Page 36
.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.

KAMU SEDANG MEMBACA
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AksiTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...