa yana mai satar kallonsu ta mirror.
Ita kanta rose a kume take da mamaki, ita duk zatonta wani abun zai saka yarinyar, bata kawo a ranta wannan abar zuwan jiya hukumarsu har tanada lasisin shiga cikinsu ba, balle harma ta shiga motar da boss yake ciki, a kusa da shima, shi da kansa ma ya bata lasisin zaman, abinda ita bai taɓa bata fuska a kaiba, ko zaman gaban motar da yakema sai ya gadama yake barintayi koda taso hakan kuwa, idan ko bata mantaba wannan itace shekara ta bakwai cif tare da shi tana aiki a ƙarƙashin group ɗinsa, ‘To mi hakan ke nufi?’ tayi tambayar a zuciyarta.
Shi kansa Jawaad mamakin kan nasa yake, amma da yake shi kogine babu mai gane gabansa balle bayansa sai bai nuna koda a fuskaba, hasalima tunda suka fice daga station ɗin kansa na duƙene yana danna tab.. Da alama wani abun yakeyi, sai dai ƙamshin turaren bilkisu duk ya addabi hancinsa.
Kowa da abinda yake kissimawa ransa har suka iso inda yake buƙata, gimba ya samu waje yay fakin, babu wanda yay yunƙurin buɗe motar a cikinsu balle ai tunanin fita, duk suna jiran umarni daga garesa. Shiko yay burus tamkar baiji motar ta tsayaba, sai faman danne-dannensa yake cigaba dayi a tab ɗin.

YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...