Page 41
.................A firgice Mama Atika, Dad, Mom, Uncle Nasir, Uncle Uwaisu, Aamilah, Salman duk suka miƙe baki hangame. Uncle Sulaiman da Uncle Sadiq da basusan komaiba illa cewar ɗan fir'auna ya mutu suka bisu da kallo dansu basusan ɗan fir'aunan ba a zahiri har yanzun. Cikin tsananin firgici da suɓutar baki Mama Atika tace, “Nasiru ba kunce sheɗanin nan ya mutu ba wai?”. Rasa mai bata amsa akai a cikinsu.
Ƙyalƙyalewa da dariya ɗan-fir'auna yay irin ta asalin tsagerun nan da suka gama gawurta a fitsara, ya nuna Mama Atika yana tsuke fuskar tamkar ba shine ya gama dariyar ba, “Ke dai tsohuwarnan anyi ƴar buƙulu, to idanma na mutu ban kwashi garaba ashe kanwa na kawo duniya, koda yake ashefa shirya kasheni akai ko? To anyi tabanza dan shegen taurin raine dani zanyi dogon zamani fiye da naki, a nunamin inda matata take malamai”. Jikin Aamilah na rawa tace, “Brother ga shi nan”. Harara ya zabga mata, “K dan tsohuwarki waye Brother ɗin? Yayah zaki ringa cemin dan gyatuminki hausa zakimin, kujimin faratun banza mai suffar yahudawan farkon ƙarni”. “Kayi haƙuri dan ALLAH yaya bazan sakeba” tai magana tana komawa bayan Jay da yay kunnen uwar shegu dasu kamar baisan wainar da ake toyawaba ta maƙale, Jay wayama yake latsawa abinsa hankali kwance kamar baya wajen. Dariya ɗan-fir'auna ya sake kecewa da ita yana faɗin, “Kaji bayani, da kikace ke tsagerace? Hegiya nifa bar ganinki ƙanwar matata billahillazi jinake kamarfa nai miki eyane dan zaki bada kala a garin maji daɗi. Amma kinci arziƙin musulunci ba'a wannan haɗin. Oga bara na shige daga ciki duk da fa inajin nauyinka fuska kawai zanyi aradun ALLAH na siɗaɗa”. Yay maganar da wani ɗora hannu ɗaya kan ɗaya irin salon nan na gaisuwar gayu ga na gaba dasu. (ALLAH ya daidaita sahunka akan lokaci habibullah😂🤣)
Jawaad da baiko ɗagoba ya jinjina masa kai kawai yana cigaba da aikin latsa wayarsa. Sai da ɗan fir'auna ya shige ɗakin da Shahudah ke kwance sannan Jay ya ɗago yana kallon Dad da yay sagade kamar wani gunkin hanya yana kallon ƙofar, firgigit ya dawo hayyacinsa saboda bugo ƙofar da ɗan-fir'auna yayi da masifar ƙarfi.
Inda Jay yake ya nufa da sauri-sauri yana baza babbar riga, Muryarsa da zafi ya furta, “Inason muyi magana”. Kallonsa kawai Jay yayi baice komaiba, sai dai fuskarsa shima a haɗen take, da ya kai maƙurar da ayanzu zai ɗauki matakin da bai ɗaukaba ada akan kowa. Guntun Murmushi yay da miƙewa yana ɗan kallonsu Uncle Nasir da suka zubo musu idanu. Rai a ɓace Dady yace, “Jawaad!!....” saurin ɗaga masa hannu Jay yayi batare daya kallesa ba. “Karkai saurin harzuƙa, muje waje muyi maganar”. Ɗauke kai Dady yayi kamar bazai sake tankawa ba sai kuma miya tuna oho ya nufi ƙofar fita yana jiyo kukan Momy dake sukar masa zuciya. Tashi Jay yay shima ya fice baiko kalli inda ƴan gidan nasu sukeba balle ya nuna yaji ihun kukan Momy dana Mama Atika.
A can gefe inda babu mutane ya hango Dad nata kai kawo ransa a ƙololuwar ɓace, Jay yay ɗan murmushi ya ƙarisa. Kallonsa Dad yay ya ɗauke kansa, “Jawaad!! Tun muna ƴar kunyar juna ka saka wannan ɗan iskan yaron ya sakarmin yarinya ta”. Murmushi Jay yayi da tura hannunsa ɗaya aljihu ɗaya kuma ya shafi kumatunsa da gashin saje ke kwance kaɗan saboda yana askewa, “Miyasa kukai tunanin kashesa ne zai baku mafita domin farin cikin ƴarku?. Irin wannan raɗaɗin da kakeji a yanzun, ita kuka shiryama taji mafiyisa Dad, Miye dalilinku na janta jikinku bayan baƙwa buƙatar ta raɓu jininku?........”
Dady ya kallesa da ɓacin rai sosai ya katsesa da faɗin, “Ya ina maka magana akan Mamana kanamin wata banzar magana taka mara tushe?”. Haɗe fuska Jawaad yayi da tura ɗayan hannunsa aljihu cikin ƙoƙarin danne nasa fushin yace, “Banason mu bama juna wahala, dan inhar muka kai ga haka komaima zan bankaɗo babu ruwana, dan haka mu tsaya iya haka ɗin kamar zaifi sauƙi. Batun Hudah na riga na gama da wannan matsalar yanzu tsakanin kune ku da sirikinku. Lokaci yayi da zaku nuna gajiyawar da baƙwaso a gareta na bakomai zaku iya bata ba, ALLAH shike bada komai ga wanda yaso a lokacin da yaso ba mutum mai barci, mai mutuwa, mai mantuwa ba. Koda yake, wannan bashi bane matsalata. Minene Ya kai Qaseem China kuma?!”.
“Kai Jawaad!! Tsagerancin naka da su Alhaji Nasiru ke faɗa har yazo kaina nima kenan? Minene matsalarka ko alaƙarka kuma da barin Qaseem ƙasar nan?, Qaseem fa ɗanane, babu kuma wanda ya isa ya sakani koya hanani a kansa, itama bilkisun ba tsoro yasa na bar maka itaba dan inada ikon hanaka auren nata tunda ɗiyar ƴar uwa tace, a hannuna kuma ka ganta. Niba sa'an yinka bane, ka kama kanka kajiki”. Ya ƙare maganar da fara tafiya zai bar wajen.
Jay dake binsa da kallo yay murmushi, “Tabbas kanada iko da ita fiyema da hakan, kuma har gobe ita kallon uba take maka dan ta baka dukkan yarda kai da ahalinka, babu wani laifinku da take kallo laifi sai dai kuskure. Haka take komai nata irin na masu ƙyaƙyƙyawar zuciya ne, tana ƙyautatama kowa zato musamman wanda ya nuna tausayinta saboda a irin rayuwar data tsinci kanta ciki, Dady ka daina tunanin har yanzu al'amarin a rufe yake, na tanadi hanyoyi masu yawa dazan bankaɗo komai harda na Qaseem da kukai ƙoƙarin rufewa dan ina bibiyarsa kuka turasa China”.
Juyowa Dad yay daga tsayuwar da yay tun fara maganar Jay. Idanu suka zubama juna na kusan mintuna biyu kafin Dady yay wani murmushi yana girgiza kansa. Batare da yace komaiba ya juya ya tafi.
Da kallo kawai Jay ya bisa har ya shige, ya lumshe idanu da furzar da huci mai zafi daga bakinsa, batare da yay ƙoƙarin sake komawa cikiba ya nufi motarsa ya bar asibitin
YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...