Shafi na sha takwas
Babu editing dai
...........A mamakin kowa sai mukaji Inna tace, “To kukam ALLAH ya ƙyauta muku, na lura sam jininku bai haɗuba, bara Aibo yazo, ai na samo maganin wannan yawan fitinar taku mara dalili”.
Ba Lawusa kawaiba, koni kaina nayi mamakin maganar inna, danni a zatonama yau saita koreni a gidan saboda na taɓo ƴar mai ɗinta, amma ji yanda ta nunama halin ko in kula akan zancen, sai daimaganarta na ƙarshe akan mafitar data samo ta tsayan a zuciya sosai, komawa nai na kwanta ina rawar sanyina.
Lawusa kam kuka ta sanya rurus wai dama inna bata ƙaunarta ai a gidan, yau sai ta tattara ta barmusu gidansu, sai inna ta aurama Sha'aibu ni a yau da rana danta nuna ma duniya ni ƴar uwartace”.
Duk surutan nata dai inna bata kulaba, matan kuma da sukazo haɗa munafinci sai gasu suna jan ƙafa suna fita ɗai-ɗai da kunya.
Ina jiyo fitar Lawusa tana cigaba da zagin Inna.
Kaina kawai na girgiza ina mamakin irin wannan tarbiyya ta Lawusa, a hakane wannan zata zama uwar wasu, ita kanta tana buƙatar tarbiyyar balle abinda zata haifa.
A haka wahallalen barci ya kwasheni, ban tashi farkawaba sai lokacin sallar zuhur, shima dai inna ce ta tasheni akan naje nai sallah.
A mamakina kuma na fito zanyi alwala sai naga inna tayi abincin rana da kanta bata tasheni ba.
Salla nayi, ina zaune sai ga sallamar Yaya Shu'aibu ya dawo cin abincin rana kamar yanda ya saba, muryar Inna na tsinkayo tana sanar masa bani da lafiya, hakan ya sakashi faɗin “Subahanallahi, miya sameta kuma?” yay maganar yana ɗage labulen ɗakin.
Sannu nai masa sannan na gaishesa, cike da kulawa ya amsa, ya ƙarasa shigowa ɗakin yana tambayata mike damuna?.
“Yaya zazzaɓine kawai, kuma Alhmdllh yama sauka”.
“Wayyo sannu, ai ko sauron gidannan ya isa saka mutum zazzaɓi, kici abinci saina kaiki kamiz ki amshi magani”.
Nace “to” tare da masa godiya.
Nanma nazata Inna zatace a'a sai naji batace komaiba, sai ma amsar tambayarsa akan Lawusa take bashi, duk abinda ya faru tsakanina da Lawusar ta zano masa, ta ɗora da faɗin, “Ni yanzu na samo mafita akan wannan yawan rigimar tasu, fitar danai yau wani gida ƴar kande ta rakani na samowa Bilkisu aikin wanke-wanke da shara, inasha ALLAHU tananma sai kaga ta haɗa kuiɗin kayan ɗakinta har muma mu mora, kaga bama ta yini gidanba balle wannan fitinar ta cigaba da girmama a gidannan”.
Shu'aibu da fuskarsa ta ɗan nuna alamun damuwa, yace, “Amma Inna ni dai da kinyi shawara dani da ba'ayi hakaba, wane kuma aikin wanke-wanke Bilkisu zatajeyi fisabillahi, ni dai duk da sana'ata ba wata mai ƙwari bace zanyi iya bakin ƙoƙari wajen sauke haƙƙin zuminci akan komai na aurenta, indai dan zaman gidane zanma matarcan ta tsallake magana Bilkisun taje ta fara koyon ɗinkin jakka a wajenta, kinga ko aure tayi ai tasamu madogara insha ALLAHU”.
Ran inna a ɓace tace, “Nikam Aibo bansan miyasa kake nina tamkar ina zalintar yarinyarnanba, yanzu shi aikin da zataje bazai taimaketaba ne? Ko aure tayi ai dai ta samu ta iya komai”.
“Hakane Inna, nima banƙi ta takiba, muyi addu'a to ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi a ciki, idan ta samu lafiya sai muyi maganar”.
“Shike nan”
Inna ta faɗa a taƙaice, da alama dai har yanzu ranta babu daɗi akan canja mata tsari da yayi.Bayan mun gama cin abincine ya ɗaukeni a napep ɗinsa zuwa ƙyamiz, an bani magani tare da allura muka dawo gida.
Mamaki ya kamamu saboda iske jibga-jibgan motoci guda biyu da mukayi a ƙofar gidan, sai walƙiya suke.
Na kalli Yaya Shu'aibu ina faɗin, “Yaya baƙinmu ne waɗannan kokuwa?”.
Cikin jimami yace, “Wlhy ban saniba Bilkisu, amma inhar hakane to lallai inaga Kawu Ali ne kuwa yazo, dama lokaci-lokaci yakanzo su gaisa da Inna idan ya samu dama?”.
“Kawu Ali? Shikuma wanene shi?”.
