Shafi na talatin da takwas
..............Bayan wucewar abokinsa office ɗin Sir Ahmad ya wuce domin amsa kiransa, yana ƙoƙarin shiga yaci karo da Qaseem shima ya fito.
Ƙoƙarin ɗauke kai Qaseem keyi, shima Jawaad ɗin har yayi niyyar hakan, sai kuma yaga rashin ƙyautuwar abun, Murmushi ya saki har kumatunsa na loɓawa, ya miƙama Qaseem hannu yana faɗin, “Assalamu alaika”.
Ƙin miƙo nasa Qaseem yayi, sai dai ya amsa masa sallamar.
Jawaad ya kamo hannun Qaseem cikin nasa tare da faɗin, “Haba ɗan uwana, miyay zafi shiba wutaba? Ina fatan na sameku lfy? Ya jama'ar gidan?”.
Ran Qaseem ya sosu da wannan rainin hankali na Jawaad, danshi matsayin rainin hankali kawai ya kalli abun, dan haka ya kasa daurewa yace, “Da wannna salon kuma ka dawo?”.
Jawaad ya murmusa yana sakin hannunsa, cikin gyara tsaiwarsa yana shafa gemu da tura hannunsa ɗaya a aljihu yace, “Minene abin salo anan Qaseem? Kaifa ɗan uwanane jinina, sannan ga alaƙar musulinci a tsakanina dakai, kuma kai yarenane, ogana a wajen aiki, shekara biyu rabon da ka ganni na ganka, da akwai ƙaddarar mutuwa tsakaninmu maybe wani zai samu saƙon mutuwar wanine a tsakaninmu, nidai tsakanina da ALLAH na gaisheka, ya rage naka ka ɗauka hakan kaima ko saɓaninsa, na barka lafiya”..
Sagade Qaseem yay yanabin Jawaad da kallo harya shige office ɗin Sir Ahmad, yayi kamar ya bisa cikin office ɗin sai kuma ya fasa, ya nufi office ɗinsa yana juya kalamun Jawaad cikin ransa.
Jawaad kam koda ya shiga, bayan yayi gaisuwar girmamawa ga sir Ahmad sai ya nuna masa wajen zama.
Hannu Sir Ahmad ya bashi cikin musabaha suka sake gaisawa, dukda dai Jawaad na nuna jin kunyar haka ɗin.
“Jay kasan miyasa na kiraka kuwa?”.
“A'a Sir”. ‘Jawaad ya faɗa cikin kaɗa kai’.
Zama sosai Sir Ahmad ya gyara, ya fara magana idanunsa akan Jawaad ɗin.
“Wato zakayi mamaki idan nace maka baƙin abubuwa da yawa sun sake shigoma hukumarnan, masu ban tsoro da mamaki. Akwai cases da yawa dakai kanka ka fara ka tafi kabari to ina mai tabbatar maka da yawansu ba'a ƙarasa suba har zuwa yau da nake maka maganar nan, waɗanda kuma aka ƙarasa ɗin sun canzu ga bisa salon daka barsu gaba ɗaya ma. Gashi wasu cases ɗin sun sake ƙaruwa da yawa, akwai jami'inmu mai matuƙar ƙwazo kamar kai ɗinnan, bayan tafiyarku nagartarsa ta sake fitowa, amma kamar yanda na sanar maka ranar ya fita wani aiki sai dai gawarsa aka kawo mana, kasan wani abun mamaki?”.
Jawaad da idonsa ya kaɗa yay jazur ya girgiza kansa.
