48

14.2K 1.2K 333
                                        

Page 48

..............Murmushi shima yaymin da kai hannu a ƙuguna ya kuma matsoni sosai jikinsa, cikin raɗa yace, “Are you ready?”. Ɓata fuska nayi ƙwalla na cikamin ido na girgiza masa kai dan nasan inda ya dosa. Wata shaƙiyyar dariya yayi dajan hancina yace, “Kedai raguwa ce yarinyarnan”. “Ni dai wlhy naji koma miye ace ba raguwaba, kai dan bakasan wahalar da ake sha bane ai”. Bakinsa ya ɗaura a saman kunnena ya ɗan ciza yana dariya da faɗin, “Shiyyasa nake son maidaki jaruma”. Nai saurin ƙanƙamesa saboda tsigar jikina dake tashi, da sauri na mintsini damtsan hannunsa “Ai na fika jarumta”.
       Saurin sakina yay da faɗin, “Ouch!. Ke dai muguwace wani lokacin”. Gwalo na masa na shige cikin ruwan. biyoni yay ciki, “Yarinya kin taro match kuwa”. Saurin ɗaukar soso nai dana haɗama kumfa na saka masa a fuska, yay ƙoƙarin riƙe hannuna naƙi bashi dama, hakan yasa mukaita facal-facal da ruwan kamar wasu ƙananun yara.
     Sai da muka gama shiriritarmu sannan muka fito. Zama nai a kujerar mirror ina goge fuska yazo ta bayana ya tsaya yana miƙamin hannunsa.
        Cike da mamaki na kalli hannun nasa, wani ɗan ƙyaƙyƙyawan akwatine mai kama da diamond amma farine shi tas wannan, sai ɗaukar ido yake da ƙyalƙyali, ɗaga kai nayi na kallesa ta cikin mirror ɗin ya ɗaga min kai da lumshe ido. Yawu na haɗiye da ƙyar nasa hannu na ɗauki ɗan box ɗin inayi ina kallonsa, ganin idonsa a kaina yake har sannan sai na nutsu waje guda, jiki a sanyaye na buɗesa. Na waro idanu sosai waje da faɗin, “Woow!” dan ƴan kune ne masu ƙyau a ciki da zobe. Bansan sanda na juya na daka tsale na ɗanesa bama ni, ya riƙeni da hannu biyu yana dariya muka faɗa saman gadon, tattare kunya nai na ajiye gefe, cikin salonsa daya koyar dani na shiga sumbatarsa fiye da yanda ya koyamin nasa karatun. A take ya rikicemin, nima dai nasan na taro match ai dama, tunda a hannu yake, dan wannan boss ɗin da kuke gani hummm, baisan wasaba ta wannan fannin.
         Duk yanda na dawo kuma ina roƙo da magiya daga ƙarshe bai saurareni ba, sai da ya samu abinda dama yakema ƙulafucin. Daga ƙarshe ya barni da kuka😒 (Kinada matsala ɗiyarga🚴🏼. Lol)
         “Haba my sweet Miemaa na Mai gadon zinarina, kukan ya isa haka Uhimyim, kece kinzo da salon da ban taɓa zaton kin iyaba, ashe kina ɗaukar karatun dai-dai gwargwado”. Cusa kaina nai jikinsa ina ɗan kai masa duka. Ya riƙe hannayen duka yana sakin murmushi mai sauti, “To shikenan nama fasa zuwa dake ni kaɗai zan tafiyata saudian gobe idan ALLAH ya kaimu”. Da sauri na ɗago na kallesa hawaye shaɓe-shaɓe, “Dan ALLAH da gaske kake?”. Goshina ya sumbata yana murmushi, “Idan kin barmin kuka ba”. Saurin share hawayena nayi, yaymin raɗa a cikin kunne. Zabura nai da sauri inaja da baya, “Dan ALLAH ka tausayamin wlhy bazan iyaba”.  Jawoni ya sakeyi jikin nasa yana murmushi, ya sake min raɗa a acikin kunne, hakkane ya sakani yin luff a jikin nasa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, shiko yana aikin shafa bayana alamar lallashi.
        Saida ya tabbatar nabar kukan sannan muka je muka sake wankan, shirin barci mukai muka koma falo, gaba ɗaya ya sake rugurguzar dani da gajiya, ko iya zaman shan fruit ɗin banyiba na kwanta da ɗora kaina a cinyarsa sai barci. Buɗe ido kawai nai da asuba na gammu a kan gadon ɗakinsa.