Da mamaki sosai akan fuskarsa ya kalleni, “Bilkisu kina nufin wai baki san Kawu Ali ba shima? Yayansu Inna ne fa, ɗakinsu ɗaya da Inna ai”.
“Wlhy ban sanshiba Yaya, kana nufindai shima babansu ɗaya da Innata kenan?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu”.
“Yaya to ko shine suke cema Ɗan iya?”.
“Ƙwarai kuwa Bilkisu shine, amma nayi mamaki, na lura dai ke babuma wanda kika sani a dangin kenan?”.
Murmushin yaƙe nayi zuciyata na suka, murya na rawa nace, “Ai yaya sanda Innata nada rai babu wani ɗan uwanta dake raɓarta, nasan dai lokacin ina ƙarama takanje dani wasu wajajen gidan dangi, amma sai na lura saboda tana da nakasa kamar kowa gudunta yakeyi, Inna Zainabu ma abinda yasa ban manta da itaba ita da Kawu Manu saboda Innata na yawan ambatarsune”.
Tausayina sosai na gani a fuskar Yaya Shu'aibu, ya girgiza kansa kawai yana sauke numfashin tsantsar takaici, “Karki damu Bilkisu, komai na rayuwa da kika gani akwai ƙalu bale, watarana sai labari, irinku da kuke tashi cikin rashin gata ALLAH yafi ɗaga darajarku da ni'imomi masu yawa da komawa birge wanda suka juya muku bayan a lokacin da kuke buƙatar taimako, mu shiga ciki kinji, ALLAH ya ƙara miki haƙuri da jimirin cinye jarabawar rayuwa”.
Murmushi nayi ina share hawayen da suka zubomin a fuska, kusan a tare muka fita zuwa cikin gidan.
Ashema ba shi kaɗai bane harda iyalinsa, matarsa da ƴaƴansa namiji da mace su biyu, kallo ɗaya nai masa na gano asalin kamanninsa da Inna zainabu, yana kuma yanayi da innata itama, da yake ni sam ban biyo innata komaiba, gaba ɗaya kamannina na babana ne, dan dana biyo Innata da nazama ƙyaƙyƙyawa kuwa, dan su jinin fulanin asaline.
Inna tanata hidima da baƙinta, bakinta kam a washe tamkar gonar audiga.
Duk tsugunnawa mukai ni da Yaya Shu'aibu muka gaishesu, inna daketa faman washe haƙora tace, “To ka gantanan Ali, wannan itace ɗiyar Asiyar da nake faɗa maka”.
Idonsa a kaina yace, “ALLAHU akbar, ashema ta zama budurwa? Koda yake rabona da ganin Asiya tunfa kafin nabar ƙasarnan, lallai sheɗan ya jagoranci zukatanmu wajen raunana zuminci, yanzu ace ɗan uwanka da kuka tashi gida ɗaya dan aure ya ɗaukesa shikenan sai zuminci ya yanke? Manu ne ma wlhy yake sanarmin rasuwa lokacin bana ƙasar shiyyasa banzo ta'aziyya ba, ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata, ke kuma data bari ALLAH ya rayaki kinji”.
Hawaye na share ina amsawa da amin.
Daga nan ya koma kan Shu'aibu yana masa tambayoyi akan yanzu mi yakeyi?.
Matarsa dai da ƴaƴansa basa cewa Uffan, saima faman danne-dannen wayoyi sukeyi.
A cikin tambayoyin da yakema Yaya Shu'aibu ne yakejin ai ya kammala diploma ɗinsa, daga haka karatun ya tsaya, a take yace ya bashi takardun zai nema masa makaranta ya koma, ya juyo gareni yana tambayata nifa?.
Kaina a ƙasa nace, “Ai kawu ni koma Secondary ɗin ban kammala ba”.
Ya ɗan nuna damuwa saman fuskarsa, hakanne ya sakashi maida kallonsa ga Inna yana faɗin, “To nifa inaga wannan itace hanyar dazan gyara kuskurena akan Asiya, Zainabu zan tafi da Bilkisu ta zauna a gidana cikin ƴan uwanta, itama ta samu ilimin da zata taimaki kanta koda anan gaba babumu a raye”.
Take fuskar Inna ta canja launi, hakama matarsa da ƴaƴansa wani kallo na sukemin mai kama da wannan ƙazamar?.
Yaya Shu'aibu ne kawai ya bayyana tsantsar murnarsa a fili, kafinma inna ta bada amsa tuni Yaya Shu'aibun nata godiya.
Hakan ne ya dakatar da ita daga son hawa dokin naƙin datai niyyar yi.
Niko bammasan yazan fasalta muku yanayin dana shigaba, ɗumin hawaye kawai nakeji suna bin kumatuna, duk da naga rashin jin daɗin iyalansa hakan bai hanani ƙwaɗayin binsu ba, koba komai burina nayin karatu mai zurfi ashe zai cika a duniya, insha ALLAHU zanyi haƙuri da kowane irin halin daza fuskanta daga garesu domin samun cikar burina”.

STAI LEGGENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AzioneTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...