Murmushi Sir Ahmad yayi na takaici yana cigaba da faɗin, “Abun mamakin da har yanzu yake cizon zuciyata shine bullets guda uku da aka harbi Abdallah dashi a ƙarjinsa da cikinsa dukansu bullets ne na jami'an tsaro, abi mafi al'ajab Bullets ɗin suna cikin bullets guda dubu sittin da shida da aka kawo ƙasarnan shekaru tara da suka wuce, waɗanda a zahirance bayanai sun nuna bullets ɗin sun ƙare gaba ɗaya bayan shekara ɗaya da wata bakwai da kawosu, bullets ne masu matuƙar haɗari, dan inhar akai harbi mutum dasu acikin seconds ashirin dukkanin illahirin jinin mutum ke tsinkewa, idan ba'ai gaggawar kaisa asibiti ba ya samu taimakon gaggawa zai iya rasa ransa a ƙanƙanin lokaci, sannan ba a kowacce bindiga yake aikiba. To abin tambaya anan, yaya akai bullets ɗin da suka ƙare shekara huɗu baya kuma suka kashe mana jami'inmu? Daga ina suka fito? Wasune aka sake shigowa dasu? Koko dai sune ɗin?”.
Gaba ɗaya jijiyoyin Kan Jawaad sun mimmiƙe ruɗu-ruɗu, maƙoshinsa sai kaikawo yake a wuyansa saboda tsabar haɗiyar busashshen yawu mai ƙona zuciya.
Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace, “Sir akan wane case wannan abun ya faru?”.
Sir Ahmad yay murmusa idonsa akan Jawaad, mazantakar Jay akan aiki da kishin ƙasarsa yasa ako wane lokaci yafi sha'awar ganinsa akan aiki na musamman, yaɗan ɗage kafaɗa yana buga tebir kaɗan da komawa cikin kujera ya kwanta, har lokacin idonsa akan Jawaad,
“Jay ƴan bindiga daɗi ne kawai, amma ga dukkan bayanan komai anan”. ‘Ya ƙare maganar da tura masa wani file gabansa’.
Ɗauka Jay yayi ba tare daya buɗeba, babu abinda zuciyarsa keyi sai tafarfasa kawai, shiru Office ɗin yayi na wasu mintoci, kafin Sir Ahmad ya katse shirun da faɗin, “A yanzu kana buƙatar runduna ta musamman Jay, fiye dasu Jabeer kawai, munada sabbin ma'aikata masu jini a jika da karsashin aiki a ransu saboda yanzune jinin jikinsu ke zagayawa cikin kowacce jijiya dalilin ƙuruciya da zafin rai mai tare da ɗokin aikin, sannan a cikinsu akwai kwararrun maharban da suka samu horo na musamman a ɓangaren harbi, wanda an daɗe ba'a yaye sabbin horaswa da wannan ƙwazonba a hukumarnan tamu, shawara kawai na baka ba umarniba, dan zuciyata ta yarda da kai, yarda irin wadda ko ɗan dana haifa ban yimawaba duk da kasan cewarsa jami'in tsaro shima, ALLAH yayi jagora haziƙi kuma jarumin yarona abin alfaharin ƙasarsa da ƴan ƙasa”.
Zazzafan numfashi Jawaad ya sauke yana miƙewa idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta, yay salute din sir Ahmad sannan ya fice tamkar wanda zaije filin daga.
Koda ya isa office ma gaba ɗaya zuciyarsa a dagule take, yama rasa wane kalar tunani ya dace ace yayi, dan lamarin ƙasarsa a kullum sake bashi tsoro take, tsoro irin mai firgitarwa da ban ta'ajibi, komai anayinsane saboda kuɗi, kuɗi! Dai kuɗi! Dai, sai yaushene mutane zasu ajiye son zuciya da burin mallakar kuɗaɗe su amshi gaskiya? Da wannan rayuwarne kuma kullum muke fatan ganin kayinmu cikin aljanna, a haka mukeso ALLAH yay mana rahama, a haka mukeso MANZON ALLAH yayi alfahari damu?,
Ya rumtse idanunsa sosai yana cigaba da haɗiyar ɓacin ran daya tokare maƙoshinsa.
Bai sake fitaba, bai kuma sake barin wani ya gansaba koda a cikin su Aliyu ne, dan kulle kansa yay a Office ɗin yanata saƙawa da kwancewa.
Har sai da lokacin salla yayine sannan ya fito domin gabatarwa.
![](https://img.wattpad.com/cover/220260947-288-k27914.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AksiTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...