            Kamar yanda ya faɗa bayan dawowarsa sallar asuba ya sakani muka shirya kaya akwati ɗaya kacal, da dukna ɗauka wasa yake wlhy, sai da naga dai da gaske yake sannan na yarda. Da taimakonsa na gyara gidan, na killace duk abinda ya dace da ya zam a kilkacen, abinda nasan zai iya lalacewa naci na tattaresa ya kaima maigadi da Sadiq da yazo zai kaimu airport. Mamaki bai nema kasheniba sai da muka fito zamu tafi, securitys ɗin hukumarmu na gani nata kaikawo, na kallesa amma sai ya ɗauke kansa alamar baya buƙatar kowace iriyar tambaya, dole naja bakina na tsuke dan a zauna lafiya tunda baya buƙata.
      Wani gida muka fara zuwa, saida muka shiga naga dattijon tsoho da naita son tunano inda na san fuskar amma na kasa hakan, ga kallon da ya kemin shima tsigar jikina har tashi take. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi cike da girmamawa.
        Yanda ya amsamin da tsantsar kulawane ya sakani kallonsa, ya sakarmin ƙyaƙyƙyawan murmushi wanda a wajen Mahaifina kawai nasan irinsa, gabana yay wata irin yankewa ya faɗi har ina ɗan dafe ƙirji, “Babana”. Na faɗa a zuciya batare dana san maganar ta fito fili ba. Daga Alhaji babba har Jay kallon Bilkisu sukai.
    Nai saurin zama ƙasa danjin ƙafafuna suna neman gaza ɗaukata, wlhy da tsohon nan yay murmushi sai naga kamar babana ne, sake ɗagowa nai na kalleaa sai naga duk idanunsu a kaina suke. Boss yace “Yaya dai?”. Kai na girgiza masa da sauri alamar babu komai ina sake satar kallon tsohon ta gefen ido.
          “Tashi ki koma saman kujera”. Muryar tsohon ta daki dodon kunnena. “Nanma Yayi Baba” na faɗa muryata naɗan rawa.
     Murmushi yayi da har na iya jinsa daga inda nake, yace, “Amarya lallai kin iya tuwo, naga wannan ɗan dokar ya washe harda kaurin wuya ya ƙara”. Murmushi nayi kaina a ƙasa, sai boss naji yana basa amsa. “Idan yaji haushi gobe muje ɗaurin aurensa Miemaa, idan ya auro matarsa shima saita ringa masa yayi kaurin wuyan”. Dariya naji ya ƙyalƙyale da ita. Haka suka cigaba da tsokanar juna cike da birgewa, kafin suɗan tattauna. Banji ya faɗa masa ainahin mi zamuje yiba, hakan sai ya bani mamaki sosai. Kusan awar mu ɗaya da rabi a gidan sannan muka fito, daga nan sai airport.
                Farin cikine mara misali ya kamani lokacin da nai tozali da Ummu, ashe tare da ita zamu tafi harda takawa, ta rungumeni a jikinta tana yaba yanda nai ɓulɓul kamar yanda ta faɗa. Amintacciyar baiwarta nata mana dariya, banga takawa ba saida zamu shiga jirgi, ‘Masha ALLAH’ na faɗa a raina dan ganin cikakken mutum mai haiba da kwarjinin mulki, lallai sarauta ba ƙarya bace. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi, ya amsa min da kulawa tare da sakamin albarka.
     Sai da suka fara shiga shi da boss da ya riƙema hannu da dogaransa biyu kacal sannan muma muka shiga. Da yake waje na musamman aka bamu sai naji kamar mu kaɗaine a jirgin, acan ƙasan raina cike nake da ɗoki da fatan dacewa akan abinda zamuje dominsa.

ƘWAI cikin ƘAYA!!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora