SURPRISE💁🏻
Wannan page sadaukarwa ne ga iyayen yaran da suka kuɓuta, gaskiya ina tayaku murna matuƙa gaya, mungodema UBANGIJI daya maido mana dasu garemu da gaggawa cikin ƙoshin lafiya kuma, ƴan uwa wannan yana sake nuna mana mu duƙufa addu'a wa ƙasarmu, aikin bana shugabanni bane kaɗai, dan idanma munƙi addu'ar mune zamusha wahala, shugabanninmu mutanene tamkarmu, suma basu isa tsaremu ba sai wanda ya haliccemu, aduk yanda rayuwa tazo mana mu amsheta matsayin jarabawa mu godema ALLAH, UBANGIJI yafi kowa sanin halin da muke ciki, muyi ƙoƙarin cinye jarabawa sai muzama masu nasara, zage-zage marasa amfani nakasace irin ta zuciya, ALLAH yay mana ni'imomi masu yawa miyasa bazamu gode masaba sai ƙoƙarin aibanta waɗanda suke mutane kamarmu da hangen gazawarsu, sai dai taimakon addu'oinmu zamu samu tsaron da muke buƙata a yankinmu, muyi haƙuri mu duƙufa wajen faɗama ALLAH kukanmu, mu gyara mu'amulanmu ga junanmu mu kanmu, dan bazamu kasance azzaluman junaba sannan muce zamu samu shugabanni adalai, mugyara sai ALLAH shima ya gyara mana danshi mai rahamane. ALLAH ya kawo mana haske da kwanciyar hankali, ya dafama shugabanninmu suma akan ƙyawawan ayyukansu, saɓanin haka ALLAH ka magance mana badan halinmu ba😭🙏🏻.
Page 32
.................Ganin yanda ta tsume sai ta bashi dariya da tausayi, ya dungure mata kai yana miƙewa da faɗin, “Yarinyarnan ki rage tsoro”.
Ni kaina bansan na sauke wani kakkauran numfashiba tare da komawa na zauna daɓar, nai azamar cusa kaina tsakanin cinyoyina ina mai godema ALLAH daya tashi. A raina sai ayyana rashin kunya irin na maza nakeyi, suyi abu kuma su fuske abinsu tamkar basuyiba.
Jay da tuni ya koma kan aikinsa yaɗan kalleta ya maida kansa ga rubutun da yakeyi, haka kawai yanaso ya ganta a yanayin tsoro dan ƙyau take masa. Bai sakebi takantaba ya cigaba da haɗa bayanai akan case ɗin mutuwar Gimba, ya ɗaukama kansa alwashi sai yabi kadin jininsa, duk masu hannu a cikin wannan al'amarin kosu ubanwaye saiya soya musu gyaɗa bisa tafin hannu. Ganin lokaci yaja sosai Bily na a yanda take tun ɗazun ya sashi sake kallonta, muryarsa babu alamun wasa yace, “Miemaa!”.
Gajiyar dake tattare dani tasa har barci ya saceni a haka ban fargaba, a bazata naji ya kira sunana, na ɗago da sauri na kallesa, shima ni yake kallo, sai dai fuskarsa babu walwala sam. “Tashi kije ki kwanta” ya faɗa yana nunamin gado da idanu. Yanda ya tsuke fuska babu sauƙi yasa na miƙe babu musu dan nasan dai kwana anan dole ya tabbata, zuwa nai na kwanta a bakin gadon sosai, naja bargon na rufama jikina batare dana cire hijjab.
Jay daya kuma maida hankalinsa ga aikinsa yace, “Kicire wannan hijjabin tunda ba cinyeki za'ai a ɗakinba”. ‘Boss matsala’ na ayyana a cikin raina ina zame hijjab ɗin naja bargon har saman wuyana.
Duk da azabar ciwon kai da ya keji haka ya jure yana cigaba da haɗa bayanan, sai kusan ƙarfe ɗaya saura ya miƙe, kallo ɗaya yayma sashin da Bilkisu take kwance ya fahimci har yanzu idonta biyu, baice komaiba ya cire jallabiyar jikinsa yasa t-shirt fara akan boxer ɗinsa ya haye gadon shima, sai dai ba kwanciya yayba, zama yay ya jingina bayansa jikin fuskar gadon ya kashe fitilar ɗakin yabar iya ta gefen gado. Bargon yaja ya lulluɓe iya ƙafafunsa zuwa cinya, ya lumshe idanunsa yana maijin zafi da ƙirjinsa ke masa wanda yaketa ƙoƙarin dannewa, tunɗazun dannewa kawai yake dan bayason ya ƙuntata zuciyar yarinyarnan da laifin daba nataba, yana buƙatar jin wasu abubuwa daga garetane shiyyasa ya kawota nan dama. Rayuwarsa da gimba ta shiga kokawar dawo masa cikin zuciya, yarone mai mutunci da sanin mutuncin duk wanda zama ya haɗashi dashi, yasha saka Gimba manyan ayyuka masu haɗari akan aikinsa kuma yay masasu cikin ƙwazo, gimba na ɗaukarsa tamkar yayansa da suka fito ciki guda, tabbas yayi rashi wanda yasan bazai taɓa maye gurbinsaba har abada, danshi tuni yabar ɗaukar gimba matsayin drivern sa kawai jinsa yake a jininsa tamkar ɗan uwansa abokin farin ciki da baƙin ciki. Wata ƴar ƙwalla ta taru mai akan fatar idanu kaɗan, hannu yasa ya shareta yana mai jero masa addu'oin neman gafara a cikin zuciyarsa. Ya ɗau tsayin mintuna goma a haka kafin ya juya ya kalli Bilkisu, ɗauke kansa yayi murya cike da ɗaci yace, “Miyasa kika dawo gidan su Hudah da zama?”.
Banyi tunanin ya fahimci idona biyu ba har yanzun, na rumtse idanuna da ƙarfi ina sauke ajiyar zuciya, batare dana motsaba nace, “Ƙaddarar maraici”.
Idanu Jay ya tsurama bayanta, tsawon sakanni ya ɗauka a haka kafin ya sake ɗauke kansa daga gareta, “Ina dangin mahaifinki suke? Misa basa cikin rayuwarki?”.
Hawayene masu zafi suka silalomin, dan yau kan Boss ya taɓomin inda yafi ko'ina ciwo a zuciyata, zaune na tashi na jingina da fuskar gadon nima, hawaye na ƴar tseren fitowa na shiga bashi amsa kai tsaye, dan na fahimci so yake kawai yasan wacece niɗin kafin zuwana gidan su aunty Shahudah, batare dana kallesaba nace, “Har iyayena suka bar duniya su dukansu basu taɓa sanar dani wata matsala dake tsakaninsu da duk danginsu ba, dukda nasha musu tambaya sai dai babu wanda ya taɓa bani amsa ƙwaƙwƙwara a cikinsu, kullum amsarsu a gareni itace, (komai da lokacinsa, idan lokacin yayi zan sani) tun ina damuwa da abun harma na ciresa a zuciya, dama ba komai ke sakani kwaɗayin son jiba sai yanda nake ganin sauran yara ƴan uwana sukan shirya a ranakun juma'a da Sallah suje gidajen danginsu, sai dai ni daga gareni ba haka baneba, tunda na girma nai wayo a gidan haya mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in na buɗi ido na ganmu, bara dai na maka gwari-gwari zakafi farimtata.
Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.
Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan har takai mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa. mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance nakasassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kake tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci ba?. Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙari bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum..........................

ESTÁS LEYENDO
ƘWAI cikin ƘAYA!!
AcciónTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...